Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhimman abubuwa 5 kan zaɓen gwamnan jihar Osun
- Marubuci, Gift Andrew
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
- Aiko rahoto daga, Lagos, Nigeria
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A ranar Asabar mai zuwa ne za a gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun, mai ƙananan hukumomi 30.
Wannan shi ne karo na bakwai da za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
An gudanar da zaɓukan gwamna a jihar a shekarun 1999 da 2003 da 2007 da 2010 da 2014 da 2018 da kuma 2022.
Tun bayan ƙirƙirar Jihar Osun a shekarar 1991, ta yi gwamnoni har guda 10, kama daga na soja zuwa na farar hula.
Jerin mutanen da suka taɓa zama gwamnan jihar
- Leo Segun Ajiborisha
- Isiaka Adeleke
- Anthony Udofia
- Anthony Obi
- Theophilus Bamigboye
- Bisi Akande
- Olagunsoye Oyinlola
- Rauf Aregbesola
- Gboyega Oyetola
- Ademola Adeleke
Gwamnan jihar na yanzu Ademola Adeleke na neman wa'adin mulki na biyu.
A 2022 ne Mista Adeleke ya lashe zaɓen gwamnan jihar ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, bayan doke gwamna mai ci a lokacin Gboyega Oyetola.
Yanzu kuma Gwamna Adeleke na takara ne jam'iyyar AP da ya koma bayan ficewarsa daga PDP.
Cikin wannan maƙala mun duba wasu muhimman abubuwa biyar game da zaɓen.
Yawan masu rajistar zaɓe
Cikin wata sanarwa da shugaban INEC, Joash Amupitan ya fitar a shafin X, ya nuna cewa jihar na da rajistar masu zaɓe miliyan 2,339,233 da za su iya kaɗa ƙuri'arsu a faɗin rumfunan zaɓe 3,763 da yankunan ƙananan hukumomin jihar 30.
INEC ta ce ta ƙara yawan na'urorin tantance masu kaɗa ƙuri'a a jihar zuwa 5,130.
Haka ma hukumar ta ce ya nunka yawan nau'urorin jiran ko-ta-kwana zuwa 1,328 ko da za a samu matsala a wasu wuraren.
Dangane da batun tsaro, shugaban na INEC ya ce hukumarsa na ƙarfafa alaƙa da jami'an tsaro domin tafiyar da zaɓen cikin lumana.
Hukumar zaɓen ta ce za ta yi aiki da sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin sufuri domin taimaka wa zaɓen.
Me ya sa ake zaɓen daban da sauran jihohi?
Tun bayan ƙirƙirar Jihar Osun a shekarar 1991, zaɓukan da ake gudanarwa a jihar sun kasance masu ɗaukar hankali, inda ƴan takara da ma masu kaɗa ƙuri'a ke fuskantar fafatawa mai zafi.
Dukkan zaɓukan gwamnan da aka gudanar a jihar tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya sun kasance suna ƙarewa a kotuna.
Sai dai zaɓen shekarar 2007 ne kaɗai ya kai ga kotu ta tsige gwamnan da ke kan mulki tare da ayyana wani ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
A zaɓen na 2007, Hukumar INEC ta ayyana Olagunsoye Oyinlola na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Sai dai bayan shafe shekaru uku ana fafatawa a kotu, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Oyinlola tare da ayyana Rauf Aregbesola na jam'iyyar ACN a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen, lamarin da ya haifar da sauyin gwamnati nan take.
An fara ƙirga wa'adin mulkin Aregbesola ne daga ranar da ya hau mulki, duk da cewa Oyinlola ya shafe shekaru uku yana kan kujerar gwamna.
Sakamakon wannan shari'a da kuma sauyin gwamnatin da aka samu, zaɓukan gwamna a Jihar Osun suka daina gudana lokaci ɗaya da na sauran jihohin Najeriya.
Duk wanda ya yi nasara a zaɓen da za a gudanar, shi ne zai jagoranci jihar daga shekarar 2026 zuwa 2030.
Ƴantakarar da ke fafatawa a zaɓen
Jam'iyyu 14 ne suka tsayar da ƴan takara domin neman kujerar gwamnan jihar.
Sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin manyan jam'iyyu uku da suka fi ƙarfi a jihar
Gwamna mai ci a yanzu, Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord Party, zai fafata da ɗan takarar Jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Oyebamiji, da kuma ɗan takarar ADC, Dr. Najeem Folasayo Salaam.
