Ko ƙungiyar JNIM a yankin Sahel ta raba gari da Al-Qaeda?

    • Marubuci, Mina al-Lami
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Ƙwararriya a harkokin masu jihadi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 10

Abubuwan da suka faru kwanan nan a ƙasar Mali, inda JNIM, reshen Al-Qaeda a yankin Sahel, ya haɗa kai da wata ƙungiyar 'yan aware da ba ta da aƙidar Musulunci wajen kaddamar da manyan hare-haren kwace yankuna a watan Afrilu da kuma watan Yuli, sun sake tayar da tambayoyi kan alaƙarsa da Al-Qaeda da kuma yiwuwar rabuwa da ita, ko da kuwa a matakin sanarwa ta hukuma ne kawai.

JNIM ta ci gaba da nuna ƙarfi a fagen yaƙi. Kwanan nan ta ɗauki alhakin wani babban hari da aka kai kan sansanin soji a tsakiyar Mali a ranar 10 ga Satumba, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar sojoji fiye da 100.

Ƙungiyar, wadda cikakken sunanta shi ne Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), har yanzu a hukumance tana matsayin reshe na Al-Qaeda, kuma tana ɗaya daga cikin rassanta biyu mafi ƙarfi tare da Al-Shabab ta Somaliya.

Sai dai a yau, JNIM ba ta yi kama da Al-Qaeda kamar da ba, ko ta fuskar bayyanar ƙungiyar ko kuma salon saƙonninta. Hakan ya haɗa da dabarun yaɗa bayanai ta kafafen yaɗa labarai, yadda take gina sunanta da kuma irin saƙonnin da take isarwa ga jama'a.

Ko da yake rassan Al-Qaeda galibi suna mayar da hare-harensu ne kan yankunan da suke aiki a ciki ko na kusa da su, amma salon saƙonnin JNIM ya yi nisa sosai daga tsohuwar akidar yaƙin jihadi ta duniya da Al-Qaeda ta saba yi.

A cikin 'yan shekarun nan, JNIM ta fi mayar da hankali kusan gaba ɗaya kan yankin Sahel.

Ta kuma kauce wa manyan batutuwan da suka shafi duniyar Musulmi, musamman batun Falasdinu, wanda ke taka muhimmiyar rawa a farfagandar Al-Qaeda da manufofinta da take bayyana a fili.

Haka kuma, ƙungiyar ta daina fitar da sanarwar haɗin gwiwa ko shiga kamfen ɗin da ake gudanarwa tare da sauran rassan Al-Qaeda. Bugu da ƙari, ta rungumi salon magana mai sassauci da sulhu ga wasu daga cikin abokan adawarta, sabanin yadda aka saba ganin ƙungiyoyin jihadi masu tsattsauran ra'ayi suna yi

Har ila yau, JNIM ta yi watsi da alamomin tantancewa da salo na musamman na Al-Qaeda waɗanda a da suke bayyana sosai a manyan bidiyoyin farfagandarta.

A aikace kuwa, ƙungiyar ta ƙulla haɗin gwiwa da 'yan aware na ƙabilar Tuareg masu ra'ayin kishin ƙasa, sannan ta bayyana aniyarta ta ci gaba da hulɗa cikin "daidaito" da "ɓangaren Rasha", tana nufin dakarun African Corps na Rasha da ke aiki a Mali.

Waɗannan sauye-sauyen na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara a tsakanin masu ra'ayin jihadi kan ko rungumar salon siyasa mai sassauci da anfani da dabarun pragmatism zai iya zama hanya mafi dacewa ta kaiwa ga karɓar iko.

Wannan muhawarar ta samo asali ne bayan da ƙungiyoyin jihadi na ƙasa da ƙasa suka sha gazawa wajen ƙwace yankuna da riƙe su na dogon lokaci.

A gefe guda kuma, Taliban a Afghanistan da kuma, a baya-bayan nan, Hay'at Tahrir al-Sham (HTS) a Syria, sun samu nasarar karɓar iko da iko da yankuna, abin da ya sa wasu ke ganin cewa sassauci da mayar da hankali kan manufofin cikin gida na iya fi ba da sakamako fiye da tsattsauran ra'ayin jihadi na duniya.

Wannan nazari yana duba alamomin da ke nuna cewa JNIM na iya kasancewa tana neman nesanta kanta da Al-Qaeda, ko dai ta hanyar rabuwa a hukumance ko kuma ta hanyar ƙara rage alaƙarta da wannan babbar hanyar sadarwar jihadi ta duniya.

Irin wannan sauyi ba lallai ne ya nuna cewa an samu cikakkiyar katsewar dangantaka tsakanin ƙungiyoyin biyu ba.

