Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Bassirou Faye da Ousmane Sonko suka raba gari?
Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya sallami firaministan ƙasar, Ousmane Sonko bayan shafe tsawon watanni ana takun saƙa tsakanin mutanen biyu.
Matakin korar - wanda aka bayyana ta gidan talbijin na ƙasar - na zuwa ne bayan zazzafar muhawarar da aka yi a majalisar dokokin ƙasar, inda firaministan ya fito fili ya soki shugaba Faye.
Da yake martani kan sallamar tasa, Mista Sonko ya wallafa saƙo a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce yau zai yi barci cikin natsuwa a gidansa.
Jagororin biyu sun riƙa samun saɓani kan abubuwa da dama masu alaƙa da gwamnati da kuama aƙida.
Aminan juna da suka ɓaɓe
Diomaye Faye da Osmane Sonko sun karɓi mulkin Senegel a watan Maris ɗin 2024.
A lokacin da suka karɓi mulki an riƙa musu taken "Diomaye moy Sonko, Sonko moy Diomaye" (Diomaye na Sonko, Sonko na Diomaye").
Mutanen biyu na da kyakkyawar alaƙar siyasa a lokacin da jam'iyyarsu ta samu nasarar kayar da ɗan takarar jam'iyya mai ci da ke samun goyon bayan tsohon shugaban ƙasar, Macky Sall.
Mista Sonko, wanda ke samun goyon bayan matasan ƙasar a lokacin, ya zaɓi Faye a matsayin wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta lokacin a madadinsa kasancewar an haramta masa tsayawa takara.
A wani yunƙuri na rama biki, bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa Bassirou Faye ya saki Sonko daga gidan yarin da yake ɗaure, sannan ya naɗaa shi matsayin firaministan ƙasar, kuma shugaban gwamnati.
Sai dai shekara biyu bayan fara mulki, sun fara samun saɓani a tsakaninsu, wani abu da ya ci gaba da ruruwa har zuwa matakin raba gari.
Me ya shiga tsakanin su?
Bayanai na cewa shugabannin biyu sun fara samun saɓani ne kan iko tsakanin shugaban ƙasar da mutumin da ya taimaka aka zaɓe shi.
Ousmane Sonko ya nuna alamun ficewa daga jam'iyyar Faye domin komawa ta hamayya.
Amma a nasa ɓangare Bassirou Diomaye Faye ya saka sharaɗin ci gaba da aiki da Sonko kan ƙwarin gwiwar da zai ci gaba da nunawa, yana mai cewa daga ranar da ya rasa ƙwarin gwiwar zai maye gurbinsa.
A ranar 2 ga watan Mayun da muke ciki ne Shugaba Faye ya nemi fayyace anmgantar da ke tsakanisa da Sonko a hira da kafar yaɗa labaran ƙasar.
Bassirou Diomaye Faye ya ce sun jima suna samun saɓani da Sonko, amma suke dannewa ba tare da barin duniya ta sani ba.
Shi ma Osmane Sonko a baya-bayan nan ya bayyana wa jama'a cewa akwai saɓani tsakaninsa da Shugaba Faye kan batutuwan siyasa masu yawa.
Waɗannan kalaman da jagororin biyu suka yi sun ƙara tsamin dangantaka tsakaninsu.
A baya-bayan kuma Shugaba Faye ya sanar da naɗin Ms. Aminata Touré domin ta jagorancin ƙawancen jam'iyyun PASTEF da suka kai shi ga nasara a zaɓen 2024.
To sai dai Sonko ya nesanta kansa da naɗin, yana mai cewa naɗin nata ya saɓa wa ƙa'idojin ƙawancen jam'iyyun.