Duka ƴantakarar za su shiga zaɓen ne da ƙarfin magoya baya.
Ademola Adeleke, wanda shi ne gwamnan jihar mai ci, na bayyana irin nasarori da ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ta samu tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2022 a matsayin hujjar neman wa'adi na gaba.
A gefe guda kuma, Asiwaju Bola Oyebamiji tsohon kwamishinan kuɗi ne na jihar.
Yana samun goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Harkokin Tattalin Arzikin Ruwa da Tekuna na Najeriya a yanzu, Gboyega Oyetola.
Haka kuma yana samun goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.
Shi kuwa Dr. Najeem Folasayo Salaam, na samun goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola kuma sakataren jam'iyyar ADC na ƙasa, wanda shi ma yake da tasiri a siyasar jihar.
Ta yaya sabuwar dokar zaɓe za ta shafi zaɓen?
Zaɓen jihar zai kasance na uku da INEC za ta gudanar tun bayan da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sanya hannu kan Dokar Zaɓe ta 2026.
Haka kuma, shi ne zaɓe na ƙarshe kafin babban zaɓen ƙasar na 2027.
Saboda haka, za a fara aiwatar da wasu sabbin tanade-tanaden dokar zaɓe a wannan zaɓen.
Wasu daga cikin sabbin tanade-tanaden sun haɗa da:
Rajistar masu kaɗa ƙuri'a:
An rage takardun da ake buƙata wajen yin rajistar zaɓe zuwa uku kacal, wato:
Takardar haihuwa (Birth Certificate)
Fasfo na Najeriya (Nigerian Passport)
Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN)
Katin zaɓe da za a iya saukewa daga intanet:
Masu zaɓe za su iya sauke katinsu na zaɓe kai tsaye daga shafin intanet na INEC.
Tura sakamakon zaɓe ta na'ura:
Tura sakamako zuwa rumbun INEC Result Viewing Portal (IReV) ta zama wajibi.
Sai dai idan aka samu matsalar sadarwa ko gazawar na'ura, INEC za ta yi amfani da takardar tura sakamako ta form EC8A domin tattarawa sakamakon.
Hanyar zaɓen 'yan takara a jam'iyyu:
Sabuwar dokar ta amince da hanyoyi biyu kacal da jam'iyyun siyasa za su bi wajen zaɓen 'yan takararsu:
Zaɓen ƴartinƙe (Direct Primaries)
Yarjejeniya (Consensus)
Wannan na nufin an soke tsarin zaɓen wakilai (Deligates).
Fitar da kuɗaɗen zaɓe ga INEC:
Dole ne gwamnati ta bai wa INEC kuɗaɗen gudanar da zaɓe aƙalla wata shida kafin babban zaɓe.
Mika sunayen 'yan takara:
Jam'iyyun siyasa za su miƙa sunayen ƴan takararsu ga INEC aƙalla kwanaki 120 kafin ranar zaɓe.
A baya kuwa ana buƙatar kwanaki 180.
Fitar da jerin sunayen ƴan takara na ƙarshe:
INEC za ta bayyana jerin sunayen 'yan takara na ƙarshe kwanaki 60 kafin zaɓe.
A baya kuwa ana yin hakan kwanaki 150 kafin ranar zaɓe.
Sai dai akwai tanadi a Sashe na 60(3) na dokar, wanda ya ce idan aka samu matsalar sadarwa da za ta hana tura sakamako ta hanyar laturoni, INEC za ta yi amfani da takardar tura sakamako ta form EC8A domin tattarawa sakamakon.
Dokokin zaɓen
- Ban da sata ko lalata akwatunan zaɓe.
- Kada a yi kamfe a rumfunan zaɓe.
- Guje wa shiga tashin hankali ko tsoratar da masu zaɓe.
- Kauce wa saye ko sayar da ƙuri'a.
- Babu katsalandan ga tsarin gudanar da zaɓen.
- Dakatar da zirga-zirgar mutane ba tare da izini ba a wuraren da aka iyakance.
Sabon Kwamishinan ƴansandan Jihar, Samuel Etaifo, wanda aka tura domin jagorantar harkokin tsaro a lokacin zaɓen, ya isa jihar kuma ya fara aiki gabanin zaɓen.
Rundunar ƴansandan ta ce ta ɗauki isassun matakan tsaro domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali.