Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu 3 da Kudu maso Yammacin Najeriya ke la'akari da su wajen zaɓen shugaban ƙasa
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yankunan ƙasar na da abubuwan da suke la'akari da su wajen yanke shawarar wanda za su bai wa ƙuri'arsu.
Kudu maso Yamma, yanki ne da ke taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, musamman idan aka zo zaɓen shugaban ƙasa.
Asalin mutum, dabarun tattalin arziki, tsaro, kasuwanci da kuma yadda ɗan takara zai wakilci muradun yankin na daga cikin abubuwan da ke iya tasiri ga ra'ayin masu zaɓe.
Amma wadanne abubuwa ne suka fi muhimmanci ga masu zaɓe a Kudu maso Yamma da yadda ra'ayin yankin zai iya sauya taswirar zaɓen shugaban ƙasa na 2027?
Adadin masu kaɗa ƙuri'a
Idan muka yi la'akari da adadin masu rajistar zaɓe a yankin, Kudu maso Yamma na cikin manyan wuraren da za su iya taka muhimmiyar rawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Bayanai daga hukumar INEC sun nuna cewa jihohi shida na yankin suna da masu rajistar zaɓe 17,958,966 a zaɓen 2023.
Lagos ce ke da mafi yawan masu rajista da 7,060,195, sai Oyo da ke da 3,276,675, sannan Ogun mai 2,688,305.
Bayan haka akwai Ondo mai 1,991,344, Osun mai 1,954,800 da kuma Ekiti, wadda ke da 987,647.
Amma yawan masu rajista kaɗai ba ya nufin cewa duk waɗannan mutane ne za su fito su kaɗa ƙuri'a. Bayanan INEC na 2023 sun nuna cewa jihohin Kudu maso Yamma sun karɓi katin zaɓe sama da miliyan 15.5, daga cikin masu rajista kusan miliyan 18.
A lokacin da aka fara sabunta rajistar masu zaɓe gabanin zaben 2027, INEC ta bayyana cewa ana samun ƙarin sabbin masu rajista, kuma bayanan hukumar sun nuna cewa Lagos da Ogun na daga cikin jihohin da suka samu masu rajista sosai a yankin.
Ga yadda jimillar masu zaɓe yake a shiyyoyin ƙasar (2023):
- Arewa maso Yamma - 22,255,562
- Kudu maso Yamma - 17,958,966
- Arewa ta Tsakiya - 15,363,731
- Kudu maso Kudu - 12,674,248
- Arewa maso Gabas - 12,542,429
- Kudu maso Gabas - 10,907,606
Abubuwan da mutanen yankin ke la'akari da su a zaɓen shugaban ƙasa
"Yawancin abin da ya fi dabaibaye siyasa da alƙiblar yankin shi ne ƙabilanci, amma ba lallai su bi alƙibla ɗaya ba a lokacin zaɓe," in ji Kabir Yayo Ali, tsohon wakilin BBC Hausa a Ibadan, wanda ya shafe shekaru yana aiko da rahotanni kan zaɓuka da siyasar yankin.
Masana sun ce Kudu maso Yamma na daga cikin yankunan da ke da matuƙar tasiri a siyasar Najeriya, musamman a zaɓen shugaban ƙasa.
Wani abin da suke dangantawa da wannan tasiri shi ne yadda mafi yawan al'ummar yankin suke da asali daga ƙabilar Yarbawa, tare da samun manyan jagororin siyasa da dattawan da ke da tasiri kan ra'ayin jama'a.
Dakta Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ne kuma malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano (CAS) ya lissafo wasu abubuwa uku da alƙiblar yankin yake karkata a kai a zaɓen shugaban ƙasa
1. ƘABILANCI
Dakta Sufi ya ce abin da yankin ya fi bayar da fifiko da jan hankalinsu shi ne ɓangaranci, kamar yadda lamarin ke tasiri a kusan dukkanin yankunan kasar.
Ya ce suna la'akari da wanda ya fito daga yankinsu fiye da komai, domin idan har akwai wani dantakara daga yankinsu sukan yi kokarin mara masa baya ya kai ga ci.
Shi ma Kabiru Yayo yana da ra'ayin cewa: "Suna amfani da yawansu wajen cusa siyasar ƙabilanci. A kowane lokaci su kaɗai suke yi, ba sa hangen 'yan sauran sassan ƙasa. Kuma hakan na haifar musu da koma-baya".
Sai dai Sufi ya ce yawancin yankin suna bin alƙibla guda idan aka zo zaɓe, in banda Legas da aka samu sauyi a baya-bayan nan da suka mara wa Peter Obi baya a zaɓen 2023.
