Ko Portugal ta fara haƙura da Ronaldo ne?

Ronaldo
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Cristiano Ronaldo ya samu kansa a benci a wasan da Portugal ta doke Norway da ci 2-1 a gasar UEFA Nations League ranar Lahadi 27 ga Satumba 2026.

Ronaldo bai shiga karawar ba kwata-kwata, duk da cewa yana cikin ƴan wasan tawagar, kuma karo na uku da hakan ta faru da shi.

Wannan shi ne karon farko cikin fiye da shekara 18 da Ronaldo ya zauna a benci tsawon mintuna 90 a wasan Portugal ba tare da ya taka leda ba.

Rabon da hakan ta faru da shi tun a wasan Euro 2008 da Portugal ta yi rashin nasara a hannun Switzerland.

Me ya sa kociya, Jorge Jesus ya ajiye Ronaldo a benci?

Kocin Portugal, Jorge Jesus, ya bayyana cewa har yanzu tsohon ɗan wasan Manchester United da Real Madrid da Juventus yana cikin tsarinsa.

A cewar Jesus, Ronaldo ya buga kusan mintuna 70 a wasan da Portugal ta doke Wales da ci 1-0 ranar Alhamis, 24 ga Satumba.

Saboda haka kwanaki uku kacal tsakani bayan wasan, Jesus ya ga cewa bai dace Ronaldo ya fara wasanni biyu a jere ba, saboda haka ya hutar da shi.

"Ronaldo ya buga kusan mintuna 70 a wasan Wales, kuma naga bai kamata ya buga mana wasa biyu a jere ba.''

Jesus ya kuma ce tun farko ya tsara saka Ronaldo a karawar daga baya yaga cewar ba sai ya shiga fafatawar ba.

Ronaldo
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Portugal ta fara wasan na Nations League da Gonçalo Ramos a matsayin ɗan wasan gaba, tare da João Félix. Ramos ya ci ƙwallo kuma ya kasance cikin ƴan ƙwallon da suka taimaka Portugal ta samu nasara a karawar.

Jesus ya ce har ya yi magana da Ronaldo cewa zai saka shi a wasa kusan mintuna 30 da suka rage a tashi daga karawar, amma yadda wasan ke tafiya kamar yadda ya tsara, sai yaga bai ga dalilin cire Ramos ba, domin yana kokari a lokacin.

Jorge Jesus ya riga ya bayyana cewa saka ƴan wasa a karawa zai dogara da abin da suke yi ko rawar da suke takawa a fili, kuma ba zai ɗauki matsayi ko sunan ɗan ƙwallo a matsayin tabbacin fara wasa da shi ba. Duk da haka, ya zaɓi Ronaldo cikin tawagarsa, bayan an naɗa shi kocin Portugal.

Saboda haka, abin da ya faru da Norway ya fi kama da sarrafa lokacin wasa da dabarar koci, ba sanarwar cewa Ronaldo ya daina zama muhimmin ɗan wasa ba.

Sau nawa Ronaldo ya fara wa Portugal wasa?

Ronaldo ya buga wa babbar tawagar Portugal wasa 234, abin da ya sa yake riƙe da tarihin wanda ya fi kowa buga wa ƙasa wasanni a tarihin ƙwallon ƙafarta.

Daga cikin waɗannan wasannin, bayanan National Football Teams sun nuna cewa Ronaldo ya fara wasa 215, yayin da ya shiga daga benci sau 16.

Wannan yana nuna irin yadda Ronaldo ya kasance ɗan wasan Portugal da yake kan gaba a yawan buga mata wasanni duk da yawan shekarunsa.

A shekarar 2026 ma, kafin wasan Norway, Opta ta nuna cewa ya fara dukkan wasa takwas da ya buga wa Portugal a shekarar. Ya ci ƙwallaye uku a wannan shekarar zuwa lokacin da bayanan suka ƙare.

Sau nawa Portugal ta ajiye Ronaldo a benci?

Ronaldo

A tsawon tarihin bugawa ƙasarsa wasa, Cristiano Ronaldo ya zauna a benci ba tare da ya shiga wasa ba sau uku.

Wannan yanayi ba kasafai yake faru da shi ba, domin kusan duk lokacin da aka saka shi a benci, ana gabatar da shi a canji ɗan wasa.

Ga bayani kan lokutan da Ronaldo ya zauna a benci bai buga wa Portugal wasa ba:

Wasa da Switzerland a cikin watan Yuni 2008: A gasar Euro 2008, Portugal ta riga ta tsallake zuwa zagaye na gaba, don haka kocin ƙasar na wancan lokacin ya hutar da manyan ƴan wasansa, inda Ronaldo ya kalli duka wasan daga benci.

Wasa da Croatia a cikin watan Yuni 2024: Kafin fara gasar Euro 2024, an ajiye Ronaldo a benci a wasan sada zumunta da Croatia kuma bai shiga karawar ba.

Wasa da Norway a cikin watan Satumba 2026: Sabon lamarin da ya faru kwanan nan a gasar UEFA Nations League, inda kocin Portugal, Jorge Jesus, ya bar Ronaldo a benci na tsawon minti 90 ba tare da ya ska shi a wasa ba.

Wannan shi ne karon farko cikin shekara 18 da abin ya faru da shi a babban wasan gasar na hukumance.

Haka kuma ranar 8 ga watan Satumba 2024 Ronaldo ya kasance a benci a wasan da Portugal ta buga da Scotland, amma ya shiga daga baya kuma ya ci ƙwallo a minti na 88. kenan a akwai wasu wasan da ya fara daga benci.

Ƙwallaye nawa Ronaldo ya ci wa Portugal?

Cristiano Ronaldo ya ci wa Portugal ƙwallaye 146 a wasa 234.

Wannan shi ne babban tarihin yawan cin ƙwallaye a tawaga a duniya a fannin taka leda.

UEFA ta tabbatar da cewa Ronaldo yana da ƙwallo 146 a raga a wasa 234, yayin da Lionel Messi yake na biyu wanda ya ci 125 a wasa 207.

A shekarar 2026 kaɗai, Ronaldo ya ci wa Portugal ƙwallo uku kafin ya halarci gasar Nations League.

Abin da ya faru a Oslo ya zo ne a wani sabon zamani ga Portugal.

Jorge Jesus shi ne sabon kocin tawagar, kuma yana ƙoƙarin haɗa ƙwarewar Ronaldo da matasan tawagar kamar Gonçalo Ramos da João Félix.

A wasan Norway, Portugal ta samu nasara ba tare da Ronaldo ya buga mata wasan ba. Ramos ya fara wasan a gurbin Ronaldo, kuma ya ci ƙwallon da ta ba Portugal damar lashe wasan da cin 2-1.

Amma hakan ba ya gogewa abin da Ronaldo ya yi wa Portugal ba.

Tuni Ronalo ya buga wa Portugal karawa 234 da cin ƙwallo 146 — shi ne kan gaba a duniya a yawan cin ƙwallaye a tawaga, kenan kasar za ta dade tana tuna rawar da ɗan wasa ya taka mata, illa dai ana ta sa ran yaushe ne zai yi ritaya.