Abu biyar da za ku iya yi ku taimaka wa ƴanbindiga ba tare da kun sani ba

Ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴanbindiga
    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da ake ci gaba da fama da matsalar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya, wasu mutane na faɗawa tarkon ƴan bindiga, ko ƴan ta'adda da sauran masu aikata laifuka ba tare da sanin hakan ba.

A makon nan ne jami'an hukumar kare fararen hula a jihar Katsina suka kama wani mutum mai harkar cirar kuɗi ta POS, a ƙaramar hukumar Matazu, bisa zargin taimaka wa ƴan bindigar wajen cire musu kuɗi ta na'urarsa.

Ko da yake hukumomin tsaro na cewa wasu mutane kan aikata hakan ne bisa kuskure, sai dai akwai waɗanda ke yi da gan-gan.

A lokuta da dama, hukumomi sun sha kama mutane da makamai a motoci zuwa wasu wurare, ɗauke da makamai ba tare da sun san abin da suke dauke da shi, ko waɗanda za su kai wa ba.

Dangane a wannan batu ne BBC ta tattauna da wani masanin tsaro a Najeriya Dakta Kabiru Adamu, wanda ya fito da wasu abubuwa goma da za ku iya yi na taimaka wa masu ɗauke da makaman ba tare a kun sani ba.

1 - Mu'amalar kuɗi

Masanin harkokin tsaron ya ce samun kuɗi na daga cikin abubuwan da masu aikata laifi ke buƙata domin gudanar da ayyukansu, kuma mutum na iya taimaka musu ta wannan hanya ba tare da ya sani ba.

Ya ce ''Karɓa, ko turawa ko cire kuɗi a madadin wani na iya zama mu'amala ta yau da kullum, amma idan kuɗin na da alaƙa da aikata laifi, hakan na iya jefa mutum cikin matsala.

"Ko da ba ka cikin ƙungiyar masu aikata laifin, idan ka taimaka musu wajen samun kuɗin da suke buƙata ko ka sauƙaƙa musu hanyar samun sa, kana iya ba su damar ci gaba da ayyukansu," in ji shi.

Ya ce akwai ƙa'idojin harkokin kuɗi da ke buƙatar mutum ya san wanda yake mu'amala da shi, musamman idan ana magana ne kan makudan kuɗaɗe ko kuma mu'amalar tana da alamun shakku.

Daga cikin waɗannan ƙa'idoji akwai doka ta musamman da Babban Bankin Najeriya ya samar, mai suna "Know Your Customer" wato (KYC), wadda ke tilasta wa masu harkar kuɗi tantance mutanen da suke mu'amala da su.

"Dole ne ka san wanda za ka ɗauki kuɗi ka ba shi. Idan aka karɓi kuɗi a wurinka, aka je aka aikata wani laifi, doka na iya ɗaukar mataki a kanka. Rashin sani ba dalili ba ne," in ji masanin.

2 - Bayar da bayanan sirri

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Kabiru Adamu ya ce, ko da yake mutane da dama na iya tunanin cewa bayar da bayanan sirri ga 'yan bindiga ko masu ɗauke da makamai, wato irin mutanen nan da ake kira (Infoma) abu ne da ake yi da gangan, akwai lokutan da mutum zai iya yin hakan ba tare da ya sani ba.

Ya ce hakan na iya faruwa a wuraren taruwar jama'a, musamman a majalisa, inda mutane ke zama suna tattaunawa cikin walwala, har su saki jiki su faɗi wasu maganganu da ka iya jefa rayuwar jama'a cikin haɗari.

"Misali, mutum ne zai zo ya zauna yana hira ko yana sana'a, a cikin jama'a sai a ji yana ta yin tambayoyi, kai kuma ba ka san wanda kake magana da shi ba, sai ka fara ba shi bayanai alhali ba ka san manufarsa ba," in ji shi.

Ƙwararren ya ce irin wannan sakin baki, ko hawa dokin baki musamman a wuraren taruwar jama'a da wasu kan shantake su yi ta zuba zance, na iya bai wa masu aikata laifuka bayanan da za su yi amfani da su wajen shiryawa ko aiwatar da hari, ko kuma bibiyar wani mutum ko wani wuri da suke son sani don cimma mummunar manufarsu.

A cewarsa, idan aka gano cewa wani bayani da mutum ya bayar ya taimaka wajen aikata laifi, wannan na iya zamar masa matsala.

3. Sayar musu da ƙwayoyi

Ƙarin wata babbar hanya da mutum zai iya tsintar kansa yana taimaka wa 'yan bindiga ko wasu masu ɗauke da makamai ita ce samar musu da miyagun ƙwayoyi, ko kuma sauƙaƙa musu hanyar samun su, in ji masanin tsaron.

