Me ya sa Boko Haram ke kai wa manyan sojoji hare-hare?

Lokacin karatu: Minti 5

Ƴan Najeriya na ci gaba da nuna alhini kan rahotonnin kisan wani babban kwamandan sojin Najeriya a wani harin mayaƙan Boko Haram a garin Banisheikh da ke jihar Borno.

Bayanai sun nuna cewa mayaƙan sun auka wa sansanin cikin dare tare da buɗe wuta kan sojojin.

Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron Najeriya ta fitar, ta ce sojojin sun samu nasarar daƙile harin bayan da suka mayar da martani da cikin jajircewa da ƙwarewa da kuma ƙarfin makamai.

Tuni dai shugaban Najeriya ya aike da saƙon jaje ga iyalan sojojin da suka mutu sakamakon a harin.

Dalilan Boko Haram na kai wa kwamandojin soji hari

Ba wannan ne karon farko da mayaƙan suke kai hari kan sojoji tare da kashe shugabannin sojoji a hare-haren da suka kai musu.

A watan Maris da ya gabata ma akwai makon da hare-haren mayaƙan suka kashe kwamandojin soji uku a mako guda.

To ko me ya sa mayaƙan ke harin manyan kwamandojin soji?

Dr Audu Bulama Bukarti, ƙwararren lauya mai binciken ayyukan ƙungiyoyin ƴanbindiga a nahiyar Afirya ya ce akwai dalilan da ke haifar da hakan.

Jefa tsoro a zukatan ƙananan sojoji

Dalili na farko da ya sa mayaƙan Boko Haram ke kai wa manyan sojoji hare-hare shi ne domin jefa tsoro da fargaba a zukatan ƙananan sojojin da ke tare da manyan kwamandojin, kamar yadda Bukarti ya bayyana.

''Duk lokacin da aka kai hari aka kashe babban kwamanda ƙananan sojoji gwiwarsu za ta yi sanyi'', in ji shi.

Shi ma Group Captain Sadiq Garba mai ritaya, mai sharhi kan ala'muran tsaro a Najeriya, cewa a tsarin soji idan aka kashe kwamanda to an kashe uwar yaƙi kenan, kuma hakan na karya gwiwar sojojin da ke rundunarsa.

"Ai ba sojojin kaɗai ba, ko fararen hula idan suka ji labarin an kashe kwamanda to labarin yakan sare musu gwiwa'', in ji shi.

Ɗaukar hankalin kafofin yaɗa labarai

Dr Bukarti ya ce wani abu da ke sa mayaƙan Boko Haram kai wa manyan sojoji hare-hare shi ne neman ɗaukar hankalin kafofin yaɗa labarai.

''Idan ƙananan sojoji suka kashe ko da 100 ne, hakan ba zai ɗauki hankalin duniya ba kamar yadda za su kashe kwamanda soji guda ɗaya'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Neman karya gwiwar al'umma kan gwamnati

Wani dalilin kamar yadda Dr Bukarti ya bayyana shi ne neman karya gwiwar mutane a kan gwamnati.

''Gwamnati na cewa tana samun nasara a yaƙin da take yi da su, to idan suka kai hari suka kashe babban soja, jama'a za su ɗauka gwamnati a matsayin wadda ta gaza'', in ji shi.

Lamarin da ya ce zai sa mazauna ƙauyukan su sake tunani game da gwamnati.

Group Captain Sadiq Garba mai ritaya kuwa cewa ya yi labarin kisan kwamandan soji na matuƙar sare wa mutane gari gwiwa.

''Ga waɗanda suka san aikin soji, in aka ce an kashe kwamanda abin da za ka ɗauka to an kashe sojoji masu yawa, saboda a galibin yaƙin da ake yi kwamandan na baya, yana tsara sojoji'', in ji shi.

Sauya salon yaƙin ƙungiyar

Ƙwararren lauyan mai binciken ayyukan ƙungiyoyin ƴanbindigar ya ce ɗaya daga cikin dalilan shi ne sauya salon yaƙin ƙungiyar.

