Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace riba Najeriya ta samu daga cire tallafin man fetur?
Lokaci kamar warhaka a shekaru huɗu da suka gabata, baya ga batun babban zaɓen ƙasar, babbar muhawarar da ta kaure ita ce ta cire tallafin man fetur.
Gwamnatin Najeriya a wancan lokaci ta bayyana wa al'ummarta cewa kuɗin da take kashewa wajen rage tsadar man fetur a ƙasar shi ne dabaibayin da ke hana ta samun ci gaba.
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya bayyana cewa a shakara ta 2022, ƙasar ta kashe kuɗi naira tiriliyan 4.39, wato dala biliyan 9.7 a kan tallafin man fetur.
A wasu shekaru gabanin cire tallafin man fetur ɗin kamfanin na NNPC ya gaza biyan gwamnatin ƙasar kuɗaden harajin da suka kamata daga gare shi, inda ya koka da rashin isassun kuɗi.
Najeriya ta dogara ne da man fetur wajen samun kuɗin shiga, kuma gwamnatocin da suka gabata sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu wajen cire tallafin man fetur, amma abin bai yi nasara ba.
Sai a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ranar da aka rantsar da sabon shugaban ƙasar Bola Tinubu, ya sanar cewa daga ranar "tallafin man fetur ya zo ƙarshe".
Sai dai kimanin shekara huɗu bayan haka al'ummar ƙasa ba su ga wani sauyi ba.
Ƙasar ta ci gaba da cin bashi babu ƙaƙautawa, daga ciki da waje, inda yawan bashin ƙasar ke ci gaba da hauhawa.
Babu wasu manyan ayyuka da za a iya gani a zahiri waɗanda gwamnatin za ta iya cewa ta aiwatar sanadiyyar cire tallafin, wanda mutane ke amfana da shi.
A wata tattaunawa da ya yi cikin watan Afrilu, sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce: "Ba za ka toshe wurin da kuɗi ke zurarewa ba kuma ka ci gaba da cin bashi...Idan ba ka biyan tallafi, kuma ka tara kuɗin, me ya sa za mu yi ta cin bashi? Wannan ne irin tambayar da ya kamata mu riƙa yi".
Shi ya sa da dama daga cikin al'ummar ƙasar ke kokwanton ko akwai wani alfanu da ƙasar ta samu daga cire tallafin man fetur ɗin baya ga hauhawar farashi da tsawwalar rayuwa a ƙasar?
Masanin tattalin arziƙi a Najeriya kuma malamai a jami'ar Bayero da ke Kano Dr Shamsudden Muhammad ya ce "tun farko abin da gwamnati ta so yi shi ne ta sakar wa kanta mara wajen samun kuɗi"
Duk da gwamnatin tarayya ta yi was alƙawurra na tallafin abubuwan da za su taimaki talaka amma ba gani ba.
Babban abin mamakin shi ne baya ga shigar da talaka cikin wahala, da gazawara duk wasu shirye-shiryen rage raɗaɗi da ta yi alaƙawari, ita kanta gwamnati ba ta samu alfanun da ta yi tunanin za ta samu ba.
Ya ƙara da cewa "Babban abin takaici shi ne hatta amfanin da gwamnati ta hango wa kanta, har yanzu ba a samu haka saboda har yanzu ana samun wagegen giɓi a kasafin kuɗi da kuma yawan ciyo bashi wajen gudanar da ayyuka, hatta wajen biyan kuɗin ƴan fansho."
Saboda haka nan masanin tattalin arziƙin ya ce "cire tallafin man fetur bai yi wa Najeriya amfani ba, hasali ma ya ƙara jefa talaka ne a cikin ƙuncin rayuwa.
Wani abu da masanin tattalin arziƙin ya taɓo shi ne yadda farashin man fetur ke tashi a Najeriya da zarar an samu tashin farashin sa a kasuwannin duniya, wanda hakan ke haifar da tashin farashin kayan masarufi.
Ya ce "sai dai ko da farashin man fetur ɗin ya sauko, kayan masarufi ba sa saukowa saboda ba a sanya ido a kansu kamar yadda ake yi wa man fetur".
A lokacin da gwamnatin ta Najeriya ke shirin cire tallafin man fetur din ta yi alƙawarin fito da wasu shirye-shiryen sassauta wahalhalun da al'umma za su iya fadawa ciki, kamar:
- Tallafin kuɗi ga al'umma (Conditional Cash Transfer)
- Bayar da bashi ga matsakaita da ƙananan sana'o'i (Presidential Conditional Grant Scheme)
- Shirin samar da motocin safa masu amfani da CNG (Mass Transit and Compressed Natural Gas)
- Sauƙaƙa kayan noma (Subsidized Agricultural Inputs and Food Distribution)
- Bayar da bashin karatu ga ɗalibai (The Nigerian Education Loan Fund (NELFUND))
Duk da cewa an ga ɓurɓushin wasu daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin Najeriya ta ce za ta fitar domin sauƙaƙa wa al'umma raɗadin cire tallafin, amma har yanzu ba a ga abin a wadace yadda za a iya cewa ya kawo wa al'umma sauƙi ba.
Gwamnatin ƙasar ta yi ta ƙoƙarin ganin an samar da cibiyoyin sauya moyoci masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da gas na CNG, sai dai duk da haka har yanzu irin wadannan cibiyoyi ƙirgaggu ne a fadin ƙasar.
Haka nan gidajen shan man na CNG ƙirgaggu ne a biranen ƙasar, kamar yadda motocin safa da gwamnatin ta yi alƙawari suka kasance ƙirgaggu.
Wani manomi, Abubakar Isiyaku a jihar Kaduna ya shaida wa BBC cewa "babu wani shiri da muka gani daga gwamnati na taimaka wa manoma wajen samun kayan noma, abin da muka gani kawai shi yadda wasu gwamnoni suka riƙa raba ƴan tireloli ƙalilan na gurɓataccen taki."
Wani abu da za a iya cewa an fi ganin tasirinsa shi ne bashin karatu ga ɗalibai.
Ya zuwa watan Nuwamban 2025, alƙaluman da gwamnatin ƙasar ta fitar sun nuna cewa ɗalibai 788,947 ne suka amfana daga bashin, daga cikin ɗalibai 1,161,531 da suka nemi bashin.
'Abin da ya sa ƴan Najeriya ba su gani a ƙasa ba'
Farfesa Ahmed Adamu, masani kan harkokin man fetur kuma malami a jami'ar Philomath University da ke Abuja, babban birnin Najeriya ya ce rashin ganin amfanin cire tallafin man fetur a Najeriya na da alaƙa da farashin dalar Amurka.
A cewarsa darajar dalar Amurka ta nunka bayan cire tallafin man fetur, wannan ya sanya alfanun da ake tunanin za a samu daga ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin Najeriya ta samu daga cire tallafi bai yiwu ba.
Masanin tattalin arziƙi Dr Shamsudden Muhammad ya ce "ba a ga wani alfanu da cire tallafin ya kawo wa Najeriya ba ya zuwa yanzu, in baya ga biyan buƙatun wasu ƙungiyoyin duniya da wasu ƙasashen duniya da suka matsa a cire tallafin.
Ya bayyana cewa irin waɗannan hukumomi su ne Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) da kuma Bankin Duniya (World Bank).