Ƙungiyoyi 5 da za su ɗauki hankali a Gasar Premier ta bana

,

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da ya rage saura ƴan kwanaki a fara gasar Premier Ingila ta 2026/27, ƙungiyoyi na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar gasar.

Wannan ya haɗa daga sayen sabbin ƴan wasa zuwa shirya wasannin share fagen tunkarar kakar wasan da kuma duba lafiyar ƴan wasansu majinyata.

Arsenal ce ta lashe gasar ta bara, a karon farko cikin shekara 22, ƙungiyar za ta so ta sake lashe gasar a karo na biyu a jere ta kuma bi irin hanyar da Manchester City ta bi ta mamaye gasar a cikin kimanin shekaru 10 lokacin Pep Guardiola.

A gefe ɗaya sauran ƙungiyoyi irin su Liverpool da Manchester City da suka lashe gasar a kusa suma za su yi duk mai yiwuwa su koma cikin jerin masu neman lashe gasar.

BBC ta yi nazari kan ƙungiyoyi biyar da za su ɗauki hankali a Gasar Premier ta bana ko ma su lashe ta a ƙarshen kakar wasan.

Arsenal gwarzuwar Premier

Arsenal za ta yi fatan ɗorawa daga kan ƙoƙarin da ta yi a bara na lashe gasar Premier karon farko bayan shekara 22.

Ana kallon za ta fi kowacce ƙungiyar ƙoƙari ne ganin yadda aka samu sauye-sauye a tsakanin manyan ƙungiyoyin gasar musamman a ɓangaren masu horaswa.

Ƙungiyoyi tara cikin 20 na Premier za su fara gasar ne da sabbin masu horaswa, wasu kuma irinsu Manchester United da Tottenham za su fara gasar ne da masu horaswar da har yanzu ba su kai shekara ba.

Amma kocin Arsenal Mikel Arteta yana tare da ƙungiyarsa tun 2019 kuma ya yi na biyu a gasar kusan sau uku a jere wanda hakan ya ba shi damar fahimtar gasar ƙwarai da gaske.

Arsenal ba ta naɗe hannu ta zauna haka ba, ta ci gaba da sayen ƴan wasa domin ci gaba da ƙarfafa tawagarta, ta sayi ɗan wasan tsakiyar Brazil Bruno Guimaraes daga Newcastle, ta kuma sayi dan wasan gefe Christos Tzolis daga Club Brugge.

Rahotanni na cewa ƙungiyar tana daf da ɗaukar dan wasan gaban Faransa da PSG Bradley Barcolaa nan gaba.

Chelsea ba za ta buga gasar Turai ba

,

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Chelsea da ta yi sabon ango Xabi Alonso, tana da dama irinta wasu ƙananan ƙungiyoyi da ba za su buga kowacce gasa ba ta ba nahiyar Turai bayan wasannin cikin gida.

Duk da cewa ƙungiyoyi tara ne za su halarci wasannin nahiyar Turai amma Chelsea ba ta samu shiga cikinsu ba saboda gaza taɓuka abin kirki a bara.

Dalilin haka shugabannin ƙungiyar sun ɗauki matakin kawo gyara cikinta, inda suka fara da kawo sabon koci Alonso da ya rike Bayer Leverkusen da Real Madrid a baya, sai dai bai samu damar da ta dace ba a Real hakan ya sa ya bar aiki da wuri.

A ƙoƙarin gyaran da take yi Chelsea ta sayi ƴan wasa da dama wasu daga cikinsu sun haɗa da: Marco Palestra daga Atalanta da Morgan Rogers wanda ya kafa tarihin ɗan wasan Ingila mafi tsada, da kuma Maxence Lacroix dan wasan baya daga Crystal Palace.

A gefe ɗaya kuma ta ɗauki tsofaffin ƴan wasa da suka haɗa da Denny Welbeck daga Brighton sai kuma Jordan Henderson daga Brentford bayan ƙarewar kwantaraginsa.

