Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 19/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab

Rahoto kai-tsaye

Daga Isiyaku Muhammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Mun fitar da ganga biliyan ɗaya na ɗanyen mai ta mashigin Hormuz - Amurka

    CENTCOM

    Asalin hoton, EPA

    Kwamandan Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM, Brad Cooper, ya ce sojojin Amurka sun taimaka wajen fitar da sama da ganga biliyan ɗaya na ɗanyen mai ta mashigin Hormuz cikin watanni biyu da suka gabata.

    A wani bidiyo da aka wallafa a shafin X na Rundunar Sojin Amurka, Mista Cooper ya ce an samu wannan nasarar ne sakamakon haɗin gwiwa da yi wa sama da jirage 2,000 rakiya.

    A cewarsa, an cire nakiyoyi daga mashigin Hormuz, kuma dubban jiragen ruwa sun ratsa ta wannan hanyar ruwan.

    Kwamandan CENTCOM ya ce ƙasashen da Amurka ke hulɗa da su a yankin sun ci gaba da fitar da man fetur, yayin da Iran ba ta iya fitar da ko ganga ɗaya ta man fetur ɗinta ta mashigin ba.

    Ya ce da haɗin gwiwar Amurka da ƙasashen Larabawa shida da ke gaar Tekun Farisa, kamfanonin safarar jiragen ruwa da hukumomin inshorar ruwa, za a ci gaba da jigilar mai ta mashigin Hormuz.

    Mista Cooper ya ce yawan man fetur, iskar gas da sauran kayayyakin da suka ratsa mashigin Hormuz cikin makonni biyu da suka gabata ya kai matakin da bai taɓa kaiwa ba cikin watanni shida.

  2. Jam'iyyar PRP ta buƙaci a yi gaggawar hukunta masu hannu a mutuwar mutum 37 a Neja

    Jam'iyyar adawa ta PRP a Najeriya ta buƙaci gwamnati ta gaggauta gudanar da bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a mutuwar mutane 37 da suka rasu yayin da suke hannun hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC a Minna, jihar Neja.

    A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar, Comrade Muhammed Ishaq, ya fitar, PRP ta ce ta yi kaɗuwa kan lamarin tare da neman kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki musabbabin mutuwar mutanen.

    Jam'iyyar ta ce duk wanda binciken ya gano yana da hannu a lamarin ya kamata a gurfanar da shi gaban shari'a.

    Ta ce abin da ya faru na ƙara nuna, a ra'ayinta, cewa gwamnati ba ta sauke nauyin kare rayuka da dukiyoyin 'yan ƙasa yadda ya kamata ba.

    Tuni dai gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamitin mutum 10 mai zaman kansa mako biyu domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da miƙa rahotonsa ga Ma'aikatar Cikin Gida.

    An kuma sanar da dakatar da jami'ai 20 na hukumar NSCDC bisa abin da ya faru a ranar Alhamis.

  3. Gwamnati ta ce ba ta da ikon ƙayyade farashin man fetur a Najeriya

    Gwamnati ta ce ba ta da ikon ƙayyade farashin man fetur a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar da ke kula da haƙo albarkatun man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta ce ba ta da ikon ƙayyade farashin man fetur a gidajen mai.

    A wata sanarwa da hukuma ta fitar, ta ce bisa tanadin dokar man fetur ta 2021 (PIA) ba za ta iya tsara farashin man fetur ko sanya farashin dole ga ƴan kasuwa ba, kamar yadda sashe na 205(1) na dokar ya tanada.

    Ta ce abin da gwamnati take iya yi kawai shi ne shiga tsakani a wasu lokuta na musamman ko wata matsala a kasuwar man.

    NMDPRA ta ce a halin yanzu babu wasu dalilai da suka bayyana da za ta ba gwamnati damar shiga tsakani wajen ƙayyade farashi.

    Hukumar ta kuma ce tana haɗin gwiwa da Hukumar Kwastam ta Najeriya da sauran hukumomin tsaro wajen sa ido kan iyakokin ƙasar, domin dakile fasa ƙaurin man fetur zuwa ƙasashen waje ba bisa ƙa'ida ba.

    Ta ƙara da cewa tana kuma aiki tare da Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye (FCCPC) wajen sa ido kan duk wani farashi da bai dace ba.

