Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 14/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 14/08/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. An kuɓutar da Ba'amurken da aka yi garkuwa da shi a Nijar batan wata 10

    An sako wani matuƙin jirgin sama Ba'amurke ɗan mishan da aka sace a Nijar kusan wata 10 da suka gabata, bayan ya shafe lokaci mai tsawo a hannun masu garkuwa da shi.

    Garkuwa da Kevin Rideout ya tayar da hankalin ƙasashen duniya tare da haifar da binciken nemansa a faɗin yankin Sahel.

    Ƙungiyar mishan ta Serving In Mission (SIM) ta tabbatar da sakinsa, tana mai cewa Mista Rideout na cikin ƙoshin lafiya kuma yanzu yana hannun jami'an Amurka.

    Iyalansa sun ce suna matuƙar godiya ga addu'o'i da goyon bayan da suka samu daga jama'a tun bayan faruwar lamarin.

    Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan yadda aka sako shi ba, ko waɗanda suka sace shi.

    An yi garkuwa da ma'aikacin agajin Kiristan mai wa'azin bishara a gidansa da ke Yamai, babban birnin ƙasar a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

    Ana kyautata zaton cewa wasu mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke ayyukansu a yankin Sahel ne suka kama shi.

    Yankin na daga cikin wuraren da suka fi fama da rashin tsaro da tashe-tashen hankula a duniya.

  2. Amurka za ta ƙaddamar da rundunar amfani da jirage marasa matuƙa

    Rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta sanar da shirin kafa rundunar farko da za ta haɗa ƙasashe da dama domin amfani da jirage marasa matuƙa na kai hare-hare a yankin.

    Amurka ta ce ta fara tattaunawa da ƙasashen yankin tare da aika musu gayyata a hukumance domin su shiga wannan shiri.

    An sanar da hakan ne a daidai lokacin da kwamandan CENTCOM, Janar Brad Cooper, ke gudanar da ziyara a wasu ƙasashen yankin, ciki har da Saudiyya.

    A cewar CENTCOM, sabuwar rundunar da aka sanya wa suna Falcon Strike Task Force, za ta ƙunshi jirage marasa matuƙa masu kai hare-hare da za su iya aiki a sararin sama, a saman ruwa, har ma a ƙarƙashin ruwa.

    Rundunar ta ce Amurka da ƙasashen yankin ne za su riƙa tafiyar da wannan shiri tare.

    Haka kuma, ta bayyana cewa wannan sabon shiri faɗaɗawa ne ga wani shirin da Amurka ta fara watanni tara da suka gabata mai suna Scorpion Strike, wanda shi ma ya dogara ne kan amfani da jirage marasa matuƙa wajen ayyukan soja.

    Amurka ta ce ta yi amfani da jiragen marasa matuƙa na rundunar Scorpion Strike wajen kai hare-hare kan wasu tashoshin jiragen ruwa da ke kudancin Iran, kuma jami'an da suka yi aiki a wannan runduna su ne za su ci gaba da tafiyar da sabon shirin Falcon Strike tare da haɗin gwiwar ƙasashen yankin.

  3. Zan tabbatar matatun man Najeriya sun koma aiki - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce zai farfaɗo tare da tabbatar da cewa matatun man ƙasar, da suka jima ba sa aiki, za su koma aiki.

    Shugaban Tinubu ya bayar da tabbacin ne a ranar Alhamis, lokacin da Ƙungiyar Ma'aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG) suka kai masa ziyara a fadarsa.

    Da yake mayar da martani kan matsalolin ƙungiyar ta bayyana, Tinubu ya ce matatun ba sa aiki yadda ya kamata a yanzu.

    Ya jaddada cewa dole ne matatun su kasance masu riba tare da samar da amfanin da aka gina su domin sa.

    Tinubu ya kuma ce ya ɗauki alhakin gyara kadarorin da kuma matsalolin da gwamnatocin da suka gabata suka bari, ba tare da la'akari da abin da ya faru a baya ba.

    "Ni ba mutum ba ne da zan je in duba wani abu sannan in dawo in ce komai yana tafiya daidai, saboda kawai na ɓoye abubuwan da shugabannin baya suka yi.''

    Ya ƙara da cewa ''ko ma mene ne ya faru a shekarun baya, yanzu alhakina ne a matsayina na shugaban ƙasa in gyara abubuwan, in tabbatar suna aiki yadda ya kamata domin amfanin mafi yawan al'ummar ƙasar nan''.

    Shugaban na Najeriya ya ce ya ɗauki wannan alhakin, kuma zai aiwatar da shi.

