KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftanta da kuma sassan duniya na ranar Litinin 24 ga watan Agusta, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi

  1. Najeriya ta ƙaddamar da yaƙi ta sama kan ƴan fashin daji

    Jirgin yaƙin sojin Najeriya

    Asalin hoton, NAF/FB

    Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ƙaddamar da wani shirin yaƙi ta sama a jihohin arewa maso yammacin ƙasar kan “ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka” da suka addabi yankin.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce yaƙin wanda ta yi wa laƙabi da ‘Hannun ƙarfe’ zai tallafa wa sojojin da ke kai samame ta ƙasa domin dawo da tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna, inda sojoji ke aiki ƙarƙashin shirin ‘Operation Fansan Yamma’.

    “Wannan shiri ya tabbatar da ƙoƙarin dakarun saman Najeriya wajen amfani da dabarun yaƙi ta sama da haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro wajen daƙile ayyukan ƙungiyoyin miyagu’.

    Haka nan a cikin wani saƙo na daban rundunar sojin Najeriya ta sanar da wani shiri na kawar da ƴan ƙungiyar Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi.

    A watan Mayu ƙungiyar IS a yankin Sahel ta yi iƙitrarin ɗaukar nauyin wasu hare-hare a jihohin Sokoto da Kebbi.

  2. Wa'adin da Amurka ta ɗiba kafin 'gallaza' wa Iran ya cika

    xxxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hafsoshin tsaron Pakistan, Field Marshal Asim Munir, zai kai ziyara Iran a yau domin kokarin farfado da tattaunawar da ta kakare tsakanin Tehran da Amurka.

    Zai kai ziyarar ne yayin da Amurka ke shirin sanar da karin takunkuman tattalin arziki kan Iran.

    Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana matakan a matsayin mafiya tsauri da girma da aka taba shirya wa wata kasa abokiyar gabar Amurka.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya yi watsi da barazanar, yana mai cewa alama ce ta rashin mafita da Amurka ke ciki.

    Iran tana nan yadda take, ko gezau, kuma tana ci gaba da barzanar kai hari kan duk wani jirgin ruwa da zai bi Mashigar Hormuz wanda ba ta ba shi izini ba.

    Sai dai kuɗin ƙasar ta Iran, wato Rial, ya faɗi zuwa mafi karancin matsayi a tarihinsa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

  3. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin (Monde tushen aiki) a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.