Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda jam'iyyar kyankyasai ke samun karɓuwa a Indiya
- Marubuci, Zoya Mateen
- Aiko rahoto daga, Delhi
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
An samu wani tambarin jam'iyya mai ban-mamaki a siyasar ƙasar Indiya: Kyankyaso.
Ba fure ba irin na babbar jam'iyyar ƙasar (BJP), ko tambarin hannu na jam'iyyar adawa, wannan karo Kyankyaso ne - mai taurin kai, abin ƙyama kuma mai wuyar halakawa - wanda a baya-bayan nan ya zama wani mashahurin abu da ake alaƙantawa ga matasa a siyasar ƙasar Indiya.
Kyankyaso ya yi ƙaurin suna ne a Indiya daga makon jiya bayan wani kalami na ministan shari'ar ƙasar Surya Kant.
A lokacin wani zama, ministan ya kwatanta matasan ƙasar marasa aikin yi waɗanda ke shiga harkar hanƙoro da kuma aikin jarida a matsayin kyankyasai ko kuma kaska.
Daga baya ya yi ƙarin haske, inda ya ce mutanen da ya kwatanta da kyankyasai su ne "masu takardun karatu na bogi", ba duka matasan Indiya ba.
To amma ko gabanin haka, kalaman nasa sun karaɗe ko ina a shafukan sada zumunta, lamarin da ya haifar da gagarumar muhawara da kuma samar da tushen wata tafiyar siyasa da aka yi wa laƙabi da "Jam'iyyar Al'umma Kyankyasai", wato 'Cocroach Janta Party' ko kuma Cockroach Peoples Party' (CJP).
Jam'iyyar ba kamar sauran jam'iyyu ba ne da hukuma ta amince da su, sai dai jam'iyya ce ta wasu dandazon mutane da ke wa juna ba'a, kuma ƙa'idar shigar ta su ne wajibi ne mutum ya kasance ba shi da aikin yi, ya kasance raggo, kuma mai hawa intanet a koda yaushe, kuma mai yawan surutu.
Wani ƙwararre kan yaɗa labarai kuma ɗalibi a Jami'ar Boston, Abhijeet Dipke ne ya kafa jam'iyyar. Ya bayyana cewa ya fara abin ne a matsayin raha kawai.
Mutumin wanda a yanzu yake zama a A,murka, ya ce yi aiki da jam'iyyar Aam Aadmi Party (AAP) ta Indiya kafin tafiya Amurkar, wata jam'iyya wadda ta samo asali daga wasu gungun masu yaƙi da ayyukan rashawa kuma ta shahara sosai a shafukan sada zumunta.
Ya shaida wa BBC cewa :"na yi tunanin bari kawai mu haɗa wata ƙungiya".
Sai dai abin da ya biyo baya ya zarce abin da ya yi tsammani.
A cikin kwanaki ƙalilan, sabuwar jam'iyyar ta CJP ta samu dubun dubatar masu son shiga cikinta ta hanyar wani fom ɗin intanet, tare da taken #Ni ma kyankyaso ne, kuma ya samu amincewar jagororin sauran jam'iyyun adawa.
Tafiyar ta kuma samu karbuwa sosai a shafukan sada zmunuta, inda matasa suka riƙa wallafa kansu da shiga irin ta kyankyasai.
Sai dai yanzu haka da alama an soke wani shafin jam'iyyar a shafin X wanda yake da mabiya sama da 200,000, inda ake tura wa masu neman shiga shafin cewa an dakatar da shi "saboda buƙata ta shari'a".
To sai dai jam'iyyar na ci gaba da samun ƙarin farin jini.
Magoya bayan tafiyar na bayyana jam'iyyar a matsayin "sabon ƴanci" a wani mummunan yanayi na siyasa wanda aka yi wa mummunan dabaibayi.
Magoya bayan tafiyar sun haɗa da mashahuran ƴan adawa kamar Mahua Moitra da Kirti Azad da kuma wani babban lauya Prashant Bhushan.
Masu sukar tafiyar kuwa na kallon jam'iyyar a matsayin wani dandali mai alaƙa da ƴan adawa, inda suke kafa hujja da alaƙar Dipke da jam'iyyar AAP, sannan suna bayyana lamarin a amatsayin boren yuyuyu na siyasa.
Sai dai baya ga abubuwan da ake gani a zahiri, wannan na nuna irin gajiyar da matasan Indiya suka yi da lamurran siyasa, wadanda ke ganin duk da cewa suna da masaniya kan siyasa to amma ba sa jin cewa suna da wakilci.
Indiya na cikin jerin ƙasashen duniya masu ɗimbin matasa, inda kimanin rabin al'ummarta biliyan 1.4 ke ƙasa da shekara 30, sai dai akwai ƙarancin shiga harkokin siyasa.
Wani nazari da aka yi a baya-bayan nan ya nuna cewa kashi 29% na matasa Indiyawa na ƙaurace wa siyasa, yayin da kashi 11% ne kawai na matasa ke da katin jam'iyya.
"Mutane sun gaji, kasancewa suna ganin ba a martaba ra'ayoyinsu kuma ba sa jin cewa lallai suna da wakilci," in ji Dipke.