Abu uku da ka iya faruwa a ƙarshen duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Duhu, da yanayi na sanyi na daga cikin nazarze-nazarce da aka fi yi kan yadda alamomin tashin duniya ka iya zama a nan gaba.

Makomar duniya na ɗaya daga cikin tambayoyi na ban mamaki da ake yi a kimiyance. Ko su kansu masana kimiyyar na ganin akwai tambayoyi da dama da ke buƙatar amsa.

Kafin mu fahimci yadda tashin duniyar zai kasance, akwai buƙatar mu gane yadda duniyar ta samo asali.

Farkon Duniya

A cewar hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, NASA, duniya na nufin komai: duk wani abu da ke cikinta har ma da lokaci.

Yadda duniyar ta samo asali shi ne abin da masana kimiyya ke kira da Big Bang Theory a Turancin Ingilishi wanda ke nufin yadda duniya ta faɗaɗa daga wani wuri guda.

A cewar nazarin, shekaru biliyan 13.8, duniya na cikin yanayi na matsanancin zafi kuma ta yi ta faɗaɗa tun lokacin.

Duniya ta ci gaba da faɗaɗa kuma cikin tsawon lokaci, an samu taurari.

Har yanzu kuma duniya na ci gaba da faɗaɗa.

Farfesa Alexander Zabot, da ke Jami'ar Tarayya ta Santa Catarina a Brazil ya ce "aikinmu shi ne mu yi nazarin kwararar kogi ba tare da mun samu damar duba sinadarai da ƙwayoyin da ke cikinsa ba."

Matsanancin yanayin sanyi

Cibiyar nazari ta Royal Greenwich Observatory a Birtaniya ta ce idan duniya ta ci gaba da faɗaɗa, za a samu yanayin da taurari za su warwatsu nesa da juna daga bisani, ba za a samu taurari ba sannan taurarin da ake da su za su ɓace.

Ana kiran wannan yanayin da "Great Freezing" wato matsanancin yanayin sanyi.

A cewar Royal Greenwich Observatory, hakan na nufin ƙwayar zarra da ke duniya zai kai yanayi iri ɗaya wanda hakan zai sa komai ya tsaya cak ya daina motsi ya kuma daina sauyawa.

Farfesa Raul Abramo na Jami'ar Sao Paulo da ke Brazil ya ce: "Komai yana nuna cewa duniya na ci gaba da zama kufai sannan tana ƙara sanyi. Taurari kuma suna ƙara yin nesa da juna. Wannan ne yanayi na ƙarshe da duniya za ta zama maƙabarta."

Tarwatsewar duniya

Kamar yadda Gidan ajiyar kayan tarihi na Royal Greenwich ya yi bayani, nazarin ya yi la'akari da batu da ke cewa duniya tana faɗaɗa cikin sauri bisa tasirin makamashi.

Ana kiran hakan da yanayin da duniya za ta tarwatse.

A cewar hukumar NASA, wani nau'in makamashi da ake kira da 'Dark Energy' wanda zai samar da wani abu da zai sanya duniya ƙara faɗaɗa cikin sauri. Hukumar ta ce akwai kaso kusan 68.3 zuwa 79 na irin wannan makamashin a duniya.

An fara gano shi a ƙarshen shekarun 1990.

A cewar Farfesa Zabot, duniya na girma, yayin da duniya ke ƙara girma, haka ma tasirin makamashin.

NASA ta ce rashin daidaiton nau'in makamashin na iya sa duniya ta fashe, wani yanayi na faɗaɗar sararin samaniya mai ƙarfi ta yadda taurari za su rushe.

Duwatsun ado

Akwai abubuwan da ka iya faruwa.

Idan nau'in makamashi na 'dark energy' ya yi rauni, ƙarfin maganaɗisu zai iya sake maido da duniya zuwa wata matsaya. NASA ta ce hakan na janyo rushewar da ka iya sa duniya ta fashe.

Wani nazarin kuma shi ne duniya na iya takurewa wuri guda kuma za a iya samun wani hazo sannan a sake samun wata sabuwar duniya. Nazarin na nufin wannan duniyar da duniyoyin da za su zo nan gaba za su kasance babu ƙarshe kuma za su yi ta faɗaɗa.

"Sai dai wani abu ne da ba mu da hujja a kai," in ji Farfesa Abrams.

Shin abu ne mai yiwuwa a iya cankar lokacin da duniya za ta zo ƙarshe?

"A a, babu manuniya ko hujja cewa za a samu gagarumar fashewa ko rushewa a gaba," in ji Farfesa Abram.

Farfesa Zabota ya ƙara da cewa: "wasu na ƙiyasta cewa wannan ne zai zama a ƙarshen kusan triliyoyin shekaru a nan gaba, yayin da wasu ke ganin lokacin ya ma fi haka."

Idan duniya ta yi aƙalla shekaru biliyan 13.8, akwai shekara biliyan 986.2 da suka rage kafin a kai shekaru triliyan ɗaya.

Wani bincike daga jami'ar Radboud da ke Netherlands ya ce duniya na raguwa cikin sauri fiye da baya.

Masu bincike sun ƙidaya cewa taurarin ƙarshe da za su tarwatse a cikin shekaru 10 na shekaru 78 na ƙarshen duniya.

Nau'ikan halittu da ke doron duniya ba lallai su wanzu ba domin shaida faruwar hakan.

Akwai yiwuwar a lokacin an naɗe duniya a lokacin ne ya kamata rana ta zama wata babbar tauraruwa mai launin ja, to amma akwai tazarar shekaru biliyan shida da suka rage kafin wannan lokaci.

"Gaskiyar magana ita ce har kawo yanzu ƴan abubuwan da muka sani kan kimiyyar duniya da faruwarta," in ji Farfesa Abrams. Kuma rashin wadatattun ma'aunai ya sa gwada haƙiƙanin asalin duniyar ya kasance mai wahala sosai.

Kuma wannan ne ya sa ake ta bincike da samar da nazarce-nazarce na gwaji da ma shaci faɗi. Misali, binciken da ba a tabbatar ba da suka haɗa da na duniyoyi masu yawa da kuma na duniyoyin da ke daura da tamu duniyar da ke nuni da wanzuwar wasu duniyoyin fiye da ɗaya.