  4. Shugaban Chadi ya yi wa jagoran adawar ƙasar Succès Masra afuwa

    Shugaban Chadi, Mahamat Deby, ya yi afuwa ga jagoran adawa kuma tsohon Firayim Ministan ƙasar, Succès Masra, wani abu da ya buɗe ƙofar sakinsa daga kurkuku.

    Mista Masra, wanda ke zaman hukuncin ɗaurin shekara 20, ya samu afuwar tare da wasu ƴan adawa takwas da aka kama bisa zargin shirya zanga-zanga.

    Haka kuma, an rage tare da sassauta wa wasu da ake tsare da su a sassa daban-daban na ƙasar hukuncinsu.

    Sai dai Fadar Shugaban ƙasar ta ce wannan afuwa ba ta kai matsayin cikakkiyar yafiya ta shari'a ba, wanda ke nufin hukuncin da aka yanke musu na ci gaba da kasancewa a hukumance, kuma har yanzu yana iya kasancewa ƙarƙashin matakan shari'a.

  5. Shugabannin da aka taɓa buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah a Madina

    Duk da cewa ɗakin da ƙabarin annabi Muhammad SAW yake ya kasance koyaushe a kulle sannan ba a barin jama'a su shiga, amma wasu shugabannin ƙasashe sun samu damar shiga ɗakin, ɗaya daga cikin wurare mafi daraja a addinin Islama.

    Ƙabarin na annabi SAW ya kasance a cikin ɗakin daya daga cikin matansa, Nana Aisha da ke a gaban masallacin Madina mai tsarki.

    A cikin ɗakin akwai ƙaburburan Sahabbansa guda biyu, Abu Bakr RA da kuma da Umar RA.

    BBC ta samu ƙarin bayani daga hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain kan shugabannin da suka taɓa samun damar shiga ɗakin Ƙabarin Manzon Allah (SAW).

  6. Yariman Saudiyya ya gana da kwamandan CENTCOM a Jeddah

    Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya ya ruwaito cewa Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya gana da Brad Cooper, kwamandan rundunar CENTCOM ta sojojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

    Jagororin biyu sun tattauna kan haɗin gwiwar tsaro tsakanin Saudiyya da Amurka.

    Bin Salman da Mista Cooper sun kuma tattauna kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki a halin yanzu, da kuma ƙoƙarin rage tashin hankali tare da ƙarfafa tsaro da zaman lafiya a yankin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya bayyana.

    A cikin makonnin da suka gabata, bayan hare-haren da aka kai kan Saudiyya, ƙasar tare da Amurka sun ƙaddamar da hare-haren haɗin giwar soji kan ƙungiyoyin mayaƙa masu alaƙa da Iran a Iraƙi.

  7. Me ke faruwa a mashigar Hormuz yayin kokawar iko da ita?

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa har yanzu akwai taƙaitar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, yayain da rikici kan ikon mashigar ke ƙara tsananta tsakanin Amurka da Iran.

    Alƙaluma daga kamfanin sanya idanu kan zirga-zirgar jiragen ruwa na Kepler sun nuna cewa jiragen ruwan da suka ratsa ta mashigar a ranar Alhamis ya ɗan ƙaru kaɗan kan jirage 12 da su bi ta mashigar a ranar Laraba.

    Kididdigar Kepler ta nuna cewa jirage tara ne suka ratsa mashigin a jiya Alhamis, idan aka kwatanta da jirage biyar da suka ratsa a ranar Laraba.

    Daga cikin waɗannan, jirage biyar sun shiga Tekun Fasha, yayin da huɗu suka fita zuwa Tekun Oman, kuma mafi yawansu sun bi hanyar jiragen ruwa ta Iran.

  8. Amurka ta yi barazanar mayar da Iran saniyar ware a duniya

    Sakataren Baitul-malin Amurka, Scott Bessent ya yi barazanar mayar da Iran saniyar ware a fannin tattalin arziki, irin wanda duniya ba ta taɓa gani ba.

    Bai yi ƙarin bayani game da batun ba, amma ya ce za a iya sanar da sabbin matakai kan Iran a mako mai zuwa.

    Sakataren Tsaro Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta ci gaba da rufe wa Iran hanyoyin ruwa na tsawon lokaci.

    Iran ta ci gaba da riƙe ikon Mashigin Hormuz.

    Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayar da rahoton harin da Iran ta kaiwa wasu jiragen dakon mai biyu.

  9. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, Haji babbar rana, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Yau ma kamar jiya, Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.