Ƴanwasa mafiya tsufa da suka taɓa buga Gasar Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Jonty Colman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Ƴanwasa bakwai ne kawai da shekarunsu ya haura 40 suka taɓa buga gasar cin kofin duniya ɓangaren maza, tun da aka fara gasar shekaru 96.
A yanzu za a samu ƙarin mutum biyar a wannan shekara bayan da ƙasashensu suka lissafa su cikin tawagarsu.
Golan Masar Essam El Hadary ne ɗawasan da ya fi tsufa da ya buga gasar cin kofin duniya yana da shekaru 45 da kwana 161 a duniya.
El Hadary ya kafa tarihin ne a lokacin da ya buga wasa a gasar cin kofin duniya a shekarar 2018 a matakin rukuni inda suka doke Saudiya 2-1.
Ƴanwasa 10 da suka fi tsufa a gasar cin kofin duniya duka ba su wuce shekaru 39 ba.
Mai tsaron ragar Scotland Craig Gordon, ɗan shekaru 43 shi ne ɗawasan da ya fi tsuda da zai buga gasar a wannan shekara.
Wannan ne karo na farko da Scotland za ta buga gasar cikin shekaru 28, inda ɗanwasan zai samu wannan dama a matsayin shi na ɗanwasa na biyu da ya fi tsufa a tarihin gasar.
Kyaftin ɗin Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekaru 41 zai iya shiga cikin jerin ƴanwasan da za su buga wa ƙasar gasar a karo na shida.
Ƴanwasa irinsu El Hadary, Faryd Mondragon, Roger Milla da Pat Jennings ne kaɗai suka taɓa buga gasar sau ɗaya kawai a daidai wannan shekaru.
Mai tsaron bayan ƙasar Japan Yuto Nagatomo, mai shekaru 39 na daga cikin ƴanwasan da suka fi tsufa da za su buga gasar idan har ya samu shiga a wannan shekarar ta 2026.
Ɗanwasan gaba na Bosnia and Herzegovina Edin Dzeko da mai ɗanwasa tsakiyar Croatia Luke Modric, dukkansu sun kai shekaru 40, kuma akwai yiwuwar za su buga gasar ta cin kofin duniya.
Shi ma golan Cape Verde, Vozinha zai cika shekara 40 gabanin wasar da ƙasarsa za ta buga a karon farko a gasar cin kofin duniya, kuma hakan zai ba shi damar shiga cikin jerin ƴanwasan da suka fi tsufa da suka buga gasar.
Send us your questions
Ƴanwasa 10 da suka fi tsufa a tarihin gasar cin kofin duniya
- Essam El Hadary - Ya buga wasa tsakanin Masar da Saudiya (25 ga watan Yuni, 2018) – Yana ɗan shekara 45 da kwanaki 161 a duniya
- Faryd Mondragon – Ya buga wasa tsakanin Kolombiya da Japan (24 ga watan Yuni, 2014) – Yana ɗan shekara 43 da kwanaki 3 a duniya
- Roger Milla – Ya buga wasa tsakanin Kamaru da Rasha (28 ga watan Yuni, 1994) – Yana ɗan shekara 42 da kwanaki 39 a duniya
- Pat Jennings – Ya buga wasa tsakanin Arewacin Ireland da Brazil (12 ga watan Yuni, 1986) – Yana ɗan shekara 41a duniya
- Peter Shilton – Ya buga wasa tsakanin Ingila da Italiya (7 ga watan Yuli, 1990) – Yana ɗan shekara 40 da kwanaki 292 a duniya
- Dino Zoff – Ya buga wasa tsakanin Italiya da Jamus (11 ga watan Yuli, 1982) – Yana ɗan shekara 40 da kwanaki 133 a duniya
- Ali Boumnijel – Ya buga wasa tsakanin Tunisiya da Ukraine (23 ga watan Yuli, 2006) – Yana ɗan shekara 40 da kwanaki 71 a duniya
- Jim Leighton – Ya buga wasa tsakanin Scotland da Maroko (23 ga watan Yuni, 1998) – Yana ɗan shekara 39 da kwanaki 334 a duniya
- David James – Ya buga wasa tsakanin Ingila da Jamus (27 ga watan Yuni, 2010) – Yana ɗan shekara 39 da kwanaki 330 a duniya
- Atiba Hutchinson – Ya buga wasa tsakanin Kanada da Maroko (1 ga watan Disamba, 2022) – Yana ɗan shekara 39 da kwanaki 296 a duniya
Sashen wasanni na BBC Ask Me Anything ne ya tattaro waɗannan bayanai.