Sanannen abu ne cewa miyagun ƙwayoyi na taka rawa wajen ayyukan masu ɗauke da makamai, musamman wajen ƙeƙasar da zuciyarsu, da cire musu tausayi ko tsoro, su samu ƙarfin gwiwar rufe idonsu wajen cutar da jama'a.

Ya ce ''Akwai magungunan gusar da hankali da dama da suke amfani da su, kuma yawanci sukan tura mutane ne su sayo musu, ko kuma su da kansu su yi ɓadda-bami su je su saya a shagunan sayar da magunguna na ƙyamis-ƙyamis, ba tare da an san su wanene ba.

Ya ce wasu kuma, musamman masu harkar sufuri da kasuwanci, na ɗauko miyagun ƙwayoyi ne daga wani wuri zuwa wani, ba tare da sun san abin da suka ɗauko ba.

A cewarsa, "Wannan na ƙara nuna muhimmancin taka-tsantsan, musamman ga masu safarar kaya, direbobi da 'yan kasuwa, domin kada a yi amfani da su wajen jigilar abubuwan da ka iya taimaka wa masu aikata laifi."

4 - Ba su kayan abinci

A cewar Dakta Kabiru Adamu, kamar sauran mutane, masu ɗauke da makamai ma na buƙatar abinci da sauran kayan masarufi domin rayuwa.

Ya ce wata hanya da suke amfani da ita wajen samun waɗannan abubuwa ita ce ta hanyar tura fararen hula su sayo ko kai musu su, ba tare da mutanen da ke gudanar da harkar sun san ainihin waɗanda za su kai wa kayan ba.

"Wani abu da ka iya ƙara jefa mutane cikin irin wannan harkar shi ne tayin kuɗi mai yawa, inda ake sayen kaya daga hannun jama'a kan farashi da ya fi wanda aka saba biya a kasuwa," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, "Suna iya ba mutum farashi mai tsoka, su ninka kuɗin da ake sayen kaya da shi a kasuwa. Wannan na iya jan hankalin wasu su sayar musu ko su taimaka musu, saboda kawai suna son cin ƙazamar riba, ba tare da sun san ainihin wanda suke taimakawa ba," in ji shi.

5 - Saya ko sayar musu da waya ko layi

Dakta Kabiru Adamu ya ce mutum na iya sayen waya daga kasuwa ko wajen wani ba tare da sanin wanda ya yi amfani da ita a baya ba.

Haka kuma, mutum na iya karɓar layin waya da aka taɓa amfani da shi a baya, walau da sunan sabo ko na wani da ya sani kuma yake mu'amala da shi, ba tare da ya san yadda aka yi amfani da layin a baya ba.

Ya ce irin wannan yanayi na iya jefa mutum cikin binciken jami'an tsaro idan aka gano cewa an taɓa amfani da wayar ko layin wajen gudanar da wani laifi.

"Wataƙila ka sayi waya ko ka karɓi layi ne a matsayin sabo, amma kafin ya shigo hannunka, ba mamaki an taɓa amfani da shi wajen wata harkar da ba ka sani ba."

Yadda za a kauce wa faɗawa matsalar

Masana harkokin tsaro na cewa akwai wasu matakai da jama'a za su iya ɗauka domin kauce wa faɗawa tarkon masu aikata laifi ba tare da sun sani ba.

A cewar Dakta Kabiru Adamu, masanin harkokin tsaro a Najeriya, na farko shi ne yin taka-tsantsan da mutanen da ba a sani ba, musamman idan aka lura suna yin maganganun da suka shafi bayanan sirri, da harkokin tsaro ko wuraren da mutane ke zama.

Haka kuma, ya kamata 'yan kasuwa su kiyaye, su kuma tantance abokan hulɗarsu da kuma adana bayanan mu'amala, musamman na kuɗi.

Ya ce, "Ga masu sufuri da direbobi, yana da muhimmanci su san abin da suke ɗauka da kuma wanda ya ba su kayan, da kuma inda za su kai, domin kada a yi amfani da su wajen jigilar abubuwan da ba su sani ba, waɗanda ka iya jefa su cikin haɗari."

Haka kuma, a cewarsa, ya dace mutum ya yi hattara idan aka yi masa tayin ba shi kuɗin da ya zarce hankali da sunan saye ko biyan shi ladan aikinsa.

Ya ce, "Muhimmin abu shi ne jama'a su fahimci cewa rashin sani ba koyaushe yake zama dalili ba. Saboda haka, taka-tsantsan, da bin ƙa'idojin kasuwanci da kuma kai rahoton abubuwan da ake zargi na iya taimakawa wajen kare mutum daga shiga harkokin masu aikata laifuka ba tare da ya sani ba."