  4. NAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun Hajjin 2027

    NAHCON

    Asalin hoton, NAHCON/FB

    Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta musanta zargin cewa an karkatar da kujerun Hajjin 2027, inda ta ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa an karya dokokin Saudiyya ko ƙa'idojin hukumar wajen rabon kujerun.

    Wannan na zuwa ne bayan wata takardar ƙorafi da wasu masu gudanar da aikin Hajji masu zaman kansu suka yi, inda suka buƙaci a binciki zargin karkatar da kujerun Hajji 5,000.

    A wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai NAHCON Shafii Sani Mohammed, ya fitar ta ce Najeriya ta samu kujerun Hajji 50,000 na shekarar 2027, inda aka ware 35,000 ga jihohi da Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da aka ware 15,000 ga kamfanonin Hajji masu zaman kansu.

    Hukumar ta ce an raba kujerun kamfanoni masu zaman kansu ne ga masu gudanar da aikin Hajji da ke ƙarƙashin manyan kamfanoni bakwai da aka amince da su, bisa ƙa'idojin Najeriya da na Saudiyya.

    NAHCON ta kuma ce wasu daga cikin masu gudanar da aikin Hajjin na fuskantar ƙalubale wajen cika ƙa'dojin da Saudiyya ta gindaya na Nusuk-Masar, wanda wa'adin shigar da bayanan mahajjata zai ƙare a ranar 26 ga Satumba 2026.

    Ta ce ba ta da ikon tsawaita wannan wa'adin da gwamnatin Saudiyya ta gindaya.

    Hukumar ta buƙaci mahajjatan da suka yi rajista ta hannun kamfanoni masu zaman kansu su tabbatar da cewa an kammala shigar da bayanan rajistarsu da na yatsunsu cikin tsarin Nusuk kafin wa'adin.

    NAHCON ta ce za ta ɗauki matakin ladabtarwa, ciki har da dakatar da lasisi ko soke shi, kan kamfanonin da suka kasa sauke nauyin da ke kansu cikin wa'adin da aka kayyade.

    Hukumar ta ce iƙirarin karkatar da kujerun za su ci gaba da kasancewa zarge-zarge ne matuƙar ba a gabatar da hujjar da ke nuna an karya wata doka ko ƙa'ida ba.

  5. An kashe mutum 48 a sabon rikici a kudancin Yemen

    Aƙalla mutane 48 ne aka kashe a sabon rikicin da ya barke tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da Saudiyya ke mara wa baya da kuma 'yan Houthi da Iran ke goyon baya a kudancin ƙasar.

    Majiyoyin soji daga ɓangarorin biyu sun tabbatar wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa an kashe mutane 17 daga cikin dakarun gwamnati.

    A nasu ɓangaren kuma, 'yan Houthi sun ce an kashe mutum 31 daga cikin dakarunsu cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

  6. Muna son gudanar da zaɓen majalisa da na shugaban ƙasa a tare - Iran

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar Cikin Gida ta Iran ta sanar da cewa tana kokarin gudanar da zaɓen majalisar dokoki da na shugaban ƙasa a lokaci guda.

    Mai magana da yawun ma’aikatar, Ali Zeinivand, ya ce an kafa wani kwamitin aiki domin haɗa zaɓukan biyu, wanda ya ƙunshi Ma’aikatar Cikin Gida, Cibiyar Bincike ta Majalisar Dokoki, Majalisar Kula da Kundin Tsarin Mulki da Majalisar Tantance Manufofin Tsarin Mulki.

    Ya ce kwamitin ya yi nazari kuma ya gano cewa za a iya haɗa zaɓukan biyu ba tare da sauya kundin tsarin mulkin ƙasar ba.

    Mista Zeinivand ya ce: “Babu wanda ke adawa da wannan batu. Muna kan hanyar kammala wannan tsari, domin bayan samun ƙarin ra’ayoyi daga majalisu daban-daban, mu gabatar da shi ga majalisa a matsayin ƙudirin doka.”

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida ta Iran ya bayyana fatan cewa za a gudanar da zaɓen majalisa da na shugaban ƙasa a lokaci guda a watan Ordibehesht na shekara ta 1407, wanda ya yi daidai da watan Mayun 2028.

