BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Iran ta yi iƙirarin nasara yayin da tace saura ƙiris a cimma matsaya da Amurka
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2026.
Abin da dokar kafa ƴansandan jihohi a Najeriya ta ƙunsa
Shugaba Tinubu ne ya buƙaci majalisun tarayyar Najeriya su yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 kwaskwarima domin kafa ƴansandan jihohi, amma gwamnoni ne za su riƙa naɗa kwamishinan ƴansandan a jihohinsu.
Real Madrid ta kusan kammala cinikin Silva, Bayern Munich na son Rashford
Ana sa ran Real Madrid za ta kammala cinikin sayan dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31,bayan wa'adin kwantaraginsa ya zo karshe a Manchester City a karshen watan da mu ke ciki.
Yadda ƴan fashin daji suka halaka mutane 18 a jihar Zamfara
Jama'a a garin Goro-Namaye da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, na ci gaba da alhinin mutuwar wasu mutane goma shatakwas da 'yan fashin daji suka halaka yayin wani mummunan farmaki da suka kai a ranar Juma'a da safe.
Ƴan uwa da za su buga kofin duniya a ƙasa daban-daban
Gasar kofin duniya ta bana ja ta ja hankali, musamman da wasu iyalai za su fuskanci juna a wasannin da za a buga sama da 100 tsakanin tawaga 48 a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Me zai faru idan aka ba AI damar gudanar harkokin duniya?
Gwaje-gwaje sun nuna yadda fasahar AI ke nuna halin rashin tabbas idan aka bar su ba tare da sanya musu ido ba.
Su wane ne kwamandojin ISWAP biyu da suka miƙa wuya ga sojin Najeriya?
Rundunar sojin ta ƙara da cewa miƙa wuyan da suka yi na ƙara tabbatar da nasarar da take samu na yaƙi da ƴan ta'adda a yankin tafkin Chadi.
Wane ne Mahdi, yaushe zai bayyana kuma a ina?
Kusan ilahirin al'ummar Musulmin duniya sun yi imani cewa a ƙarshen zamani za a yi wani mutum bawan Allah mai suna Mahdi wanda zai yaƙi zalunci sannan ya tabbatar da adalci.
Kacici-kacici: Ku gwada basirarku a kan rigunan da ƴan wasan tawagar ƙasashe za su saka a gasar Kofin Duniya
Ku gwada basirarku a wannan gasar kacici-kacicin game da Kofin Duniya.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 13 Yuni 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 13 Yuni 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 13 Yuni 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Ra’ayi Riga, 19:29, 12 Yuni 2026, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Wasanni
KAI TSAYE, Gasar kofin duniya 2026: Amurka ta ragargaji Paraguay a wasan farko
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan gasar kofin duniya 2026 da aka fara ranar Juma'a a birnin Mexico
United na son Hall, Madrid na harin Gvardiol
Manchester United na kan bakanta na son ɗauko dan wasan Newcastle Lewis Hall, yayin da Barcelona na harin Bernardo Silva, sai Real Madrid da ke zawarcin ɗan wasan Manchester City Josko Gvardiol
Ƴan asalin Najeriya 14 da za su buga kofin duniya a 2026
Tawagar Najeriya ba ta samu damar shiga gasar cin kofin duniya na 2026 da za a fara daga 11 ga watan Yuni ba. To sai dai tana da ƴan asalin kasar da za su wakilce ta a wasannin.
Yaushe wata kasar Afirka za ta ci Kofin Duniya?
Moroko ta zama ta farko a Afirka da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya a Qatar 2022, amma ko yaushe wata tawaga daga nahiyar za ta iya lashe wannan kofin?
Gasar kofin duniya 2026: Shin wa zai lashe kofin bana?
Wannan shafi ne da zai kawo muku wasu abubuwan da ya kamata ku sani kan gasar cin kofin duniya da za a fara daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli a Amurka da Canada da kuma Mexico
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Me ya sa Najeriya ke martaba ranar 12 ga watan Yuni?
Zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, shi ne na farko a Najeriya bayan juyin mulki na 1983.
'An cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka'
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai tsaye dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 12/06/2026
Yadda hare haren ƴan bindiga ke neman hana noma a wasu yankunan Zamfara
Matsalar tsaro matsala ta hana jama'ar garuruwa fiye da goma na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara sakat
Abu huɗu da za su iya hana ɗorewar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka
Sake farfaɗowar yaƙin ya zo ne kwanaki bayan Iran ta kai hari da makamai mai linzami kan Isra'ila a ranar Lahadi.
Trump ya dakatar da hare-haren da ya shirya kai wa Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 11 ga watan Yuni, 2026.
Yadda cutar kwalara ta yi ɓarna a jihar Borno
Ƙungiyar Likitoci ta MSF ta ce adadin majinyatan da ke buƙatar kulawar gaggawa na ƙaruwa tun bayan da aka samu rahoton ɓullar cutar ta farko a ranar 1 ga watan Mayu.
Yadda aka yi jigilar Uranium a asirce daga Venezuela zuwa Amurka
Aikin dai wani ɓangare ne na yunƙurin da ƙasashen duniya ke yi na rage yawan sinadarin HEU da za a iya amfani da shi wajen ƙera makaman nukiliya.
Yadda magoya baya ke shan wahalar samun bizar zuwa kallon gasar Kofin Duniya
Magoya bayan ƙasashen da za su buga gasar Kofin Duniya sun ce hana su bizar Amurka da ƙa'idojin da aka gindaya, suna jin kamar an ware su daga gasar ne.
Gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun lashi takobin kawar da talauci da matsalar tsaro
Gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun yunkura domin kawar da talauci da matsalar tsaro a jihohinsu
Fitattun ƴan Najeriya da aka daɗe ana damawa da su a siyasar ƙasar
Mun waiwayi tarihi domin zaƙulo wasu ƴansiyasa da suka fi daɗewa a fagen siyasar ƙasar.
Da gaske ne mata sun fi maza tausayi?
Har yanzu muna da tunanin cewa asali a wuri halitta mata sun fi maza tausayi tausayi, haka nan kuma ana kallon maza a matsayin masu son babakere da nuna iko.
Nawa ne dukiyar Elon Musk kuma me zai iya saya da ita?
Adadin na da tarin yawa ta yadda mutane da dama ba za su iya ƙimanta yawan kuɗin ba sai dai a yi ta hasashe.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