''A tsawon shekarun baya muna ɗaukar Boko haram a matsayin mai yaƙin sunƙuru ko yaƙin sari-ka-noƙe'', in ji Dr Bukarti.

Ƙwararren masanin tsaron ya ce amma yanzu fito-na-fito mayaƙan suke yi da sojojin a sansanin sojin.

''Kuma hakan na nuna maka irin yadda ƙungiyar ta ƙara ƙarfi sosai'', in ji shi.

Aƙidar ƙungiyar

Dr Bukarti ya ce abin da ya sa mayaƙan ke kai hare-haren kan manyan sojoji shi ne aƙidarsu.

''Dama a aƙidarsu suna yi wa ayoyin ƙur'ani fassarar son rai domin su dogara da su wajen kai wa manyan sojoji hare-hare'', in ji shi.

Me ya janyo ƙaruwar hare-hare kan sojoji?

A baya-bayan nan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na tsananta hare-hare musamman kan sojoji.

Wani abu da ke ci gaba da ɗaukar hankali masu sharhi kan al'amuran tsaro a ƙasar.

Ko a watan Maris da ya gabata ma an samu makon da mayaƙan suka kai hare-hare aƙalla biyar kan sansanonin soji da ke jihar Borno inda suka kashe wasu kwamandojin soji uku cikin mako guda a watan.

Dr Bukarti ya ce dalilan da suka janyo ƙaruwar hare-haren ƙungiyoyin na da yawa, amma wasu daga cikinsu sun haɗa da:

Nuna ƙarfin makamai

Ƙaruwar hare-haren alama ce da ke nuna cewa ƙungiyoyin na ci gaba da samun ƙarin makamai.

Dr Bukarti ya ce hakan na nuna cewa har yanzu ƙungiyoyin na ci gaba da samun manya-manyan makamai kamar yadda ake gani a lokacin ƙaddamar da hare-harensu.

A baya-bayan nan dai bayanai na nuna cewa ƙungiyar Boko Haram ta fara amfani da jirage marasa matuƙa wajen ƙaddamar da hare-haren.

Ci gaba da ɗaukar sabbin mayaƙa

Wani dalilin da ya janyo ƙaruwar hare-haren Boko Haram kan jami'an tsaro a baya-bayan nan shi ne yadda ƙungiyar ke ci gaba da ɗaukar sabbin mayaƙa a cewar Dr Bukarti.

''Sojojin Najeriya sun jima suna iƙirarin kashe ɗaruruwan mayaƙan Boko Haram da na ISWAP da gomman kwamandojin ƙungiyoyin, amma sai ka ga kamar ana da'awar maganin ƙaba, amma kai na ƙara kumbura'', in ji shi.

Bayanai sun nuna cewa ƙungiyoyin kan yi amfani da wa'azi da jan hankali da tayin kuɗi domin ɗaukar gomman mayaƙa.

Ƙarin ƙarfin ƙungiyar

Ƙwararren mai binciken kan ayyukan ƙungiyoyin ƴanbindigar ya ce ƙaruwar hare-haren ƙungiyar alama ce da ke nuna cewa har yanzu ƙungiyar na cin karenta babu babbaka a ƙasar.

''Domin idan ka kula duka waɗanan kashe-kashe da aka yi na manya-manyan sojojin a ƴan watannin nan za ka ga a sansanonin sojojin ko kwantan ɓauna aka yi su,'' in ji shi.

Dr Bukarti ya ce ƙalilan ne cikin hare-haren da aka samu sojojin ne suka kai wa mayaƙan a mafakarsu.

''Yanzu idan ka duba harin nan na Benisheikh, wannan fa babban gari ne da ba ƙauye ba, kuma yake kan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu, amma aka kai masa hari duk da kasancewarsa babban sansanin soji'', in ji shi.