Yadda Hisba ta hukunta matasan da suka yi auren sirri a Bauchi

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar Hisba a jihar Bauchi ta ladabtar da wasu matasa biyu mace da namiji da aka ɗaura aurensu kan sadakin naira 3,000.

Kwamishinan Hisba a jihar Bauchi, Barista Aminu Balarabe Isa, ya shaida wa BBC cewa matasan biyu waɗanda shekarunsu ba su wuce 30 ba, sun nemi wani limamin da ba a gano ba ya ɗaura musu aure a kan sadaki ƙanƙani.

Bauchi na daga cikin jihohin Najeriya da ke bin tsarin shari'ar Musulunci wajen yanke hukunci kan laifukan da suka shafi zamantakewa.

Bidiyon yadda hukumar ke yi wa matasan bulala ya karaɗe shafukan sada zumunta inda kuma mutane da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan batun tare da nuna damuwa kan yadda matasa ke neman rusa tsarin yin aure.

Ya ce sun kamo matasan ne domin ya zama darasi ga sauran mutane da masu tunanin ɗaukan irin wannan hanya.

Yadda aka gano ma'auratan

Shugaban Hukumar ta Hisba a Bauchi, Barista Aminu Balarabe Isa, ya ce sun samu rahoton cewa matasan biyu da ke zaune a cikin garin Bauchi sun haɗa abokansu tare da naɗa waliyyai da limami inda aka ɗaura aurensu a kan naira N3,000.

Ya ce bayan an ɗaura auren ne kuma matasan biyu suka nemi wani gida mai kama da hotel inda suka keɓe na tsawon kwana biyar 'tare da yin abin da bai kamata ba' a tsakaninsu.

"Ƙorafe-Ƙorafe da muka samu a hukumance, muka yi haɗin gwiwa da ƴan kwamitin sintiri na jihar Bauchi aka kamo su, don mu ji ainahin abin da ke faruwa."

"Da aka kawo su gabanmu, sun tabbatar da faruwar lamarin cewa sun aikata waɗannan laifuffuka." in ji Barista Balarabe Isa.

Barista Aminu Balarabe Isa ya ce lamarin bai wuce mako biyu da faruwa ba kuma ya ce zaman da suka yi da matasan sun gano cewa wannan ne karon farko da hakan ta faru a tsakaninsu.

Ya shaida wa BBC cewa matashin yana da sana'arsa bisa binciken da suka yi sannan yarinyar tana son shi kuma "iyayen ma sun sani."

Me shari'ar Musulunci ta ce kan aure?

Ya ce matasan sun saɓa haƙƙi na Ubangiji saboda aure yana da ƙa'idoji waɗanda kuma idan aka saɓa musu aure bai tabbatu ba.

Ya ruwaito faɗar Annabi Muhammad SAW cewa "babu aure idan babu sadaki, babu shaidu da kuma waliyyai."

Shugaban hukumar ta Hisba ya ce "waliyyan matasan da suke da haƙƙi su aurar da su suna raye - mahaifin yarinyar da yaron suna raye amma ba tare da saninsu ba suka tsallake waɗannan abubuwan, suka yi gaban kansu saboda biyan wata buƙata suka kira abokansu suka ɗaurawa kansu aure."

A cewar shi, addini ya fayyace hukunce-hukuncen aure tun daga kan nema zuwa yadda za a ɗaura shi."

Ya ƙara da cewa a halin da ake ciki sadaki bai gaza 130,000 mafi ƙaranci, amma akwai lissafin da sadakin ya kai 200,000 duk da cewa akwai saɓanin malamai.

"Su waɗannan yara sun yi gaban kansu, iyayensu na nan kuma idan aka bari waɗannan abubuwan suna faruwa, lamarin aure zai lalace, yara za su yi ta yin gaban kansu.

Wane hukunci aka yi musu?

Shugaban hukumar ta Hisba ya ce abokan da suka ɗaura auren an ladabtar da su ta hanyar sa su shara da kuma bulala.

"Su kuma matasan, a hukumance, wasu malamai sun bayar da fatawar a duba yadda za a gyara auren musamman idan suka yi istibra'i sai a ga yadda za a duba ƙa'idoji da Musulunci ya ƙayyade don a tabbatar da wannan aure." in ji Barista Aminu Balarabe Isa.

Me iyayen 'ma'auratan' suka ce?

Shugaban hukumar ta Hisba ya ce sun zauna da iyayen matasan da masu unguwannin da matasan suka fito.

"Iyayen yaran sun amince a gyara auren, a bi duk ƙa'idojin da suka kamata, za su ba da gudunmawar da ta dace don a yi auren bisa ƙa'ida." kamar yadda Barista Aminu Balarabe Isa ya faɗa.

A cewarsa, ba wai iya jihar Bauchi ba, ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo irin waɗannan abubuwan shi ne lalacewar tarbiyya a tsakanin al'umma.

Akwai kuma sakacin iyaye wajen kula da halin da ƴaƴansu suke ciki.

Ya ce matasan a halin yanzu sun koma gaban iyayensu yayin da ake ci gaba da neman limamin da ya ɗaura auren.