"Yankin, alƙibla ɗaya yake fuskanta... yawancin jihohin ba su cika rarrabe ƙuri'unsu ba, shi ya sa duk wanda ya samu amincewar yankin ya samu damar da za ta ba shi nasara."
2. AYYUKAN RAYA ƘASA
Yankin Kudu maso Yamma na kallon irin ci gaban da gwamnati mai ci ta kawo musu ko kuma jam'iyya.
"Sukan kalli wanne tagomashi suke samu daga gwamnati, idan suka kwatanta da wani yankin," in ji Dr Sufi.
Yawancin manyan abubuwan ci gaba da manyan ayyuka da gwamnati ke yi dai na ba da fifiko sosai a yankin, musamman ma da suke cikin waɗanda ke samar da haraji mai gwaɓi ciki har da Legas da ke kan gaba.
3. SAMUN MANYAN MUƘAMAI
Idan aka zo rabon muƙamai ana la'akari sosai wajen yadda za a kasafta manyan muƙaman gwamnati ga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Dr Sufi ya ce muƙaman da aka ba yankin su ma suna yin tasiri wajen jan ra'ayin masu zaɓe saboda irin ƙarfin ikon da suke da shi.
Ya ce mutanen yankin sukan tsaya su ga yadda ake damawa da su a gwamnati ko jam'iyya kafin yanke shawarar su yi ɗantakarar shugaban ƙasa wanda suke ganin zai tafi da su.
Sai dai masanin ya ce hakan ba yana nufin cewa al'ummar yankin kullum suna bin matsaya ɗaya ba ce, domin akan iya samun sauyi a wasu lokutan.
Me ya sa Kudu maso Yamma ke da muhimmanci?
Kabir Yayo Ali ya ce muhimmancin yankin a zaɓen shugaban ƙasa ya sa kusan duk wani ɗan siyasa ke neman goyon bayan al'ummar yankin idan lokacin zaɓe ya yi.
Ya ce shi ya sa mafi yawancin lokuta sai an yi gamayyar jam'iyyu da haɗin kai tsakanin yankuna ga ɗan takarar da ke son samun gagarumar nasara a Kudu maso Yamma.
"Jihar Oyo ita ce kan gaba, saboda ita ce cibiyar jihohin wannan yanki. Sai Ogun, sai Legas. Ita ce ta haifar da sauran jihohin," in ji shi.
Duk da girman tasirin Lagos, bambancin ƙabilu da yawan mutanen da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya da ke zaune a jihar na iya sa yanayin siyasarta ya bambanta da sauran jihohin yankin.
Shi ma Dr Sufi ya ce za a iya kallon jihar Oyo na matsayin ta gaba-gaba a wajen tasiri a siyasar yankin Kudu maso Yamma.
Jihohin da suka fi tasiri (Lagos, Oyo da Ogun)
Duk da cewa dukkan jihohin Kudu maso Yamma na da muhimmiyar rawa a zaɓen shugaban ƙasa, akwai Oyo da Ogun da Legas da suka fi jan hankali saboda yawan masu rajistar zaɓe da kuma irin tasirin sakamakonsu.
Su kaɗai suna da sama da miliyan 13 na masu rajistar zaɓe, wato fiye da kashi 75 cikin 100 na masu rajistar zaɓe a shiyyar.
Bayanan hukumar INEC na zaɓen 2023 sun nuna cewa Lagos ce ke da mafi yawan masu rajistar zaɓe a yankin, da mutum 7,060,195. Bayan Lagos sai Oyo mai 3,276,675, sannan Ogun mai 2,688,305.
Wannan ya sa Lagos, Oyo da Ogun kaɗai suke da kusan miliyan 13.03 na masu rajistar zaɓe, adadin da ya fi na kowace shiyya a ƙasar ban da Arewa maso Yamma.
Amma abin da ya fi jan hankali shi ne yadda waɗannan jihohi suka raba ƙuri'unsu tsakanin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa a 2023.
A Lagos, inda Bola Tinubu ya kasance tsohon gwamna kuma ake kallon jihar a matsayin babbar cibiyar siyasarsa, Peter Obi na Labour Party ne ya samu nasara. Obi ya samu 582,454 yayin da Tinubu ya samu 572,606, tazarar ƙuri'a kusan dubu 10 ce. Atiku Abubakar na PDP kuwa ya samu 75,750.
A Oyo, Tinubu ya samu nasara da 449,884 ƙuri'a, yayin da Atiku ya samu 99,110, Obi kuma 182,977. A Ogun, Tinubu ma ya yi nasara da 341,554, yayin da Atiku ya samu 85,829, Obi kuma 123,831.
Sakamakon zaɓen 2023 ya nuna cewa Kudu maso Yamma na da wata alƙiblar ba lallai a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.