Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta sake watsi da tayin Barca kan Rodri, Inter za ta diba lafiyar Spence
Manchester City ta yi watsi da sabon tayin Barcelona na fam miliyan 55 kan ɗanwasanta na Spain Rodri, inda take son fam miliyan 60 ga ɗanwasan na tsakiya mai shekara 30 yayin da ƙungiyoyin biyu ke ci gaba da tattaunawa. (Sky Sports)
Ɗanwasan baya na Tottenham da Ingila Djed Spence, mai shekara 26, za a diba lafiyarsa a ranar juma'a inda zai kammala yarjejeniya da Inter Milan ta fam miliyan 25.6. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Arsenal ta taya ɗanwasan baya na Spain Marc Pubill amma Atletico Madrid ta ce ɗanwasan mai shekara 23 ba na sayarwa ba ne. (AS - in Spanish)
Hull City na dab da kammala cinikin ɗanwasan tsakiya na Faransa Lucas Gourna-Douath, mai shekara 23, daga Red Bull Salzburg kan fam miliyan 3.4. (L'Equipe - in French)
Hull ta taya ɗanwasan tsakiya na Everton da Ingila Tim Iroegbunam, mai shekara 23 kan fam miliyan 15. (Teamtalk)
Ipswich Town na da tabbacin ɗauko ɗanwasan gaba na ƙasar Jamus Derry Scherhant, mai shekara 23 daga Freiburg a wannan bazara. (Teamtalk)
Bayer Leverkusen ta yi watsi da tayin fam miliyan 17 na Ipswich kan ɗanwasan tsakiya na Argentina Exequiel Palacios. (Sky Sports Germany)
Napoli sai ta tantance makomar ɗanwasan gaba Lorenzo Lucca, mai shekara 25, kafin soma tattaunawa da Arsenal kan batun ɗanwasanta na Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 29. (Corriere dello Sport - in Italian)
West Ham na da tabbacin cimma yarjejeniya tsakaninta da Celtic kan ɗanwasan tsakiya na Belgium Arne Engels, mai shekara 22. (Football Insider)