Me ake tattaunawa a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya?

Taron MDD

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da shugabannin ƙasashe daga sassa daban-daban na duniya suka hallara a birnin New York na Amurka, hankulan jama'a sun koma kan taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na shekara-shekara, wanda aka fi sani da UNGA karo na 81.

Taron na kasancewa ɗaya daga cikin manyan tarukan diflomasiyya a duniya, inda shugabanni ke tattauna batutuwan da suka shafi makomar duniya.

Ana gudanar da taron ne a kowace shekara tare da halartar wakilan ƙasashe mambobi 193 na Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda ke ba da ra'ayoyinsu kan manyan ƙalubalen da duniya ke fuskanta.

Daga ciki akwai yaƙe-yaƙe da rikice-rikice da matsalolin tattalin arziki da kuma batun sauyin yanayi.

A bana, taron na zuwa ne a lokacin da rikice-rikice ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na duniya, ciki har da yaƙin Iran da na Ukraine da sauransu.

Ana kuma sa ran shugabanni za su tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa wajen magance waɗannan matsaloli.

Mene ne taron UNGA?

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

UNGA na nufin United Nations General Assembly, wato Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

Taron ne babbar kafa ta tattaunawar Majalisar Dinkin Duniya, inda dukkan ƙasashe mambobi 193 ke da wakilci kuma kowace ƙasa na da ƙuri'a guda ɗaya.

Ana gudanar da taron ne a hedkwatar United Nations da ke birnin New York na Amurka.

UNGA shi ne babban taron shekara-shekara na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda shugabannin ƙasashen duniya ke hallara domin tattauna muhimman batutuwa kamar yaƙe-yaƙe, sauyin yanayi, tattalin arziki, lafiya, fasahar AI da kuma makomar haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa

An samar da babban zauren ƙarƙashin Sashe na Huɗu na Kundin Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda aka sanya wa hannu a birnin San Francisco a ranar 26 ga watan Yunin shekara ta 1945.

Kundin ya fayyace muhimman ayyukan zauren, waɗanda suka haɗa da bunƙasa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa a fannonin tattalin arziki da zamantakewa da al'adu da ilimi da lafiya tare da taimakawa wajen tabbatar da haƙƙin ɗan Adam.

Babban Zauren na gudanar da zamansa daga watan Satumba zuwa Disamba a kowace shekara, sannan idan buƙata ta taso, ya sake zama daga watan Janairu zuwa Agusta.

Me ake tattaunawa a taron?

Ana yin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a kowace shekara ne domin bai wa ƙasashen duniya damar tattauna manyan batutuwan da suka shafi zaman lafiya, tsaro, ci gaba da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Taron na tattauna manyan batutuwna da suka shafi duniya da suka haɗa da:

Manyan matsalolin duniya

Amina Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da taron UNGA ke mayar da hankali a kai shi ne yadda za a magance matsalolin da ke addabar duniya.

Waɗannan sun haɗa da yaƙe-yaƙe da rikice-rikice da ke haddasa mutuwar jama'a da raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Haka kuma, shugabannin duniya kan tattauna matsalar yunwa da talauci, musamman a ƙasashe masu tasowa, inda miliyoyin mutane ke fuskantar ƙarancin abinci da matsin rayuwa.

Baya ga haka, sauyin yanayi na daga cikin manyan ƙalubalen da ake tattaunawa a taron, saboda yadda yake haddasa fari da ambaliyar ruwa da tsananin zafi da ke shafar rayuwar al'umma da tattalin arzikin ƙasashe.

Ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe

Shettima a taron UNGA

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Najeriya

Haka kuma taron UNGA kan mayar da hankali wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashe da samar da hanyoyin haɗin gwiwa a fannoni kamar tsaro da tattalin arziki da ci kuma gaba.

Haka kuma, taron na bai wa shugabanni damar musayar ra'ayoyi da neman mafita kan matsalolin da ba ƙasa ɗaya kaɗai za ta iya magance su ba.

Ta hanyar wannan haɗin gwiwa, ƙasashe kan yi ƙoƙarin cimma matsaya guda domin samar da zaman lafiya, ci gaba da walwala ga al'ummomin duniya baki ɗaya.

Bibiyar Manufofin Ci Gaba Masu Ɗorewa (SDGs)

Wani muhimmin batu da ake tattaunawa a taron UNGA shi ne yadda ƙasashen duniya ke aiwatar da Manufofin Ci Gaba Masu Ɗorewa (SDGs), waɗanda suka haɗa da rage talauci da inganta ilimi da lafiya, da kuma kare muhalli.

Shugabanni kan yi bitar ci gaban da aka samu tare da tattauna matakan da za su taimaka wajen cimma waɗannan manufofi nan da shekarar 2030.

Zaɓen sabbin shugabannin MDD

MDD

Asalin hoton, Getty Images

Yanke wasu muhimman shawarwari na Majalisar dinkin Duniya, ciki har da amincewa da kasafin kuɗin majalisar da zaɓen wasu mambobin kwamitin tsaro na majalisar da sauran muƙamai.

Wannan taron na bana shi ne ke kasancewa na ƙarshe da babban sakataren Majalisar, Antonio Gutteres zai jagoranta, wanda wa'adinsa ke cika a ƙarshen shekarar nan.

Damar ganawar shugabannin duniya

Wani muhimmin alheri da taron UNGA ke samarwa shi ne bai wa shugabannin ƙasashe damar ganawa da juna domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashensu da kuma duniya baki ɗaya.

A irin waɗannan ganawa, shugabannin kan ƙulla alaƙar diflomasiyya, sasanta saɓani da kuma neman hanyoyin haɗin gwiwa a fannonin tsaro, tattalin arziki da ci gaba.

A taƙaice, manufar taron UNGA ita ce samar da wani babban dandali da dukkan ƙasashen duniya za su yi amfani da shi wajen tattauna ƙalubalen da ake fuskanta, da nemo hanyoyin haɗin gwiwa domin samar da zaman lafiya, ci gaba da walwalar al'umma a duniya.