A maimakon haka, yana iya kasancewa sakamakon wata fahimtar juna ko yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, tare da zama wata dabarar siyasa da aka tsara domin inganta damar JNIM ta shiga harkokin siyasa da samun karɓuwa a cikin gida.

Haka kuma, irin wannan mataki na iya taimakawa wajen kwantar da hankulan masu fargabar cewa Al-Qaeda na ƙoƙarin karɓar iko ko kafa cikakken tasiri a Mali.

Ta wannan hanyar, JNIM za ta iya gabatar da kanta a matsayin ƙungiya mai mayar da hankali kan al'amuran cikin gida da na yankin Sahel, maimakon a gan ta a matsayin wani reshe kai tsaye na wata ƙungiyar jihadi ta duniya.

Mayar da hankali kan batutuwan cikin gida da masu ruwa da tsaki

A cikin shekaru biyu da suka gabata, JNIM ta ƙara karkatar da saƙonninta zuwa batutuwan ƙorafe-ƙorafe na cikin gida da na ƙasa, maimakon manyan batutuwan jihadi na duniya.

Yayin da a baya take yin tsokaci kan al'amuran da suka shafi al'ummar Musulmi ta duniya (ummah), ciki har da batutuwan Afghanistan, Gaza, Syria da kuma zane-zanen barkwanci na Annabi Muhammad a Faransa, ba ta sake fitar da wata sanarwa a fili kan wani batu da bai shafi yankin Sahel ba tun watan Disamban 2024.

Akasin haka, kusan dukkanin saƙonninta sun mayar da hankali ne kan Mali, Burkina Faso da yankin Sahel gaba ɗaya, inda take bayyana gwamnatocin yankin a matsayin masu cin hanci da rashawa da kuma wakilan ƙasashen waje masu amfani da su wajen aiwatar da manufofinsu.

Tun lokacin da ta ƙaddamar da babban harinta a Mali a ranar 25 ga Afrilu, 2026, kusan dukkan sanarwar da ƙungiyar ta fitar sun mayar da hankali ne kan cigaban siyasa da na soji a cikin ƙasar.

Daga cikin waɗannan sanarwar, aƙalla guda goma sha shida sun yi Allah-wadai da abin da JNIM ta zargi gwamnatin Mali da kuma abokan huldarta na Rasha da aikatawa, wato cin zarafi da kisan fararen hula da take cewa an yi wa "civilians" a yayin ayyukan soji.

Dukkan sanarwar biyu sun goyi bayan aiwatar da Shari'ar Musulunci, amma sun fi ba da muhimmanci ga batutuwan tsaro, adalci, kyakkyawan shugabanci da wadata.

Misali, sanarwar Afrilu ta gabatar da Shari'a a matsayin ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da za su kasance cikin wani "tsarin miƙa mulki na adalci, zaman lafiya da haɗin kai", maimakon ta sanya ta a matsayin babban ginshiƙin shirin.

Sai dai kuma da wuya JNIM ta yi watsi gaba ɗaya da ambaton Shari'a, domin hakan na iya jawo fushin mambobinta masu tsattsauran ra'ayi tare da haifar da tunanin cewa ta yi watsi da tushen akidarta ta jihadi domin neman moriyar siyasa. Irin wannan ƙalubale ne ma Hay'at Tahrir al-Sham (HTS) ta fuskanta a Syria.

A watan Yunin 2026, JNIM ta yi ƙoƙarin gabatar da kanta a matsayin mai ruwa da tsaki ta fuskar siyasa ta hanyar bayar da ladan Yuro miliyan biyu (€2m) ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga "kawar da" ko gano inda shugaban mulkin sojin Mali, Assimi Goïta, yake.

Haka kuma, ta yi alƙawarin bayar da Yuro miliyan ɗaya (€1m) kan kowane ɗaya daga cikin wasu manyan jami'an soja biyu.

An rubuta wannan tayin lada na JNIM ne da harshen Faransanci, kuma ya yi kama da ladan dala miliyan 12.4 da shugabannin Mali suka sanar a baya domin kamo shugabannin JNIM da kuma ƙungiyar FLA.

Ta hanyar amfani da wata dabara da gwamnatoci kan yi amfani da ita wajen neman waɗanda suke nema ruwa a jallo, JNIM kamar tana ƙoƙarin juya matsayin ɓangarorin biyu. Wato tana son gabatar da gwamnatin mulkin sojin ƙasar a matsayin wadda take karya doka ko ta fita daga tsarin halacci, maimakon ita kanta ƙungiyar.

