Kane na shirin tsawaita zamansa a Munich, Liverpool na harin Scott

Harry Kane
Bayanan hoto, Harry Kane
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan Ingila Harry Kane, na dab da amincewa da sabon kwantaragi da Bayern Munich, inda ake sa ran za su kamala yarjejeniyar da zai kasance a ƙungiyar har kakar wasanni ta 2029. (Sky Sports)

Ɗan wasan Turkiya Arda Guler, ya amince da ci gaba da zama a Real Madrid, yayin da Arsenal da Manchester City ke harin ɗan wasan.(Teamtalk)

Kwantaragin Jacob Murphy da Newcastle United za ta ci gaba da kasancewa har zuwa kakar wasa mai zuwa, idan ɗan wasan ya ke dab da tsawaita zamansa da shekara guda. (Mail - subscription required)

Ƙungiyoyin Firimiya na ci gaba tuntunɓar Issa Doumbia, da ya koma Sporting daga Venezia a kakar wasa mai zuwa kan yuro miliyan 26, sannan ya na za su ajiye euro miliyan 80 idan ya amince da barin ƙungiyar kafin cikar wa'adinsa ba. (Tuttomercatoweb - in Italian)

Liverpool na kan gaba wajen ɗaukar ɗan wasan Bournemouth Alex Scott, inda aka sa masa kudi kan fam miliyan 100. (Mail - subscription required)

Ƙungiyoyin dake buga gasar Firimiya masu dama ne dai, ke c gaba da bibiyar Jacob Hodl a filin wasa na Vitality a ranar Alhamis , yayin da Sturm Graz ta buga wasa da Bournemouth. (Football Insider)

Har yanzu ɗan wasan Leeds United Lukas Nmecha, bai kai ga amincewa da sabuwar yarjejeniyar ba, yayin da ɗan ƙasar Jamus ɗin da kwantaraginsa ta ƙare a kakar wasan nan, ke son ƙarin lokacin bugawa ƙungiyar wasa. (Teamtalk)

Mai horar da ƴan wasan Wrexham Phil Parkinson na ci gaba da fuskantar ƙarin matsin lamba daga Liverpool, yayin da shi kuma tsohon kayftin ɗin ƙungiyar ke harin gurbin nasa, inda har aka sami gurbi. (Talksport)