Gwamnoni 7 da za su iya fuskantar ƙalubale a zaɓen 2027

- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa a Najeriya, hankalin 'yan siyasa da masu zaɓe na karkata zuwa kan wasu gwamnoni da ake ganin za su sha baƙar wuya ko ma su rasa mulki a zaɓen 2027 da ke tafe.
Masana na cewa rikicin cikin gida a jam'iyyu, da sauya sheƙa, da matsalar tsaro, da tsadar rayuwa da tasirin manyan 'yan siyasa na daga cikin abubuwan da za su iya haifar musu da matsala.
Sai dai ƙalubalen ba iri ɗaya ba ne ga kowane gwamna. Wasu na fuskantar matsin lamba daga abokan hamayyarsu, wasu kuma daga cikin jam'iyyunsu, yayin da wasu ke ke fuskantar kalubale kan matsin rayuwa da sauran wasu dalilai da za su iya kawo musu cikas a fatan na su.
Dangane da wannan batu ne BBC ta tattauna da Farfesa Isa Saidu, wani masanin siyasa, kuma malami a sashen nazarin siyasa na jami'ar Ahmadu Bello da ke garin Zaria.
1. Kano: Abba Kabir Yusuf
A cewar masanin, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na cikin gwamnonin da za su fi fuskantar manyan ƙalubale a ƙoƙarinsu na sake komawa kan kujerunsu.
Ya ce rabuwarsa da tsohon ubangidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ake kallon shi a matsayin jagoran siyasar jihar, na daga cikin manyan ƙalubalen da ke gabansa, duba da ƙarfin siyasa da tasirin Kwankwaso a Kano.
"Abba tsohon ɗan Kwankwasiyya ne, kuma a nan ya ci zaɓensa, a nan ya koyi siyasa. Ba shakka Allah ya ƙaddara zai zama gwamna, amma kowa ya san sanadiyyar Kwankwaso ne, kuma sun fi kowa sanin lagonsa. Don haka akwai jan aiki a gabansa matuƙar yana da aniyar sake komawa kan kujerarsa," in ji masanin.
Ya ƙara da cewa shi kansa rikicin masarautar Kano tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi II, da Sarki Aminu Ado Bayero na iya ƙara dagula masa lissafin siyasa.
"Abba na cikin tsaka mai wuya, irin abin da Hausawa ke cewa gaba kura, baya sayaki. Idan ya fi karkata ga Sarki Sanusi, magoya bayan Sarki Aminu Ado za su fusata. Idan kuwa ya fi karkata ga Aminu Ado, magoya bayan Sarki Sanusi za su fusata," in ji shi.
2. Kaduna: Uba Sani
A cewar masanin, babban ƙalubalen da Gwamna Uba Sani zai fuskanta shi ne ɓacin ran magoya bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.
Ya ce baya ga haka, mutane da dama a Kaduna na kokawa kan rashin gudanar da ayyukan raya ƙasa, ko da yake gwamnan ya sha danganta hakan da basussukan da gwamnatin jihar ta gada daga lokacin mulkin El-Rufai.
Ya ƙara da cewa tun da farko Uba Sani ya samu nasara ne da goyon bayan El-Rufai, wanda a yanzu ba ya tare da shi.
''Magoya bayan El-Rufai na kallon abubuwan da ke faruwa da shi, musamman gurfanar da shi a kotu da zarge-zargen da ake yi masa, kuma yawanci na nan a cike, za ka ji ma suna zargin cewa Gwamna Uba Sani ne ke da hannu a matsalolin da El-Rufai ke fuskanta'' a cewarsa.
Baya ga haka, ya ce 'yan adawa na da ɗan takara mai tasiri, Ashiru Kudan na jam'iyyar ADC, wanda a zaɓen da ya gabata na 2023 ma daƙyar gwamna mai cin ya kayar da shi.
3. Kebbi: Nasir Idris
A cewar Farfesa Saidu, ɗaya daga cikin ƙalubalen da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, zai fuskanta shi ne hamayya daga tsohon Ministan Shari'ar ƙasar Abubakar Malami, wanda ke neman kujerar gwamnan a ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
Ya ce Malami na da goyon bayan jama'a tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta yin takara a shekarar 2023, kuma yadda ake ta ƙwace kadarorinsa bisa zargin cin hanci da rashawa na iya sa mutane su ji tausayinsa.
Ya ƙara da cewa ''Idan aka yi la'akari da irin martanin da gwamnatin jihar ke mayar wa Malami, za a iya fahimtar cewa ita kanta gwamnatin na kallonsa a matsayin babban ƙalubale a zaɓen 2027''
Baya ga haka, a cewarsa, matsalar tsaro da satar mutane da ake samu a jihar, musamman sace ɗalibai, na iya taka rawa wajen kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnan na sake komawa kan mulki a zaɓen mai zuwa.