Chelsea ta fi kowacce ƙungiya a Premier matasan ƴan wasa waɗanda za su daɗe ana fafatawa da su.

Da wannan ake hasashen cewa za su buga Premier ba tare da gajiyawa ba, ba tare da wata damuwa ta cewa ƴan wasansu za su gaji ba.

Aston Villa gwarzuwar gasar UEFA Europa

,

Asalin hoton, Getty Images

Aston Villa ita ce gwarzuwar gasar UEFA Europa ta 2026, kuma ta samu nasarar ne bayan doke SC Freiburg da ci 3-0.

Ta kuma kammala gasar Premier ta 2025/25 a matsayi na huɗu a saman Liverpool da tazarar maki biyar.

Aston Villa tana da kocinta Unai Emery wanda ya koma a watan Nuwamban 2022. Tun bayan nan ɗan Sifaniyan yake ta ƙoƙari a tawagar amma a wannan kakar da ta gabata ce ya taka muhimmiyar rawar gani.

Ƙungiyar tana da baraden ƴan wasa matasa da mafi yawansu ke tsakanin shekarun 21 zuwa 31.

Duk da cewa ta sayar da ɗaya daga cikin mafiya ƙwazo a tawagar a bara Morgan Rogers, ta ɗauki Johan Manzambi ɗan Switzerland daga Freiburg da Jao Gomez na Brazil daga Wolves, ta kuma ɗauki aron ɗan wasan Argentina da ke buga wasa a Chelsea Alejandro Garnacho.

Duka waɗannan na cikin abubuwan da ake kallon za su bai wa tawagar ta Unai Emery damar taka rawar gani da ɗorawa daga inda ta tsaya a ƙoƙarin da ta yi a bara.

Manchester City ta daɗe ta na mamaye Premier

,

Asalin hoton, Getty Images

Duk da cewa ana mata hasashen za ta iya fuskantar koma baya, to amma hausawa na cewa mushen kura ya fi ƙarfin Allah sarki.

Ta yi rashin kocinta Pep Guardiola amma ta maye gurbinsa da Enzo Maresca wanda ya gaza a tsohuwar ƙungiyarsa ta Chelsea.

Ɗan wasanta da ke da matuƙar tasiri na tsakiya Bernardo Silva shi ma ya tafi a wannan kakar kuma ya zuwa yanzu ba ta sanar da ɗaukar wanda zai maye gurbinsa ba.

Sai dai kuma mafiya tasiri irinsu Rodri da ake ta faman kai ruwa rana a kansa tsakanin Real Madrid da Barcelona.

Erling Halaand na nan tare da su ga Umar Marmoush da ɗan wasan gefe na tawagar da ta saya a rabin kaka Antoine Semenyo.

Manchester United za ta koma Champions League

,

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ana mata kallon za ta taka rawar gani a wannan kakar wasan da za a fara.

Wannan ya biyo bayan ƙoƙarin da ƙungiyar ta yi a ƙarƙashin kocinta Michael Carrick wanda ya amshi ragamar ƙungiyar a watan Janairun wannan shekarar bayan korar tsohon kocinta Ruben Amorim.

Carrick ya amshi ƙungiyar United na matsayi na bakwai amma sai da ta ƙare a matsayi na uku a ƙarshen kaka.

Duk da cewa ta yi rashin babban ɗan wasanta na tsakiya ɗan ƙasar Brazil Casemiro, amma ta iya sayen ɗan wasan tsakiya daga Aston Villa Youri Tielemans, ta kuma sayi Andrey Santos wabda shi ma ɗan Brazil ne daga Chelsea.

Kuma ƴan wasan gabanta da ake tunanin za su iya taka rawar gani a nan gaba, sun ƙara samun ƙarfi tun bayan dawowar ɗan wasanta Marcus Rashford daga Barcelona inda tya yi zaman aro.