    A karkashin dokokin Iran na yanzu, an shirya gudanar da zaɓen majalisa na gaba a Esfand 1406, wato Maris 2028, yayin da zaɓen shugaban ƙasa aka shirya gudanar da shi a Khordad 1407, wato Yuni 2028.

    An dage zaɓen ƙananan hukumomi, wanda aka shirya gudanarwa a wannan bazarar, saboda halin da ake ciki na yaƙi.

    Jami’an Iran sun ce za a gudanar da zaɓukan ne watanni biyu bayan kawo ƙarshen yaƙin.

  7. Amurka da Denmark sun shiga yarjejeniyar tsaron Greenlan - Trump

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka da Denmark, da Greenland sun cimma yarjejeniyar da za ta bai wa Amurka ikon kula da harkokin tsaro a yankin Greenland har abada.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Trump ya ce yarjejeniyar za ta kuma sanya Amurka ta zama mai kula da duk wasu sauran bukatun yankin na Greenland.

    Wakilin BBC ya ce jami'a a Denmark da Greenland sun yaba da cimma wannan yarjejeniya amma ba su tabbatar da ikirarin Mista Trump na cewa za ta bai wa Amurka cikakken iko da yankin na Greenland ba.

    Firaministan Denmark ta kara da cewa, ana bukatar amincewar majalisa kafin yarjejeniyar ta fara aiki.

  8. An kusa kawo ƙarshen yaƙin Iran sannan farashin mai ya sauka - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sake nanata cewa za a kawo ƙarshen yaƙin da Iran nan ba da jimawa ba, tare da hasashen cewa farashin man fetur zai ragu bayan kawo ƙarshen rikicin.

    “Mutane ba sa son Iran ta mallaki makamin nukiliya, kuma kun san abin da suke so... Za a kawo ƙarshen wannan yaƙin nan ba da jimawa ba, kuma idan ya ƙare, farashin man fetur zai koma inda yake a baya, ko ma ya yi ƙasa da haka,” in ji shi yayin wani taro kan harkokin kiwon lafiya da aka gudanar a Fadar White House.

    Da yake magana kan amfani da jiragen yaƙin B-2 wajen kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran, Donald Trump ya ce ya yi imanin cewa matakin soji ya zama dole domin hana Tehran mallakar makaman nukiliya.

    “Ba ni da wani zaɓi,” in ji shi. “Na gaya wa tawaga ta cewa dole ne in ɗauki mataki kan Iran, domin da ba mu kai musu hari da jiragen B-2 ba, da sun mallaki makaman nukiliya.”

    A kwanakin baya ma ya yi irin wannan hasashen game da yaƙin da kuma farashin makamashi, inda a ranar Laraba ya ce da zarar rikicin ya ƙare, farashin man fetur zai ragu cikin sauri.

  9. Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wanda take zargi da yi wa Isra'ila leƙen asiri

    Mizan

    Asalin hoton, Mizan

    Hukumar shari’a ta Iran ta sanar da cewa ta zartar da hukuncin kisa kan wani ɗan ƙasar da aka yanke wa hukuncin kisa bayan an gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin yi wa Isra’ila leƙen asiri.

    Kamfanin dillancin labarai na Mizan, mai alaƙa da hukumar shari’a, ya ruwaito cewa mutumin mai suna Hossein Pedran ya bai wa hukumar leƙen asirin Isra’ila, Mossad, bayanai kan muhimman wuraren soji da ke lardin Isfahan.

    Mizan ta ce: “Dangane da kayan aiki da aka gano a wajen Hossein Pedran da kuma ikirarin da ya yi, an gurfanar da shi bisa tuhume-tuhumen leƙen asiri da haɗin gwiwar bayanan sirri domin amfanin gwamnatin Sahayoniya, da kuma fara haɗin gwiwar bayanan sirri da gwamnatin Amurka da Iran ke kallon maƙiyi, ta hanyar gabatar da buƙatar haɗin gwiwa da bayyana niyyarsa ta yi wa hukumar leƙen asirin Amurka aiki, tare da wasu ƙarin tuhume-tuhume.”

    A cewar rahoton Mizan, an aiwatar da hukuncin kisan Hossein Pedran ne bayan Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin.

