Me kisan kwamandojin ISIS da Amurka ta yi a Najeriya ke nufi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Talatar nan ne hedikwatar tsaro ta Najeriya ta sanar da cewa haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasar da na Amurka ya yi sanadiyyar kashe mayaƙan ƙungiyar ISIS aƙalla 175 a arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar ta ce wannan ne lokaci mafi muni ga ƴan ƙungiyar sakamakon ayyukan dakarun ƙasashen biyu.

Sanarwar ta ƙara da cewa farmakin da dakarun suka kai wanda ya fara kwanaki ya kuma yi sanadiyyar lalata shingayen ƙungiyar da rumbunan makamansu da moɓayarsu.

Hedikwatar tsaron ta ce farmakin ya kashe manyan kwamandojin ƴan ƙungiyar ciki har mataimakin shugaban ISIS, da aka fi sani da Abu Bilal Al-Minoki, inda ta kuma ce rundunar za ta bi duk inda ƴan ta'adda suke domin ganin bayansu.

Kwamandojin ISIS/ISWAP da aka kashe

Hedikwatar tsaron a cikin sanarwar ta ce cikin ƴan ƙungiyar 175 da ta kashe a farmakin na kwanaki sun haɗa da kwamandoji na ISIS da ISWAP kamar haka:

  • Abu Bilal Al-Minoki - Mataimakin shugaban ISIS.
  • Abd-al Wahhab - Kwamanda mai kitsa hare-hare da watsa farfaganda.
  • Abu Musa al-Mangawi - Jigo a ISWAP.
  • Abu al-Muthanna al-Muhajir - Babban mai kula da kafafen watsa labarai kuma makusancin al-Minoki.

Ko kisan kwamandojin zai daƙile ta'addanci?

Malam Kabiru Adamu ya ce lallai alaƙar ta tsaro tsakanin ƙasashen biyu za ta taka rawar gaske amma kuma hakan ba zai kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a ƙasar ba, inda ya ce dole sai Najeriya ta bi wadannan hanyoyin kafin ta ci ribar taimakon da Amurkar ta yi mata.

  • Magance abubuwan da ke janyo ta'addanci: Dole ne sai ita Najeriya ta yi ƙoƙarin magance ababan da ke haifar da ta'addanci kamar talauci, cin hanci da rashawa, rashin ingantacciyar gwamnati da ɗumamar yanayi da kuma dabarun saka jama'a cikin tafiya da haɓaka tattalin arziƙi da kuma sauya tunanin ƴan ta'adda.
  • Hana ƙungiyoyin ta'addanci farfaɗowa: Wani abu shi ne dole a yi ƙoƙarin hana ƙungiyoyin sake yunƙurowa bayan kashe shugabanninsu saboda suna da wannan ƙwarewar.
  • Dabarun hana yaɗuwar ƙungiyoyin ta'addanci: Sannan akwai matsalar ita kanta Amurka wajen yadda ƙungiyoyin ƴan ta'adda ke kallon ta kasancewar ba sa son Amurka saboda duk lokacin da ita Amurka ta kai musu hari a kan wata ƙasa to ƙungiyoyin ta'adda kan yi gayya su addabi wannan ƙasa. Saboda haka dole Najeriya ta san dabarun bayanan da za ta rinƙa fitarwa domin yaƙar hakan. kuma hakan ne zai hana su ɗaukar sabbin mabiya da kuma toshe musu hanyoyin samun kuɗi.
  • Cigaba da kai hare-hare: Sannan kuma dole ne a ci gaba da kai hare-hare zuwa maɓoyar ƴan ta'addar - sanannun wuraren guda huɗu ne.

Tasirin haɗakar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya

Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Consulting Firm ya ce alaƙar tsaron tsakanin ƙasashen biyu na da fa'ida.

"Mun san cewa Amurka ta yi ta turo jiragenta daga Ghana domin tattara bayanan tsaro kuma da alama kwalliya ta byu kudin sabulu musamman bisa la'akari da yadda hadakar ta yi sanadiyyar kashe manyan jagororin ƴan ta'adda," in ji Kabiru.

"Sojojin Amurka sun yi fice a duniya saboda ƙwarewa da kayayyakin aiki da suke da shi da kuma cewa ƴan siyasarsu suna mara musu baya. Sannan shugaba Trump ya ƙarfafa ma'aikatar tsaron Amurka ta hanyar sauya sunan ma'aikatar zuwa ma'aikatar yaƙi," in ji Kabiru.

Sai dai kuma ya ce akwai abin da ya kamata Najeriya ta yi kafin cin moriyar haɗakar.

"Wannan haɗaka tsakanin Najeriya da Amurka tana da kyau sosai kuma idan Najeriya ta bi Amurka ta hanyoyin siyasa da diflomasiyya domin ƙulla dangantaka tsakaninsu zai taimaka wa manufarta ta magance matsalar tsaro a cikin gida."

Ribar da Najeriya za ta samu

Malam Kabiru Adamu ya lissafa ƙarin wasu abubuwa guda uku da ya ce su ne manyan ribar da Najeriya za ta samu sakamakon haɗakar tsaron

  • Bai wa Najeriya bayanan sirri.
  • Rage matsaloli dangane yadda Najeriya take aikinta na soji da suka haɗa shugabanci da kayan yaƙi.
  • Sauya sunan Najeriya daga mai yawan ta'addanci