Liverpool da Man United na hamayya kan Nmecha, Alexander-Arnold na nazari kan makomarsa a Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool da Manchester United na daga cikin ƙungiyoyin gasar Premier da ke zawarcin ɗan wasan tsakiya na Borussia Dortmund kuma ɗan ƙasar Jamus, Felix Nmecha. Liverpool na ganin ɗan wasan mai shekara 26, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 84, a matsayin wanda za ta iya ɗauka idan ta kasa samun ɗan wasan tawagar Ingila Alex Scott, mai shekara 23, daga Bournemouth. (Teamtalk)
Ɗan wasan tsakiya na Argentina, Emiliano Buendia, mai shekara 29, ya kusa cimma yarjejeniyar sabon kwantiragi da Aston Villa, bayan samun ci gaba a tattaunawar da ake yi. (Mail)
Ɗan wasan baya na tawagar Ingila, Trent Alexander-Arnold, na tunanin makomarsa a Real Madrid saboda rashin samun isasshen lokacin buga wasa. Tsohuwar ƙungiyarsa ta Liverpool na daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke sanya ido kan halin da ɗan wasan mai shekara 28 ke ciki. (Teamtalk)
Ficewar JJ Gabriel daga Manchester United ta kusa tabbata. Real Madrid ta gabatar da tayi mai tsoka domin ɗaukar ɗan wasan gaba na Ingila mai shekara 16, yayin da Barcelona da Bayern Munich ke nuna sha'awar ɗaukarsa. (Sport)
Manchester United na sa ido kan ɗan wasan baya ɗan ƙasar Brazil mai shekara 23, Wesley, wanda ke buga wa Roma wasa, gabanin yiwuwar ɗaukar sa a watan Janairu.
Rio Ngumoha ya nesanta kansa daga yiwuwar komawa Arsenal; ɗan wasan na gefe ɗan ƙasar Ingila mai shekara 18 ya bayyana cewa tattaunawa kan tsawaita kwantiraginsa a Liverpool na tafiya "yadda ya kamata". (Metro)
Tsohon ɗan wasan baya na Real Madrid da tawagar Spain, Sergio Ramos, na duba yiwuwar komawa Turai da buga wasa a gasar La Liga, inda ƙungiyar Getafe ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 40. (Four Four Two)
Manchester United na iya fuskantar gasa daga Juventus wajen ɗaukar mai horaswa ɗan ƙasar Italiya mai shekara 57, Antonio Conte, idan har suka kori babban kocinsu Michael Carrick. (Talksport)
Ana cewa Brighton ba ta da wata fargaba game da makomar kocinta Fabian Hurzeler, bayan ya fara kakar wasa ta bana cikin nasara. A cikin ƴan makonnin nan dai danganta kocin ɗan ƙasar Jamus mai shekara 33 da yiwuwar komawa Manchester United. (Football Insider)


























