Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin WAEC da NECO
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban sakandire ta ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ilimin ƙasar ta fitar, ta ce an dakatar da shirin ne domin sake shawara game da shi da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki.
Tun da farko ma'aikatar ta ce za ta ƙara yawan kuɗin jarrabawar biyu daga naira 27,000 zuwa 50,000 daga shekarar 2027 mai kamawa.
Ma'aikatar ilimin ta bayyana dalilai na tattalin arziki, inda ta ce a halin tattalin arzikin da ake ciki 27,000 ba zai iya biyan buƙatun jarrabawa ba.
Matakin ya haifar da suka da muhawara daga ƴanƙasar da dama, waɗanda ke ganin shirin zai ƙara yawan kuɗin jarrabawar zai ƙara yawan ɗaliban da za su daina zuwa makaranta.
Inda aka riƙa kiraye-kiraye ga gwamnati da ta jingine shirin nata.
Ma'aikatar ta ce ta yaba wa shawarwarin da ta samu kan batun daga ƴanƙasar.