Haɗa kai da ƙungiyoyin ƴan aware

Wata muhimmiyar alama da ke nuna yadda JNIM ke ƙara rungumar siyasar amfani da abin da ya dace da lokaci ita ce shirinta na fito-na-fito wajen haɗa kai da Azawad Liberation Front (FLA), wata ƙungiyar 'yan aware da ba ta da akidar Musulunci. Wannan na da muhimmanci saboda JNIM ta daɗe tana bayyana cewa manufarta ita ce kafa tsarin mulki bisa Shari'ar Musulunci.

Tun bayan farmakin haɗin gwiwa da aka ƙaddamar a watan Afrilu na 2026, JNIM ta fito fili tana amincewa da haɗin kai da FLA. Sau da dama tana kiran mambobin ƙungiyar da suna "abokan hulɗa", har ma "'yan'uwa", tare da yabawa abin da ta kira "jarumtakar" ayyukansu. Irin wannan harshe ba kasafai ƙungiyoyin jihadi ke amfani da shi wajen bayyana ƙungiyoyin kishin ƙasa ko marasa akidar addini ba.

Da alama wannan salon magana na nufin nuna cewa akwai gamayyar ƙarfi guda ɗaya da ke adawa da gwamnatin mulkin sojin Mali. Haka kuma yana taimakawa wajen ƙarfafa gwiwar abokan hulɗar cikin gida da kuma anfani da matsayin siyasa da FLA ke da shi fiye da na JNIM.

Gwamnatin Mali da kafafen yaɗa labaran da ke da alaƙa da ita sun zargi ƙasashen Aljeriya da Mauritaniya da goyon bayan FLA. Haka kuma an yi zargin cewa Ukraine da Faransa suna tallafa wa wannan ƙungiyar 'yan aware.

Bayan hare-haren watan Afrilu, JNIM ta ci gaba da ɗaukar alhakin hare-hare da dama a tsakiyar Mali, musamman a yankunan Mopti da Ségou.

Amma a game da arewacin ƙasar, musamman yankunan Kidal da Gao inda aka gwabza wasu daga cikin faɗace-faɗacen da suka fi tasiri, ƙungiyar ta yi magana kaɗan ne kawai game da ayyukanta, tana barin FLA ta fi ɗaukar ragamar bayyana abubuwan da suka faru.

Wannan na iya nuna cewa an ɗauki wata dabara ta ba FLA damar samun karin haske da karɓuwa a idon jama'a, yayin da ake guje wa jawo hankali sosai ga rawar da JNIM ta taka, wadda za ta iya haddasa muhawara ko suka.

A nata ɓangaren, FLA ta yi taka-tsantsan wajen bayyana dangantakarta da JNIM a matsayin haɗin gwiwa ta anfani da yanayi a filin daga, ba wani haɗin kan siyasa ko akida ba.

A watan Afrilu, FLA ta bayyana dangantakar tata da JNIM a matsayin "haɗuwar dabaru" domin kifar da gwamnatin mulkin sojin Mali.

Daga baya kuma, a watan Satumba, ta sake bayyana wannan haɗin kai a matsayin "haɗin gwiwar aiki", tare da jaddada cewa ba "ƙawancen siyasa" ba ne. Wannan bayani ya zo ne yayin da FLA ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da African Corps na Rasha game da zirga-zirgar sojoji da janyewarsu, sannan kuma tana neman goyon bayan Turkiyya.

Irin waɗannan matakai na iya amfani wa JNIM a kaikaice, domin suna ba ta damar anfani da halaccin siyasa da kuma damar mu'amala da ƙasashen duniya da FLA ke da shi.

A wata hira da ya bayar ranar 15 ga Satumba, kakakin FLA, Mohamed Elmaouloud Ramadane, ya ce duk wata tattaunawar da aka shirya domin kawo ƙarshen rikicin Mali dole ne ta haɗa da JNIM. A cewarsa, ƙungiyar tana ƙara amfani da "harshen siyasa" tare da gabatar da wani shiri da ya mayar da hankali kan buƙatun cikin gida.

A ɓangaren JNIM, wata hujja da za ta iya bayyana dalilin wannan haɗin kai ta fito ne a cikin wani saƙon murya da aka wallafa a ƙarshen watan Afrilu, wanda majiyoyin intanet masu aminci da ke kusa da Al-Qaeda suka danganta da ƙungiyar. Mai jawabin ya nuna cewa haɗin kai da 'yan aware na Tuareg ya yiwu ne saboda sun bayyana niyyar "kafa Shari'ar Musulunci".

Ana kallon wannan bayani a matsayin wani yunƙuri na rage matsin lambar akida da ka iya tasowa sakamakon haɗin gwiwar da JNIM ke yi da ƙungiyar da ba ta da akidar Musulunci.

