Me ke janyo wa Super Eagles matsaloli a baya-bayan nan?

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya tana mataki na biyu a rukuni na 12 a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2027.
Hakan ya biyu bayan da Guinea Bissau ta doke Super Eagles 3-0 a wasan cikin rukuni ranar Talata a Estádio Nacional 24 de Setembro.
An fara cin Super Eagles ta hannun Franculino Djú a minti na 15 da fara wasan, kuma haka suka je hutu mai masaukin baki tana cin 1-0.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Guinea Bissau ta kara sa matsin da ta kai ta kara kwallo na biyu ta hannun Mama Baldé, sannan Álvaro Djaló ya kara na uku daf a tashi.
Da wannan sakamakon Guine Bissau ce ta daya a kan rukuni na 12 da maki shida, bayan da ta fara nasara a kan Tanzani 2-0 a wasan farko a rukunin.
Ita kuwa Najeriya tana da maki uku, saboda doke Madagascar 2-1 a wasan farko da ta yi a Uyo, yayin da Madagascar da Tanzania suke da maki daya kowwacce.
Me wannan rashin nasara da Super Eagles ta yi a Guinea Bissau ke nufi?
Kociyan Najeriya, Eric Chelle ya ce daga dalilan da ya sa suka yi rashin nasara har da rashin fili mai kyau da suka kara da Guinea Bissau da kuma rashin kyawun yanayi, sai dai ya ce ba su taka rawar da ya kamata su samu maki ba a fafatawar.
Rabon da Super Eagles ta yi rashin nasara da aka zura mata kwallaye da yawa tun wasan sada zumunta da Portugal da yi rashin nasara 4-0 ranar 17 ga watan Nuwambar 2022.
Kafin nan kuma Sifaniya ta doke Najeriya 3-0 ranar 23 ga watan Yuni a 2013 a Fifa Confederation Cup.
Kenan ba kasafai ake zura kwallaye da yawa a ragar Super Eagles ba, amma mai ya sa Guinea Bissau ta yi wannan namijin kokarin.
A tarihin karawar tsakanin ƙasashen biyu, Guinea-Bissau ta samu nasara ɗaya a wasannin baya, yayin da Najeriya ta ci fafatawa uku cikin karawa huɗu da suka gabata, kafin wannan da suka kara a Guinea Bissau.
A wasan neman gurbin AFCON na 2023, Guinea-Bissau ta ci Najeriya 1-0 a Abuja, kafin Super Eagles ta rama da ci 1-0 a Bissau.
Rashin nasarar da Najeriya ta yi a wannan karawar ya sa za ta kara shiga cikin matsi a wasannin da suke gabanta, domin neman gurbin Afcon 2027.
Shin mece ce matsalar Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Irin wannan sakacin ne ya sa Super Eagles ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya da aka yi a Amurka da Kanada da Mexico, duk da cewar kasa 10 ce ta wakilci Afirka a babbar gasar tamaula ta duniya.
Anas Sani Tkuntawa mai sharhi a fanni wasanni ya ce tun farko kociyan Super Eaglesa, Chelle ya gina tawagar Najeriya a kan Victor Osimhen da shi aka dogara da dorawa alhakin cin kwallaye, kuma sauran yan wasan sun fi mayar da hankali a lokacin da mai taka leda a Galatasaray ke cikin fili, sai dai yana jinya bai samu damar amsa goron gayyata ba.
Ya kuma ce za ka Super Eagles tana sa kwazo duk lokacin da Osinmen ke cikin fili, amma koda dan wasan ya je Guinea Bisau ba lallai ya sauya sakamakon karawar ba, amma dai karsashen yan wasan da rawar da za su taka za ta fi wadda suka kasa yin katabus.
Anas ya ce wasu manyan yan wasan Najeriya gani suke kamar alfarma suke yi wa Super Eagles da suke buga mata tamaula, ba sa saka kwazo kamar yadda suke yi a kungiyoyinsu na Turai.
Ya bayar da misalin yan wasan da ake fara karawa da su a Super Eagles irin su Frank Onyeka da Wulfred Ndidi da Alex Iwobi da Kelvin Bassy da kuma Ademola Lookman, ya ce idan kana kallon yadda suke taka leda a kungiyoyinsu na Turai suna taka leda bakin rai bakun fama, amma idan suna bugawa gida abin ba haka yake ba.
Haka kuma Anas ya ce ya kamata kociyan Najeriya ya sake dabaru wajen yan wasa 11 da yake fara karawa da su, dole ya zabo masu zafi da za su gajiyar da abokiyar hamayya daga baya ya saka wadanda za su karasa aiki.
Ya kuma yabawa kociyan wajen gayyatar sabbin yanwasa cikin tawagar da ya hada da Moses Usor da kuma George Ilenikhena, wadanda suka ci Madagascar a wasan farko da suka yi.

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Nura Garba Sabon Sara shima mai fashin baki a fannin wasanni ya fayyace yadda ake ganin matsalolin da ke tattare a Super Eagles.
Ya fara da cewar a baya yadda Nageriya ke taka leda tana amfani da gefen hagu da kuma dama wajen kai hari ba wuya an shiga cikin da'irar abokiyar hamayya, sannan kuma yan wasan gefe daga gaba, suna dawowa cikin yan tsakiya domin tare kalubale.
Ya ce a wasa biyun da Najeriya ta buga ba ta yi wannan salon ba yadda ya kamata, sai gurbin kai hari baya samun kwallaye da yawa a gaba.
Haka kuma Nuran ya ce rashin Victor Osimhen ya sa an rasa mai matsawa masu tsaron bayan abokan hamayya, kenan hakan yana sawa matsi na hawan Super Eagles, domin ba ta samu mai salon irin taka ledarsa ba.
Saboda haka ya ce a wasannin da Super Eagles take buga wa an rage kai hare-hare da kuma amfani da gefe yadda ya kamata, sannan yan wasa ba sa sak kwazo irin na kishi, suna taka leda kamar karawar ba ta dame su ba.
Kasa nawa ne za su samu gurbi a rukuni na 12?

Asalin hoton, Getty Imagaes
Za a gabatar da gasar cin kofin Afirka tsakanin kasa uku da ya hada da Kenya da Uganda da kuma Tanzaniya a shekarar 2027.
Rukuni na 12 ya kunshi Guine Bissau da Najeriya da Tanzani da kuma Madagascar - kenan tunda mai masukin baki tana cikin rukunin kenan kasa daya ake buga da za ta samu tikitin shiga wasannin bado.
Kenan duk wadda ta kammala wasaninta da maki mafi rinjaye, ita ce za ta je babbar gasar kwallon kafa ta Afirka da za a yi a badi a 2027.
Ita Tanzani da take mai masaukin baki tana cikin wannan rukunin ne, domin ta samu damar hada yan kwallon da za su taka mata rawa a wasannin badi.
Wasan gaba da Najeriya za ta kara shi ne na sada zumunta da Jamaica ranar 6 ga watan Oktoba, sannan kuma



























