KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 20/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 20/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Rabi'atu Kabir Runka

  1. Jihohi 7 da Tinubu zai fi fuskantar ƙalubale a zaɓen 2027

    Tinubu

    Yayin da zaɓen shugaban Najeriya na shekarar 2027 ke ƙara matsowa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar ƙalubalen siyasa a wasu jihohi da ka iya zama masa tarnaki, yayin da yake neman samun nasara domin yin wa'adi na biyu a zaɓen mai zuwa.

    Ko da yake jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara faɗaɗa tasirinta a siyasar ƙasar, wasu jihohi na iya zama ƙalubale ga Tinubu, musamman idan aka yi la'akari da tarihin siyasarsu, matsalolin da suke fuskanta da dai sauransu.

    Wani rahoto na Cibiyar Nazarin Zaɓe ta International Republican Institute (IRI) ya bayyana cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da rashin amincewar jama'a ga 'yan siyasa na daga cikin manyan abubuwan da za su iya tantance yadda zaɓen 2027 zai kasance.

    Farfesa Abubakar Kari, masanin harkokin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja da ke Najeriya, ya yi tsokaci kan waɗannan jihohi da kuma dalilan da za su iya sa Shugaba Tinubu ya fuskanci ƙalubale a cikinsu.

  2. An sanya dokar hana fita a birnin Paris Na Faransa

    PARIS

    An sanya dokar hana fita da daddare a wasu sassan biranen Paris da Lyon da Lille da kuma Nice, yayin da hukumomin Faransa ke ƙoƙarin daƙile tashin hankali da sace-sacen kayayyaki da suka addabi ƙasar tun ranar Asabar.

    An haramta gudanar da zanga-zanga a Paris babban birnin ƙasar, wanda ya fuskanci mafi munin tarzomar da ta samo asali daga zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa.

    Firaminista Sebastien Lecornu bai yi watsi da batun yiwuwar ayyana dokar ta-baci ba, bayan da Ministan Harkokin Cikin Gida ya amince cewa lamarin ya fi ƙarfin yansanda.

    Shugaba Macron dai ya bar ƙasar, inda ya fara ziyarar ƙasashen yankin Gulf.

  3. 'Ban yi nadamar cire tallafin mai ba, kuma ba zan taɓa mayar da shi ba'

    Bola Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce bai yi nadamar cire tallafin man fetur ba, wanda a baya-bayan nan ke ci gaba da ɗaukar hankali a ƙasar.

    A baya-bayan nan ne ƴantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyun hamayya ke bayyana matsayarsu kan tallafin man, ciki har da wanda ya ce zai mayar da shi idan ya ci zaɓen 2027.

    To sai dai yayin da yake jawabi a wani taro da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya a Abuja, shugaba Tinubu ya ce bai yi nadamar cire tallafin ba.

    "Ina jin yadda abokan hamayyata na siyasa ke yin alƙawarin dawo da tallafin man fetur," in ji Shugaba Tinubu.

    ''Batun mayar da tallafin man fetur, kamar ka ce Annabi Musa A.S ya koma Misra ne'', in ji shi, yana mai cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da ɗaukar nauyin biyan tallafin ba.

    Tinubu ya ce Najeriya na fuskantar haɗarin durƙushewa ta fuskar tattalin arziki idan ta ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin.

    “Da ra’ayoyinku ne na zo na cire tallafin mai tun daga ranar farko. A’a, Najeriya za ta durƙushe ta fuskar tattalin arziki. Babu wani abin da ya rage da za a ci gaba da biyan tallafin mai da shi,” in ji shi.

    Shugaban ya ce yana sane da cewa wasu daga cikin abokan hamayyarsa na siyasa sun yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur, amma ya jaddada cewa bai kamata Najeriya ta koma tsohuwar hanyar tafiyar da tattalin arzikinta ba.

  4. Ba ni da shirin komawa APC - Tambuwal

    Hoton tambuwal

    Tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma jigo a jam'iyyar ADC mai hammaya a Najeriya, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya musanta batun komawa jam'iyyar APC mai muli.

    Cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Tambuwal ya fitar, ya ce tsohon gwamnan na Sokoto ba shi da wani shiri na komawa APC, tare da bayyana cewa irin waɗannan ikirari ba su da tushe tare da yin watsi da su.

    Sanarwar ta ce Tambuwal na da alaƙa da abokantaka da ƴan siyasa daga jam'iyyu daban-daban sakamakon shekaru da ya shafe yana aikin gwamnati.

    Ta ce bai kamata a ɗauki irin waɗannan alaƙoƙi a matsayin alamar sauya sheƙar siyasa ba.

    Ofishin ya kuma ce hotuna da bidiyoyin da ake yaɗawa ba su tabbatar da wani shiri na sauya jam'iyya ba.

    Ya ƙara da cewa Tambuwal na ci gaba da kasancewa a ADC, kuma hankalinsa na kan ƙarfafa jam'iyyar da kuma shirye-shiryen tunkarar zaɓen shekarar 2027.

  5. Trump ya soki Zelensky kan jan ƙafar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

    Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa a shirye yake ya gana da shugabannin Rasha da China, bayan da kafofin yaɗa labaran Amurka suka rawaito cewa Vladimir Putin ya gabatar da shawarar gudanar da taron ƙolin da zai yanke hukunci kan makomar Ukraine.

    Sai dai Shugaba Trump ya ce ba za su mayar da hankali kan batun ba, a maimakon haka za su fi mayar da hankali kan kawar da makaman nukiliya.

    Rahoton Jaridar Wall Street Journal game da shawarwarin Mista Putin ya haifar da fargaba a Turai, da kuma Allah-wadai daga Kyiv.

    Mista Trump dai ya ci gaba sukar shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, inda ya ce watakila lokaci ya yi da wani daban zai gudanar da tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin ƙasar.

  6. Sallama

    Masu shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar Talata.

    Rabi'atu Kabir Runka ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.