Me ya kamata a yi idan mutum ya yanke jiki ya faɗi?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Talata 11 ga watan Agusta ne wasan wasan sada zumunta na share fage a Katsina ya rikiɗe zuwa ɗaya daga cikin labaran da suka fi tayar da hankali da bayar da mamaki a harkar ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Chinedu Ozor, matashin ɗan wasan baya mai shekara 18 da Katsina United ta ɗauka a kwanakin baya, ya faɗi a fili yayin wasan da ƙungiyar ta kara da Niger Tornadoes a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.
Cikin ƴan sa'o'i kaɗan, duniyar ƙwallo a ƙasar ta shiga jimami, bayan da aka bayyana cewa ya mutu kwatsam ba zato ba tsammani.
Sai dai daga baya aka samu wani abin mamaki, inda a daidai lokacin da ake ci gaba da jimamin mutuwarsa, sai rahotannin suka fara fitowa cewa fa lallai bai mutu ba.
Ana fafata wasannin ne a ƙarƙashin a gasar share-fage na kofin Gusau/Ahlan da ake yi domin shirye-shiryen fara gasar premier ta baɗi.
An dai gano cewa Ozor yana da rai ne bayan ma'aikatan ɗakin ajiyar gawa sun lura yana motsi bayan an riga an cire tsammani. Daga nan aka mayar da matashin zuwa Asibitin Janar na Katsina, inda aka ce an kai shi sashen kula da marasa na musamman wato ICU, sannan aka sanya masa iskar oxygen.
Nan take, labarin da ya fara a matsayin rasuwar ɗan wasan ƙwallon ƙafa ya koma wani labarin daban na tashi bayan 'mutuwa.'
Ozor ya koma Katsina United ne kwanan nan bayan zamansa a Kano Pillars. Yana da shekara 18 kacal,wanda hakan ya sa ake ƙirga shi a cikin zaratan matasan da ake musu kallon suna rawar takawa sosai a harkar, kuma suke da babban burin da suke son cimmawa.
Sai dai bayan kwana ɗaya kuma aka sake samun labarin cewa matashin ɗan wasan ya rasu.
Me ke janyo yanke jiki a faɗi?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Muhammad Dahir, likita ne a ɓangaren 'community medicine' a asibitin koyarwa na tarayya da ke Katsina, ya ce yanke jiki ya faɗi na zuwa ne daga ƙwaƙwalwar mutanen.
Likitan ya ce ana samun yawaitar irin haka a tsakanin ƴanƙwallon ƙafa, sai dai ya ce akwai abu biyu da ya kamata a fahimta.
"Idan ka ga mutum mai lafiya, misali wanda yake wajen motsa jiki ya yanke jiki ya faɗi ba tare da hatsari ba, ko kuma a ce ya bugu, to akwai matsala," in ji Dr Muhammad.
Sai dai ya ce akwai bambanci tsakanin bugun zuciya na "heart attack," da abin da ke faruwa a irin wannan yanayi.
"Shi wannan abin da ke faruwa ana kiransa da suna cardiac arrest ne. Ita ma zuciya tana da tsarin lantarki kamar yadda wutar lantarki take. Idan mutum lafiyayye ya yanke jiki ya faɗi, to ana kiransa 'sudde cardiac arrest' wato zuciya ta tsaya cak ba zato ba tammani," in ji likitan.
Likitan ya ƙara da da cewa a lokuta dama yanayin yakan faru ne ba tare da gargaɗi ko nuna alama ba.
"Shi heart attack da ake magana jini da ke zuwa zuciya ne yake daina zuwa saboda jijiyoyi sun toshe. Shi kuma cardiac arrest yanayin lantarkin jikin ne ke samun matsala. Idan lantarkin ta tsaya, sai komai ya tsaya cak."
Ya ce jinin ne abinin zuciya, "kuma zuciya ke ba sauran sassan jiki jini, kuma jinin ne ke ɗauke da sinadarin oxygen wanda shi ne makamashin da ke taimakon sauran sassan jiki gudanar da ayyukan jiki."
Likitan ya ce da zarar babu wannan sinadarin oxygen ɗin, "ƙwaƙwalwa ce ke fara fuskantar akwai matsala, sai ta ɗauke wuta, sai ka ga mutum ya fara fita hayyacinsa," in ji shi.
Me ya kamata a yi?

Asalin hoton, Getty Images
Dr Muhammad Dahir ya ce akwai abubuwa da dama da ya kamata a kula da su idan mutum ya yanke jiki ya faɗi.
Ya ce da farko babban abin da ya fara shi ne a kira lambar gaggawa domin neman taimakon asibiti ko ma'aikatan jinya.
"Sai a fara dannar ƙirjin da ake kira 'CPR'. Ana so ne a kwantar da mutum a rigingine, sai a riƙa masa dannar ƙirgi," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa akwai buƙatar kowa ya koya yadda ake yi.
Dr Muhammad ya ce ana so ne a dunƙule hannun dama, a ɗaura na hagu a sama, sannan a riƙa danna.
"Ana so a riƙa danna tsakanin 100 zuwa 1200 a cikin minti 1, kuma ana so dannar ta kai zuwa sentimita 5 zuwa 6. Sannan a duk danna kamar 30 a hura masa iska sau biyu a baki."
Likitan ya ce idan aka yi gaggawar ɗaukar wannan matakin kafin zuwa asibiti, yana taimakawa waje ƙara damar tsira da rai.












