Su wane ne suka sace masallata a ƙauyukan jihar Neja?

Asalin hoton, Umaru Bago/X
Bayyanar wani bidiyo da ake zargin daga ƙungiyar Lakurawa ya sake jefa al'ummar jihar Neja cikin fargaba da tashin hankali, bayan da aka ga gomman mata da ƙananan yara tare da wasu mutane zaune a cikin wani daji.
Bidiyon, wanda ya fara karaɗe shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, ya fito ne kwana biyu bayan harin da wasu ɗauke da makamai suka kai wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Borgu na jihar Neja a lokacin sallar Juma'a, inda aka yi zargin cewa sun yi awon gaba da ɗaruruwan mutane daga wasu ƙauyuka.
Duk da cewa har yanzu babu wata cikakkiyar tabbatarwa daga hukumomi kan sahihancin bidiyon da kuma yadda aka same shi, wasu na zargin cewa mutanen da aka gani a cikinsa su ne waɗanda aka ɗauke a harin.
Hakan ya sa bidiyon ya zama wata sabuwar mahangar fahimtar halin da waɗanda aka sace ke ciki, tare da ƙara jawo hankali kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
A lokaci guda kuma, ana ci gaba da danganta harin da ƙungiyar Lakurawa, wadda a cikin shekarun baya ta yi kaurin suna a wasu sassan arewa maso yammacin Najeriya da yankunan da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar.
Me bidiyon ya ƙunsa?
A cikin bidiyon na tsawon sakan 57 an ga gomman mutanen zaune cikin ciyayi a tsakiyar daji.
Mutanen sun haɗa da mata da ƙananan yara da magidanta zaune a ƙarƙashin wata bishiya.
An jiyo muryar ɗaya daga cikin masu ɗaukar bidiyon na cewa ''wane ne mahaifinsa ke ciki, wane ne mamanshi ke ciki wane ne ƙanwarsa ke ciki sannan kuma
''Gasu kamar yadda kuke ganinsu, kowa sai ya duba''.
A cikin bidiyon an ga yadda mata ke riƙe da ƙananan yara ciki har da jarirai, inda ake ta jin kukan ƙananan yara a cikin bidiyon.
Su wane ne suka sace mutanen?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin sace mutanen, to amma masana tsaro sun fara tsakaci kan waɗanda ake zargi da sace mutanen.
Dr Audu Bulama Bukarti mai bincike kan ayyukan ƴanbindiga a ƙasashen Afirka ya ce bisa ga dukkan alamu ƙungiyar masu ikirarin jihadi ne suka sace mutanen.
''Duk da cewa akwai ƴanbidiga da dama a yankin, kama daga ƴan fashin daji da ƴan Mahamuda da ƴansadiƙu da kuma Lakurawa'', in ji shi.
Dr Bukarti ya ƙara da cewa akwai yiyuwar ƴanbindigar su kasance ƴan Sadiqu ko ƴan Mahmuda.
''Daga bayanan da suke fitowa daga yankin ne cewa Lakurawa ba su yi ƙarfi a yankin ba kamar Mahmuda da ƴan Sadiqu'', in ji masanin tsaron.
Shi ma Dr Kabiru Adamu shugaban ƙungiyar Beacon Security mai sharhi kan al'amuran tsaro a yankin Sahel ya ce harin ka iya zama na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke aiki a yankin ne.
Masanin tsaron ya ce akwai ƙungiyoyi aƙalla biyar da ke ayyukansu a yankin, kuma dukkansu za su iya yin wannan hari.
''Akwai ƙungiyar ƴanfashin daji da ƙungiyar Ansaru akwai ƙungiyar Mahamudawa da kuma ragowar ƙungiyar Darul Salam, sakuma a baya-bayan nan ƙungiyar Lakurawa da ƙungiyar JNIM da suka fara shigo'', in ji shi.
Masanin tsaron ya ce a baya-bayan nan bayanai sun nuna cewa duka waɗannan ƙungiyoyi na aiki ne a tare a yankin.
Me ya sa yankin Borgu ke zama mafakar ƴanbindiga?
Dr Kabiru Adamu ya ce yankin Borgu ya ƙunshi yankunan ƙananan hukumomi biyar da suka shafi jihohi uku da suka haɗa da Neja da Kebbi da kuma jihar Kwara.
''Yanki da tsohuwar Borgu da ya ƙunshi ƙananan hukumomi biyar na jihohin yankin uku'', in ji shi.
Ya ce yanki ne mai ɗauke da yanayin da zai yake bai wa ƴanbindiga damar gudanar da ayyukansu, saboda yadda yake.
''Yanki ne da ke ƙunshe duwatsu da manyan dazuka da ruwa kuma dajin yankin ya nausa har cikin ƙasar Benin''.
Me jami'an tsaro ke yi?
Kawo yanzu babu wani martanin daga ɓangaren jami'an tsaro dangane da fitowar wannan bidiyo.
Amma dai tuni rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da hari kan ƙauyukan na Borgu tare da sace gomman mutane a masallacin Juma'a.
A nata ɓangare gwamnatin jihar Neja ta bai wa jami'an tsaro umarnin tabbatar da kuɓutar da mutanen cikin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labaran jihar, Obed Nana ya fitar ya ce gwamnan jihar, Umar Bago ya buƙaci jami'an tsaron su gaggauta aiki tare don kuɓutar da mutanen.











