Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 23/05/2026

Wannan shafi labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 23/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Mutum uku ke neman takarar shugaban ƙasa a PRP

    Jam’iyyar adawa ta PRP a Najeriya ta tantance mutum uku da suke neman tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta.

    Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Kwamared Muhammed Ishaq, ya fitar ta ce akwai sama da ƴan takara 260 da ke neman muƙamai daban-daban a ƙarƙashin jam’iyyar a Najeriya.

    ’Yan takarar da PRP ta tantance da ke neman tikitin takarar shugaban ƙasar sun haɗa da Dr. Nnaoke Ufere daga jihar Abia, da Engr. (Dr.) Yakubu Mohammed Kingsley daga jihar Edo, da Donald Duke, tsohon gwamnan jihar Cross River.

    Jam'iyar ta ce za ta gudanar da dukkanin zaɓukan fitar da gwanin jam'iyyar a ranar Litinin, 25 ga Mayu, 2026 a sassa daban-daban na ƙasar.

  2. Na yaba wa gwamnonin APC kan yadda suke tafiyar da zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ya ce gwamnonin ƙasar sun shirya tare da gudanar da zaɓukan fitar da gwani a faɗin jihohisu.

    Yayin da yake jawabi a mazaɓarsa ta Ikoyi bayan ya halarci zaɓen, Shugaba Tinubu ya ce ya ji daɗin yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana kamar yadda aka tsara.

    ''Wannan shi ne siyasa, siyasa ta tun daga tushe, inda kowane mambar jam'iyyarmu ke da damar shiga zaɓen kamar ni ma yadda na zo na yi'', in ji shi.

    Shugaban Tinubu ya ƙara da cewa hakan ya nuna cewa Najeriya tana da tsarin dimokraɗiyya mai ƙarfi.

    ''Haƙiƙa na gamsu da yadda gwamnoni suka yi ƙoƙari a jihohinsu, wajen tarukan jam'iyyarmu tun daga matakin mazaɓa da ƙananan hukumomi da kuma zaɓukan fitar da gwani da tantance ƴantakara'', in ji shi.

  3. Rukunin ƙarshe na maniyyatan Najeriya sun nufi makka daga binrin Madina

    Rukukin Ƙasashe na maniyyatan Najeriya sun nufi birnin Makka, bayan da suka bar Madina domin fara shirye-shirye aikin hajjin bana.

    A cikin makon nan ne hukumar Alhazan ƙasar Nahcon ta sanar da kammala jigilar maniyyatan ƙasar zuwa ƙasa mai tsariki.

    A bana hukumar ta kammala jigilar maniyyatan cikin hanzari, wani abu da zai taimaka musu kammala shirye-shiryen aikin hajjin cikin nutsuwa.

    Jigilar maniyyatan a kan lokaci ta taimaka wa da dama daga cikin samun damar yin ziyara a birnin Madina, gabanin fara aikin hajjin.

    Nahcon ta ce da zarar maniyyatan sun isa birnin Makka za su yi Umara kafin fara aikin hajjin.

    A ranar Litinin ne maniyyatan za su fara aikin hajjin bana, inda za su fita zuwa filin Minna da ke wajen garin Makka.

    A ranar Talata ne kuma za su yi tayuwar Arfa, ɗaya daga cikin muhimman ginshikan aikin hajji.

  4. Me ya sa Bassirou Faye da Ousmane Sonko suka raba da gari?

    Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya sallami firaministan ƙasar, Ousmane Sonko bayan shafe tsawon watanni ana takun saƙa tsakanin mutanen biyu.

    Matakin korar - wanda aka bayyana ta gidan talbijin na ƙasar - na zuwa ne bayan zazzafar muhawarar da aka yi a majalisar dokokin ƙasar, inda firaministan ya fito fili ya soki shugaba Faye.

    Da yake martani kan sallamar tasa, Mista Sonko ya wallafa saƙo a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce yau zai yi barci cikin natsuwa a gidansa.

    Jagororin biyu sun riƙa samun saɓani kan abubuwa da dama masu alaƙa da gwamnati da kuama aƙida.

  5. Kamfanin SpaceX ya kammala gwajin kumbonsa mafi girma a duniya

    Kamfanin SpaceX ya kammala gwaji na 12 kan kumbonsa mai suna Starship, wanda hukumar sararin samaniya ta Amurka (NASA) ke shirin yin amfani da shi wurin zuwa duniyar wata nan gaba.

    Starship - wanda shi ne kumbo mafi girma kuma mafi ƙarfi a tarihi ya tashi ne daga jihar Texas.

    Daga shigarsa sararin samaniya Starship ya buɗe kofofinsa ya saki tauraron ɗan'adam na gwaji guda 20 kafin ya sauko ya faɗa a teku.

    Gwajin kumbon dai na zuwa ne gabanin shirin da ake yi na sayar da hannayen jarin kamfanin SpaceX - mallakin hamshakin attajirin nan Elon Musk.

  6. Amurka ta buƙaci masu son zaman ƙasar dindindin su fita daga cikinta su sake neman izini

    A wani babban matakin sauyi da aka ɗauka kan manufofin shige da ficen Amurka, gwamnatin Trump ta sanar da cewa akasarin ƴan ƙasashen waje da ke neman izinin zama a ƙasar na dindindin (Green Card) su fita daga ƙasar kafin su miƙa buƙatarsu a ofishin jakadanci.

