BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
An murƙushe yunƙurin sojoji na yin bore a Nijar - Gwamnati
A cikin wata sanarwa, Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce da misalin ƙarfe 12:20 na dare wasu sojoji sun kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.
KAI TSAYE, Za mu kai hari kan dukkan wuraren Amurka idan yaƙi ya ci gaba - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 29 ga watan Agustan 2026.
Hanyoyi 6 da ƴanbindiga ke kashe kuɗaɗen da suke karɓa
Wani rahoto ya yi ƙiyasin cewa masu garkuwa da mutane sun karɓi kimanin dala miliyan 5.8 a matsayin kuɗin fansa tsakanin watan Yulin 2025 da Yulin 2026.
Arsenal na sa ido kan Rashford, Alvarez ba ya son komawa Man City
Arsenal na sa ido kan Marcus Rashford, Chelsea ma na sa ido kan ɗanwasan Monaco Lamine Camara yayin da Valencia ke farautar ɗanwasan tsakiya na Liverpool Harvey Elliott.
Me ya sa yaƙin Iran ya zama matsala ga Trump a zaɓe?
Nasarar yaƙin tattalin arzikin Amurka da Iran ta dogara ne kan ainihin haɗin gwiwar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, China, India, Turkiyya da sauran ƙasashen da ke hulɗa da Iran.
Barazana 5 da duniya ke fuskanta a 2026 da yadda hakan zai shafi Afirka
Rashin tabbas na ƙara yin ƙamari a tsakiyar yanayin duniya, a cewar rahoton da ke bayani kan barazanar da duniya ke fuskanta na 2026 na taron ƙolin tattalin arziƙi na duniya wanda aka wallafa a ranar 14 ga Janairu, 2026.
Matsalar tsaro: Buƙatu biyu da ƴanmajalisar Najeriya suka miƙa wa Tinubu
'Ziyartar Tinubu zuwa jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar tsaro zai taimaka wajen magance matsalar'
Dawo da Nijar cikin Ecowas da amfani da dakarun ECOMOG: Abubuwan da Atiku ya faɗa wa BBC
A wata tattaunawa da BBC, Atiku ya ce matakin da Najeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka suka ɗauka kan Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkin Faso bayan faruwar juyin mulki a ƙasashen bai dace ba.
Illar da Iran ta yi wa harkokin leƙen asirin Amurka da ba a sani ba - NBC
A ranar farko ta wata na shida na yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran, jaridar Wall Street Journal ta ba da rahoton cewa jami'an leƙen asiri da na soja da dama sun yi gargaɗi ga Shugaban Amurka Donald Trump kafin fara yaƙin, amma ya yi watsi da su.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 29 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 29 Agusta 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 29 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Ra’ayi Riga, 19:29, 28 Agusta 2026, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Wasanni
Waɗanne ƴanƙwallo ƙungiyoyinku ke buƙata kafin rufe kasuwar ƴanwasa?
Arsenal har yanzu tana kasuwa tana neman ɗan gaba, kuma ta daɗe tana nuna sha'awar Julian Alvarez.
KAI TSAYE, Baleba da Diallo ba za su buga mana wasa ba - Carrick
Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta
Arsenal ta ci gaba da neman Alvarez, Enzo Fernandez zai koma Man City
Arsenal ta ci gaba da zawarcin Julian Alvarez, Manchester City na neman Iliman Ndiaye na Everton yayin da Aston Villa ta tuntuɓi Rafael Leao.
Arsenal da Madrid, Man Utd da Munich PSG da Villa duk a Champions Lig
Za a fara wasannin rukunin matakin farko ne a ranar 8 ga Satumba, yayin da zagayen karshe zai gudana ranar 27 ga Janairu, 2027.
Ko Bukayo Saka ya dawo kan ganiyarsa?
Ƙoƙarin Bukayo Saka a wasan farko na wannan kakar, wanda Arsenal ta samu gagarumar nasara, wanda ya sa wasu magoya bayan kungiyar suka fara yarda cewa Gunners za ta iya kare kambunta na Premier League.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
'In ka gudu su harbe ka, in ka tsaya su sace ka': Munin garkuwa da mutane a Najeriya
BBC ta tattauna da ɗaya daga waɗanda harin ƴanbindiga ya ritsa da su, wadda ta ce maharan sun kashe mutane da dama.
Amurka ta wallafa sunayen ƴan Najeriya 10 da za ta kora saboda aikata laifuka
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya a sauran sassan duniya, Juma'a 28/08/2026
Abinci 12 da ke inganta lafiyar ƙwaƙwalwa da tunani
A wannan rahoton za mu kawo muku wasu kalar abinci da sha 12 da ake ganin suna taka muhimmiyar rawa wajen kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da tunani da kuma inganta ta.
Tinubu da gwamnoni sun kafa kwamitin lalubo hanyoyin rage tsadar sufuri
Tinubu ya ce sun ɗauki matakin rage kuɗin sufuri a jihohinsu, musamman ta hanyar amfani da motocin CNG da na lantarki, saboda "idan man fetur ya yi arha, kuɗin sufuri ma ya kamata ya ragu".
Yadda ƴanbindiga suka karɓi fiye da naira biliyan 7 kuɗin fansa a Najeriya
Wani sabon rahoto da ƙungiyar SBM Intelligence na nazari kan al'amuran tsaro a duniya ta fitar ya yi ƙiyasin cewa masu garkuwa da mutane sun karɓi kimanin dala miliyan 5.8 a matsayin kuɗin fansa tsakanin watan Yulin 2025 da Yulin 2026.
Wane ne Khalid Mohammed, mutumin da 'ya tsara' hari mafi muni kan Amurka?
Mutumin da ake zargi da kitsa harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 a Amurka, Khalid Sheikh Mohammed zai gurfana a gaban ƙuliya a watan Yunin 2028.
Harsuna 10 da Hausa ke barazanar shafe su a arewacin Najeriya
Wannan ya sanya Hausa ta zama harshe mafi rinjaye da mutane daga ƙabilu daban-daban ke amfani da shi wajen mu'amala da juna wanda hakan ya sa wasu ƙanana harsunan asali da dama ke fuskantar barazanar ɓacewa daga harshen Hausa.
Shin Isra'ila za ta iya samun galaba kan Turkiyya idan za su gwabza yaƙi?
Turkiyya ita ce ƙasa ta farko mai rinjayen Musulmi da ta amince da Isra'ila a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Amma kusan shekara tamanin bayan haka, al'amura sun sauya sosai.
Su wane ne Hausawa kuma daga ina suka samo asali?
Hausawa mutane ne da suka yaɗu a wurare da dama na duniya, kuma suna daga cikin al'umma mafiya yawa a nahiyar Afirka.
Sabbin dabarun da ƴanbindiga ke amfani da su don tara kuɗi a Najeriya
NFIU ta yi zargin cewa masu tara wa ƙungiyoyin kuɗi da ke zaune a ƙasashen waje na amfani da shafukan sada zumunta wajen neman wa ƙungiyoyin tallafi ta hanyar fakewa da ayyukan jin ƙai da tallafin ilimi, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Wane ne Ibrahim Masari, kuma mene ne tasirinsa a jam'iyyar APC?
Wasu na kiransa da "ɗan gaban goshi" a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. Shi ne babban mashawarcin na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin siyasa.
Ba za a iya cimma yarjejeniyar diflomasiyya da Iran ba - Netanyahu
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 26 ga watan Agustan 2026.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