    Rahoton hukumar shari’ar bai bayyana ainihin lokacin da aka kama shi ba, ko inda aka yi shari’ar, ko kuma cikakkun bayanan da aka gabatar a kotu.

  10. Abin da ya sa muke goyon bayan Tinubu ya zarce - Rarara

    Mawaƙin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya ce shi da sauran ƴan Kanywood na goyon bayan Shugaba Tinubu saboda "ba ya ƙarya da yaudara".

    Rarara ya kuma nemi ƴan ƙasar su yi haƙuri da yanayin da ake ciki.

    Bayanan bidiyo, Abin da ya sa muke goyon bayan Tinubu ya zarce - Rarara
  11. Zelensky ya yaba wa Trump bisa amincewa da takunkumi kan Iran da Rasha

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    A baya mun ruwaito cewa Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta kakaba tsauraran takunkumi kan Rasha tare da tsawaita takunkuman da aka kakaba wa Iran.

    Yanzu Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya gode wa shugaban Amurka kan rattaba hannu kan dokar.

    Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ne ya taimaka wajen rubuta dokar, wanda ya rasu a farkon wannan bazarar. Kafin rasuwarsa, Mista Graham ya kai ziyara Ukraine.

    Mista Zelensky ya rubuta a shafin sada zumunta na X cewa: “Hanya mafi kyau ta girmama ƙwaƙwalwar Lindsay ita ce a aiwatar da tanade-tanaden wannan doka gaba ɗaya kuma cikin gaggawa.”

  12. Waɗanda suka mutu a harin Masallaci a Pakistan sun haura 30

    Pakistan

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin mutanen da suka mutu a harin bam da aka kai da mota a wata masallaci a arewa maso yammacin Pakistan ranar Juma’a ya haura 30, kamar yadda rahotanni suka nuna.

    Jami’ai sun ce an tayar da wata mota da aka cika da abubuwan fashewa a gaban masallacin da ke gundumar Kohat a lardin Khyber Pakhtunkhwa, kafin wasu ‘yan bindiga su kutsa cikin wani sansanin ‘yan sanda da ke makwabtaka da masallacin.

    Fiye da mutum 100 sun jikkata.

    Jami’an tsaro sun ce yanzu an kammala share gine-ginen bayan wani samame da suka kwashe dare suna gudanarwa.

    Pakistan ta fuskanci karuwar hare-haren ta’addanci sosai tun bayan da Taliban ta sake dawo da iko a Afghanistan da ke makwabtaka da kasar.

  13. Amurka ta sake lafta wa Rasha takunkumi

    Amurka da Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Trump ya rattaba hannu kan kudirin dokar ƙaƙaba sabbin takunkumai masu tsauri kan Rasha, bayan da Majalisar Wakilai ta amince da kudurin da gagarumin rinjaye a ranar Laraba.

    Wakilin BBC ya ce magoya baya dai sun ce makasudin dokar shi ne dakile kudaden shiga da Rasha ke samu daga man fetur da iskar Gas da ta ke amfani da su wurin gudanar da yakinta kan Ukraine.

    Dokar za ta bai wa Shugaban Trump damar sanya harajin kasuwanci mai nauyi, idan ya ga dama, kan manyan kasashe masu sayen man fetur da iskar gas daga Moscow, kamar su China da Indiya.

  14. Trump ya hana CNN shiga fadar White House domin ɗauko labarai

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya ce zai hana wasu manyan kafofin yada labarai na Amurka guda uku shiga Fadar White House nan take.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya zargi CNN da MS Now da Politico da ci gaba da yada "labaran karya," inda ya ce wannan matakin hana shiga martani ne kan hakan.

    Wakiliyar BBC ta ce A baya shugaba Trump Ya dauki matakin shari'a kan wasu kafofin yada labarai da suka hada da New York Times da BBC, kuma akai-akai yana samun sabani tare da cin mutuncin yan jarida.

    A cikin wata sanarwa, CNN ta bayyana matakin a matsayin cin zarafi da ya saba wa doka, tare da take hakkinsu na gudanar da aiki ba tare da cikas ko tsangwama daga gwamnati ba.

  15. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da kuma yin muhawara.

    Ku kasance tare da mu.