4. Zamfara: Dauda Lawan
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A jihar Zamfara kuwa, Farfesa Saidu ya ce matsalar tsaro na daga cikin manyan ƙalubalen da Gwamna Dauda Lawal zai fuskanta, domin a cewarsa, wannan matsala ce ta taimaka wajen kayar da tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, a zaɓen 2023 da ya gabata.
Ya ce ''Duk da yadda al'ummar jihar suka ƙi zaɓar APC a zaɓen gwamna na baya, Lawal, wanda ya lashe zaɓen a ƙarƙashin PDP, ya koma APC, lamarin da ya ce ya jawo ɓacin ran wasu daga cikin mutanen da suka zaɓe shi''
"Wannan ya fusata mutane da dama, domin jama'ar da nake magana da su suna shaida mini cewa sun san akwai APC, amma suka ƙi zaɓarta a zaɓen da ya wuce. Amma sai ga shi wanda suka zaɓa ya koma APC. Kenan, yana nufin su ba su san abin da ya fi dacewa su yi ba?" in ji shi.
Ya ce ko da yake babu shakka ƙarfin siyasar Lawal ya ƙaru bayan haɗewarsa da wasu manyan 'yan siyasar jihar da suka koma APC, ciki har da tsoffin gwamnoni biyu, sai dai irin hakan ta faru a lokacin da Gwamna Bello Matawalle ya bar PDP ya koma APC, amma duk da haka ya sha ƙasa a zaben 2023.
5. Taraba: Agbo Kefas
A cewar Farfesa Saidu, shima gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, zai fuskanci ƙalubalen siyasa sakamakon raba agri da mutumin da ake yi wa kallo Alu-Ja, a siyasar jihar, wato Janar Theophilus Yakubu Danjuma (mai ritaya)
Ya ce mutane da dama na mamakin matakin da gwamnan ya ɗauka na raba gari da tsohon ubangidan na sa , wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen mara masa baya a zaɓen gwamna na 2023, tare da komawa jam'iyyar APC.
"Mutane da yawa sun kasa fahimtar hikimar raba gari da ya yi da shi har ya koma APC. Ba shakka, wannan na iya shafar alaƙarsa da wasu daga cikin mutanen da suka mara masa baya a baya," in ji masanin.
Ya kara da baya ga hakan mutane da dama na kokawa kan rashin gudanar da ayyukan more rayuwa a jihar, yayin da suke gani a makota.
6. Benue: Hyacinth Alia
A cewar mai sharhi kan harkokin siyasar, Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ma na fuskantar irin na sa ƙalubalen siyasa a zaɓen 2027, musamman sakamakon takun-sakar da ke tsakaninsa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
Sun ce rashin jituwar da ke tsakanin manyan jiga-jigan APC a jihar na iya raba kan jam'iyyar, tare da shafar ƙoƙarin gwamnan na sake samun goyon bayan magoya baya.
"Babban ƙalubalen Alia shi ne yadda zai shawo kan rikicin cikin jam'iyyarsa, ganin irin tasirin da Akume ke da shi a siyasar Benue," in ji wani mai sharhi.
Baya ga rikicin jam'iyya, matsalar tsaro da hare-haren da ke ci gaba da shafar wasu yankunan jihar na iya zama muhimmin batu ga masu zaɓe wajen tantance ayyukan gwamnatin Alia.
7. Delta: Sheriff Oborevwori
Ya ci gaba da cewa shi kansa gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori sai ya yi da gaske, duba da irin rikicin cikin gidan da ke tsakanin mutanensa da wasu ƴaƴan jam'iiar da ya tarar, wadanda wasunsu ma tuni sun fice.
Ya ce babban ƙalubalen da ke gabansa shine na abokin hamayyarsa Sanata Ovie Omo-Agege, tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawan ƙasar, wanda ya fice daga APC zuwa jam'iyyar NDC bayan rashin jituwa kan kujerar Sanatan Delta ta Tsakiya. Wannan rikici na iya ƙara dagula lissafin siyasa a yankin Delta ta Tsakiya, musamman idan ɓangarorin biyu suka yi amfani da magoya bayansu wajen fafatawa a zaɓen 2027.
Baya ga haka, a cewarsa mutane da dama a jihar na kokawa kan matsin tattalin arziki, da rashin aikin yi da rashin ayyukan raya ƙasa.





























