Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugabannin da aka taɓa buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah a Madina
- Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Duk da cewa ɗakin da ƙabarin annabi Muhammad SAW yake ya kasance koyaushe a kulle sannan ba a barin jama'a su shiga, amma wasu shugabannin ƙasashe sun samu damar shiga ɗakin, ɗaya daga cikin wurare mafi daraja a addinin Islama.
Ƙabarin na annabi SAW ya kasance a cikin ɗakin daya daga cikin matansa, Nana Aisha da ke a gaban masallacin Madina mai tsarki.
A cikin ɗakin akwai ƙaburburan Sahabbansa guda biyu, Abu Bakr RA da kuma da Umar RA.
BBC ta samu ƙarin bayani daga hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain kan shugabannin da suka taɓa samun damar shiga ɗakin Ƙabarin Manzon Allah (SAW).
Haramain Sharifain ya ce an buɗe wa shugabanni da dama da sarakunan Saudiyya, kuma ga shugabannin kamar yadda hukumomin na Saudiyya suka rubutowa BBC a 2021:
Shugabannin Pakistan
Paskitan na da alaƙa mai ƙarfi da Saudiyya, kuma shugabanninta da dama sun samu wannan karramawa daga hukumomin Saudiyya da aka taɓa buɗe wa ɗakin da aka binne Annabi (SAW).
Tsohon Firaministan Pakistan Muhammad Nawaz Sharif wanda ya fi dadewa a kan mulki a tarihin ƙasar ya sha kai ziyara ƙabarin Manzon Allah a Madina.
Nawaz Sharif yana cikin shugabannin da hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya suka ce an buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah (SAW).
Nawaz Sharif ya taɓa wallafa hotunansa a shafinsa na Twitter a ziyarar da ya kai Masallacin Manzon Allah a Madina a shekarar 2015 da 2018.
Haramain Sharifain ya ce an taɓa buɗe wa Firaminista Zulfikar Ali Bhutto ɗakin Manzo Allah wanda ya mulki Pakistan daga 1973 zuwa 1977.
Haka ma an buɗe wa Tsohon Firaminista Janar Muhammad Zia-ul-Haq wanda ya mulki Pakistan daga 1978 bayan hamɓarar da gwamnatin Ali Bhutto zuwa 1988 lokacin da ya mutu a hatsarin jirgin sama.
Shugaban Chechnya, Ramzan Kadyrov
Haramain Sharifain ya ce shugaban Jamhuriyyar Chechen Ramzan Kadyrov yana cikin shugabannin da aka taɓa buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah.
Ramzan Kadyrov ya taɓa kai ziyara Masallacin Manzon Allah a Madina a 2018, inda ya samu tarba daga shugabannin Saudiyya.
Kadyrov wanda ya gaji mahaifinsa Akhmad Kadyrov da aka kashe a 2004, ya zama shugaban ƙasar Chechnya ne a 2007 bayan ya kai shekara 30 da haihuwa.
Sarakunan Saudiyya
Haramain Sharifain ya ce sarakunan Saudiyya da dama sun shiga ɗakin da aka binne Manzon Allah.
Hukumomin sun ce Sarki Abdulaziz da Sarki Faisal suna cikin kundin tarihi a rubuce da suka kai ziyara ɗakin da aka binne Manzon Allah.
Amma kuma Haramain Sharifain ya ce akwai sarakunan Saudiyya da suka kai ziyara da ba a rubuta su ba.
Shugaban Iran Sayyid Mohammad Khatami
Haramain Sharifain ya ce tsohon shugaban Iran Sayyid Mohammad Khatami na cikin shugabannin da aka ba damar shiga ɗakin da aka binne Manzon Allah.
Khatami mai sassaucin ra'ayi shi ne shugaban Iran na biyar wanda ya yi mulki daga 1997 zuwa 2005.
Ya yi ƙoƙarin samun goyon baya da haɗin kan ƙasashen larabawa a ziyarar mako ɗaya da ya kai wasu manyan ƙasashen yankin a 1998 ciki har da Saudiyya inda ya gudanar da aikin Umrah zamanin sarki Fahd.
Ziyarar da ya kai Saudiyya ita ce ta farko da wani babban jami'in gwamnatin Iran ya kai tun juyn juya halin ƙasar a 1979.
"Abubuwan da muka gani a ɗakin ƙabarin Manzon Allah"
Wani Shehin malamin Saudiyya Sheikh Aaeed Ben Omar al-Rouis yana cikin waɗanda suka samu damar shiga ɗakin ƙabarin Manzon Allah a Masallacin Madina.
Al-Rouis ya bayar da labarin abubuwan da ya gani a lokacin da ya raka Sarki Faisal bin Abdulaziz da ya yi mulkin Saudiyya tsakanin 1906 zuwa 1975.
A wani bidiyo da aka wallafa a Youtube, Shehin Malamin ya ce da suka shiga ɗakin mai alfarma, Sarki Faisal ya samu wasu akwatunan ƙarfe, waɗanda ba a san abubuwan da ke ciki ba.
Ya ce bayan ziyarar Sarki Faisal ya kafa kwamiti da zai tantance abubuwan da ke cikin akwatunan.
Al-Rouis ya ce a lokacin shi wakili ne daga ma'aikatar kuɗi ta Saudiyya kuma bayan buɗe akwatunan an samu zinare da wasu abubuwan ado a cikin akwatin farko, yayin da na biyun kuma ya ƙunshi wasu sarƙoƙin azurfa.
Ya ƙara da cewa an kuma samu wasu wasiƙu daga al'ummar Musulmi, waɗanda ke ɗauke da baitikan yabo da addu'o'i ga Manzo SAW tare da neman rahamar Allah ta hanyarsa.
Malamin ya ce shiga ɗakin mai alfarma ya ba shi damar ganin ƙabarin Manzon Allah da Sahabbansa da kuma iyakokin ɗakin.