Manyan dazukan Najeriya 6 da suka zama mafakar ƴanbindiga

Wani daji

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wani gumurzu da aka yi tsakanin jami'an tsaron Najeriya da ƴanbindiga a jihar Kebbi ya sake jawo hankali kan muhimmiyar rawar da manyan dazuka ke takawa a matsalar tsaron arewacin ƙasar.

Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun yi artabu da wani gungun ƴanbindiga da suka taso daga jihar Sokoto zuwa Kebbi ta cikin daji bayan samun bayanan sirri, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro 10 tare da kashe fiye da ƴanbindiga 40.

Shekaru da dama kenan manyan dazukan arewacin Najeriya ke kasancewa wuraren da ƴanbindiga ke samun mafaka da tattara makamai da kuma shirya hare-hare.

Faɗin waɗannan dazuka da yadda wasu daga cikinsu ke haɗa jihohi da dama har ma da ƙasashe maƙwabta, na ba wa miyagun damar kauce wa jami'an tsaro da kuma sauya matsuguni cikin sauƙi idan aka matsa musu a wani yanki.

Yayin da gwamnati da hukumomin tsaro ke ƙara ƙaimi wajen fatattakar masu aikata laifuka daga irin waɗannan wurare, har yanzu akwai wasu dazuka da ke ci gaba da zama sanannun mafaka ga ƙungiyoyin ƴanbindiga da sauran masu ɗauke da makamai.

A wannan labari za mu duba manyan dazukan arewacin Najeriya shida da suka fi fitowa a rahotannin tsaro kan ayyukan ƴanbindiga.

Dajin Sambisa

Ƴanbindiga

Asalin hoton, AFP

Wannan yanki ne a yankin Borno kuma daji ne da ya fi ɗaukar hankali a duk lokacin da aka yi maganar Boko Haram a Najeriya.

Dajin Sambisa na cikin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Yana da nisan kilomita 60 kudu maso gabashin birnin Maiduguri.

Dajin Sambisa ya yi iyaka da jihohin Yobe da Gombe da Bauchi ta wuraren Darazo, kuma masana da dama sun yi amanna cewa dajin ya naura yamma har jihar Kano.

Girman dajin ya kai murabba'in kilomita 60,000. Turawan mulkin mallaka sun mayar da wajen gandun daji a zamanin mullkinsu.

"Girman dajin ya ninka girman yankin kudu maso gabashin Najeriya," a cewar Farfesa Dikwa, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma wanda ya san Dajin Sambisa da kyau.

Dajin na ƙarƙashin ƙananan hukumomin Askira/Uba daga kudu da Damboa daga kudu maso yamma da kuma Konduga da Jere daga yammaci.

Dajin yana zagaye da dogwayen tsaunukan Gwoza da Mandara masu tsawon mita 1,300 waɗanda suka haɗe kan iyakar Najeriya da Kamaru.

A shekarun baya-baya, mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP sun mayar da dajin mafakarsu.

Dajin Kainji

ƴan bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Dajin Kainji - wanda ya haɗa jihohin Neja da Kwara a yammacin Najeriya - na da faɗin kusan murabba'in kilomita 5,341.

A baya an fi saninsa da gandun namun daji, amma a baya-bayan nan dajin ya zama cibiyar ayyukan masu ɗauke da makamai.

A farkon wannan wata ne aka sako wasu mutane kimanin 170 da ƴanbindiga suka sace a farkon shekarar nan a jihar Kwara.

Dr. Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security Limited, ya ce idan ba a yi abin da ya dace ba, akwai barazanar dajin zai iya zama tamkar Sambisa.

"Akwai ƙungiyoi da dama da dabobin ƴanbindiga a cikinsa, sannan a baya-bayan nan akwai ƙungiyoyi masu alaƙa da jihadi irin su IS da al'Qaeda da suke shiga dajin suna iko da tozarta mazauna ƙauyukan da ke kusa da dajin," in ji shi.

Dajin Rugu

ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Dajin Rugu wani katafaren daji ne mai cike da bishiyoyi ya shafi jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna da kuma jihar Neja.

Bayanai sun ce dajin ya kai murabba'in kilomita kimanin 2,000, kuma ya shafi har Jamhruiyar Nijar.

A baya dajin ya yi fice da namun daji da kuma wajen yawon buɗe ido, amma a yanzu ya zama ɗaya daga cikin manyan wuraren da ƙungiyoyin ƴanbindiga ke amfani da su a matsayin mafaka da kuma sansanin gudanar da ayyukansu.

Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana Rugu a matsayin wani babban daji mai haɗari wanda ya zama mafaka ga ƴan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dajin Kamuku

ɗanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Dajin Kamuku, wanda a baya aka fi sani da Gandun Kamuku (Kamuku National Park), wani daji ne mai duhu da ke cikin yankin ciyayi da bishiyoyi.

Cikin wata hira da BBC Barista Audu Bulama Bukarti ya ce dajin shafi yammacin jihar Kaduna, musamman yankin Birnin Gwari.

Dajin - mai murabba'in kilomita 1,1200 - shi ne mafi yawan ƴanbindigar da ke addabar yammacin jihar Kaduna ke amfani da shi a matsayin mafakarsu.

Dajin Sububu

wani ɗanbindigar

Dajin Sububu na ɗaya daga ciin manyan dazukan da ƴanbindiga ke samun mafaka a arewacin Najeriya.

Dajin ya shafi ƙananan hukumomin Maradun da Maru Shinkafin da kuma Bakura a jihar Zamfara.

Sannan a malala har zuwa jihar Sokoto ta yankin ƙananan hukumomin Isa da Rabah da Sabon Birnin, kamar yadda Dr. Bukarti ya bayyana.

Kacalla Halilou Sububu da sojojin Najeriya suka kashe a shekarar da ta gabata na daga cikin fitattun ƴanbindigar da ke amfani da dajin.

Kuyan Bana

Wasu ƴanbindiga

Asalin hoton, NPF

Dajin Kuyan bana, wani gawurtaccen daji ne da ya haɗa jihohi Zamfara da Katsina da Kebbi da Neja har ma da jihar Sokoto.

Masana tsaro sun ce saboda duhun dajin da kuma yadda ya haɗa jihohin ƙasar da dama, ya sa ƴanbindiga suka mayar da shi mafakarsu.

Dr. Bukarti ya ce ƴanbindigar da ke wannan daji ne ke addabar wasu yankunan waɗannan jihohi.