    Wani mai magana da yawun hukumar shige da fice ta Amurka ya ce sabuwar manufar ta rage buƙatar nema da kuma korar waɗanda aka hana su izinin zama a ƙasar.

    Lauyoyin shige-da-fice da ƙungiyoyin bayar da agaji sun ce akwai yiyuwar sauyin zai haifar da rarrabuwar iyalai da kuma tilasta wa waɗanda suka tsira daga fataucin mutane da tashin hankali komawa ƙasashen da suka tsere daga cikinsu .

  7. Yusuf Tuggar ya sha kaye a zaɓen fitar da gwanin gwamnan Bauchi

    Toshon ministan harkokin wajen Najeriya, Ambassador Yusuf Tuggar, da Bala Maijama’a A. Wunti, tsohon babban jami'in kamfanin mai na Najeriya, NNPLC sun sha kaye a zaɓen fitar da gwanin takarar gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC.

    Rahotonnin jaridun Najeriya sun ce an jinkirta sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Alhamis, har zuwa safiyar yau Asabar, inda aka sanar da tsohon gwamnan jihar , Mohammed Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    A shekarar 2019 ne Barister Mohammed Abubakar, da aka fi sani da MA ya sha kaye a hannun Bala Mohammed na jam'iyar PDP.

    Yusuf Tuggar na cikin ministocin Tinubu na farko da suka ajiye muƙamansu domin tsayawa takara a zaɓen 2027 kamar yadda dokar zaɓen ƙasar ta danatar.

    A ƙarshen watan Maris ne tsohon ministan harkokin wajen Najeriyar ya sauka daga muƙaminsa don tsayawa takara

  8. Babban hafsan sojojin Pakistan ya gana da Araghchi don kawo ƙarshen yaƙin Iran

    Babban hafsan sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir - da ke bulaguro a Tehran - ya gana da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, domin tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce shugabannin biyu sun tattauna hanyoyin diplomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurkja, tare da ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a yankin Yammacin Asiya.

    Wannan ce ziyarar Munir ta biyu zuwa Tehran cikin makonni.

    Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ministan harkokin cikin gidan Pakistan ke ziyara a Iran.

    Pakistan na ƙokarin shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka.

  9. Jam'iyyar APC na gudanar da zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa

    A yau ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasar, domin zaɓen mutumin da zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

    Za a gudanar da zaɓen ne ta hanyar ƴartinƙe kamar yadda jam'iyyar ta tsara.

    Cikin sanarwar zaɓen da ta fitar, APC ta ce ta tsara gudanar da zaɓen ne bayan kammala na gwamnoni da na ƴan majalisun tarayya.

    Mutum biyu ne ke fafatawa a zaɓen na yau, wato Shugaba Bola Tinubu da ke neman wa'adin mulkin na biyu, sai kuma Stanley Osifo da ke ƙalubalantarsa.

    Daraktan yaɗa labaran sakatariyar jam'iyyar, Mallam Bala Ibrahim ya ce za a gudanar da zaɓukan a duka mazaɓun ƙasar.

  10. An samu ɓullar Ebola a lardunan da ake rikici a DR Congo

    Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ta ce yanzu haka an samu rahoton ɓullar cutar Ebola a wasu lardunan gabashin ƙasar da ke fama da rikici.

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce yana da muhimmanci a iya gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar.

    Wani jami'in hukumar mai kula da nahiyar Afirka, Otim Patrick Ramadan ya ce ana samun ƙaruwa adadin waɗanda ake tunanin suna ɗauke da cutar, kuma hakan abu ne mai kyau, saboda yana bayar da damar a hana cutar yaɗuwa a cikin al'umma.

    Sama da mutum 700 ne suka kamu da cutar ta Ebola, yayin da sama da mutum 170 suka mutu.

  11. Shugaban Senegal ya sallami firaministan ƙasar Ousmane Sonko

    Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya sallami firaministan ƙasar, Ousmane Sonko bayan shafe tsawon watanni ana takun saƙa tsakanin mutanen biyu.

    Matakain korar wanda aka bayyana ta gidan talbijin na ƙasar, na zuwa ne bayan zazzafar muhawarar da aka yi a majalisar dokokin ƙasar, inda firaministan ya fito fili ya soki shugaba Faye.

    Da ya ke martani kan sallamar tasa, Mista Sonko ya wallafa saƙo a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce yau zai yi barci cikin natsuwa a gidansa.

    Jagororin biyu sun riƙa samun saɓani kan abubuwa da dama masu alaƙa da gwamnati da kuama aƙida.

    A baya-bayan nan dai Mista Sonko ya yi nuni da yiwuwar komawa jam’iyyar adawa, lamarin da masu sharhi ke ganin wani mataki ne na tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2029.

    A shekarar 2024 ne Mista Sonko, wanda ke samun goyon bayan matasan ƙasar a lokacin, ya zaɓi Faye a matsayin wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta lokacin a madadinsa kasancewar an haramta masa tsayawa takara.

  12. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ci gaba da bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan abaran da muke wallafawa.