ADC ta gargaɗi ICPC kan ci gaba da hana mutane ganawa da El-Rufai
Jam’iyyar ADC ta nuna damuwa, tare kuma da zargin hukumar yaƙi da ayyukan rashawa da laifuka masu alaƙa da haka ICPC da hana shugabannin jam’iyyar ganin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta hannun sakataren yaɗa labarunta na ƙasa Bolaji Abdullahi a yau Juma’a, ta ce hukumar ICPC ta hana sakataren jam’iyyar Rauf Aregbesola da wasu shugabanninta ganin Nasir El-Rufai a inda ake tsare da shi a Abuja a ranar ta Juma'a.
Ta ce ICPC ta ɗauki wannan mataki ne duk da matakin jam’iyyar na neman ganin tsohon gwamnan a hukumance – wanda ake riƙe da shi bisa zargin almundahana.
Jam’iyyar ta ce an hana jagororin nata ganin El-Rufai “ba tare da wani tartibin bayani ba”.
Wasu hotuna da aka riƙa yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu daga cikin jagororin jam’iyyar a wajen ofishin hukumar da ke Abuja, inda suka yi cirko-cirko.
Haka nan ADC ta ce yayin da jagororin nata ke ƙoƙarin ganin tsohon gwamnan “an turo manyan motoci aƙalla uku maƙare da jami’an ƴansanda zuwa ofishin”.
“Abin da muka lura da shi, shi ne ana amfani da tsarin gwamnati wajen cuzgunawa, da hantara ta hanyar tsarewa, da kuma ɗaukan duk wani mataki na ganin an karya gwiwar ginshiƙin ƴan adawa,” a cewar sanarwar.
A farkon wannan mako iyalan El-Rufai sun zargi hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa da ƙin ba su damar ganinsa a inda yake tsare.
Nasir El-Rufai - wanda ya yi ruwa da tsaki wajen goyon bayan zaɓen Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya - ya koma zamo ɗaya daga cikin wadanda suka fi sukar gwamnatin bayan ɓaɓewar da ɓangarorin biyu suka yi jim kaɗan bayan fara mulkin Tinubu.
Daga baya El-Rufai ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki inda ya koma jam'iyyar ADC ta haɗakar ƴan'adawa waɗanda suka lashi takobin kayar da Bola Tinubu a zaɓen shekara ta 2027.
Hukumomin Najeriya na tsare da tsohon gwamnan na jihar Kaduna ne tun ranar 17 ga watan Fabrairun 2026 kan wasu zarge-zarge da suka shafi rashawa da almundahana, waɗanda tuni ya musanta.
Haka nan Nasir El-Rufai yana fuskantar wata shari'ar da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS kan zargin satar sauraron wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.