Sai dai wannan ƙawance ya jawo suka daga masu tsattsauran ra'ayin jihadi, musamman daga ISIS, wanda ke gabatar da shi a matsayin hujjar cewa Al-Qaeda ta yi sulhu da abin da suke kira "masu ridda" domin cimma muradun siyasa.

Haka kuma, makomar dorewar wannan haɗin kai ba ta da tabbas.

Ko da yake ƙungiyoyin biyu suna da muradi guda a halin yanzu, wato kifar da gwamnatin mulkin sojin Mali, manufofinsu na dogon lokaci sun bambanta ƙwarai. FLA na neman cin gashin kai ko kuma 'yancin kai ga yankin Azawad a arewacin Mali, yayin da JNIM ke neman kafa tsarin mulki bisa Shari'ar Musulunci, tare da manufofin da suka zarce iyakokin Mali.

Irin waɗannan sabanin manufofi ne suka haddasa rugujewar haɗin kan magabatan ƙungiyoyin biyu a lokacin tawaye na shekarar 2012. Wannan na nuni da cewa haɗin gwiwar da ake gani a yau na iya kasancewa kawai "auren anfani" ne wanda zai ci gaba ne muddin suna da abokin gaba guda ɗaya.

Isar da saƙonnin kwantar da hankali ga abokan gaba

A lokaci guda da ta ƙaddamar da manyan hare-harenta na soja a ƙarshen watan Afrilu, JNIM ta kuma fara wani tsararren kamfen na sadarwa da aka tsara domin isa ga masu sauraro daban-daban, ciki har da al'ummomin yankin, masu yiwuwar zama abokan hulɗa, ƙasashen yankin, har ma da abokan adawarta.

Manufar ƙungiyar ba kawai nuna ƙarfin soja ba ce, har ila yau tana ƙoƙarin kwantar da hankalin waɗanda da sun iya shiga yaƙi a kanta ko taimaka wa abokan gabanta.

Kamar yadda Hayat Tahrir al-Sham (HTS) ta yi a Syria a ƙarshen shekarar 2024, da alama JNIM tana ƙoƙarin samar da yanayin da zai ba ta damar riƙe nasarorin da ta samu a filin daga, tare da kauce wa martanin ƙasashen yankin ko na duniya wanda a baya ya kan dakile ci gaban ƙungiyoyin jihadi a Mali.

Saboda haka, dabarun sadarwarta sun mayar da hankali kan abubuwa uku:

  • Tsoratar da manyan abokan gabanta kai tsaye, wato gwamnatin Mali da sojojinta.
  • Jan hankalin jama'ar yankin domin samun goyon baya ko akalla rashin adawa.
  • Rage yiwuwar ƙarin maƙiya ta hanyar gabatar da kanta a matsayin ƙungiya ta Mali mai neman sauyin siyasa a cikin ƙasa, maimakon ƙungiyar jihadi ta duniya.

A wani mataki da ba kasafai ake gani ba, JNIM ta sanar da dakarun African Corps, waɗanda ke da alaƙa da Ma'aikatar Tsaron Rasha kuma suke taimaka wa sojojin Mali, cewa ba za a kai musu hari ba muddin suka nisanta kansu daga faɗan.

Har ila yau, ƙungiyar ta bayyana cewa tana neman gina "dangantaka mai daidaito da inganci" da abin da ta kira "ɓangaren Rasha".

Haka kuma, ta yi wa sojojin Mali alƙawarin cewa za su kasance cikin aminci idan suka kaurace wa yaƙi ko suka ƙi fafatawa da ita.

Sai dai irin wannan salon saƙon ba sabon abu ba ne gaba ɗaya ga JNIM.

A shekarar 2021, ƙungiyar ta yi ƙoƙarin karkatar da ra'ayin jama'a a yankin Sahel da kuma Faransa kan gwamnatin Emmanuel Macron gabanin wani taron ƙasashen yankin kan yaƙi da ta'addanci da aka gudanar a Chadi.

A matsayin wani ɓangare na wannan kamfen, JNIM ta yi kira ga gwamnatocin ƙasashen Sahel da su dakatar da duk wani haɗin kai da Faransa idan suna son kauce wa hare-haren jihadi.

A cikin saƙonta ga waɗannan gwamnatoci, ƙungiyar ta ce:

"Wannan ba yaƙinku ba ne."

Masu nazari na ganin cewa irin waɗannan saƙonni na nuna yadda JNIM ke ƙoƙarin haɗa ƙarfin soja da dabarun siyasa, inda take son gabatar da kanta ba kawai a matsayin ƙungiyar yaƙi ba, har ma a matsayin wani ɗan wasa na siyasa da ke neman tasiri a makomar Mali da yankin Sahel.