Me korar da ADC ta yi wa Nafi'u Bala ke nufi?

Lokacin karatu: Minti 4

Jam'iyyar ADC mai adawa ta sanar da korar tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar wanda ke ikrarin shi ne halastaccen shugabanta, Nafi'u Bala Gombe tare da wasu ƴan jam'iyyar da ke kiran kansu jagororin jam'iyyar

A ƙarshen babban taronta da ta gudanar ranar Talata a Abuja, ADC ta ce ta kori mutanen ne bisa ayyukansu yin zagon ƙasa domin wargaza jam'iyya.

Tun bayan da hukumar INEC ta sanar da cire sunan Sanata David Mark da Rauf Aregbesola daga na'urarta a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar ADC.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba ta 1 ga watan Afrilun 2026, Inec ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon umurnin kotu kan shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi'u Gombe.

Kuma tun bayan lokacin ne Nafi'u Bala Gombe ya yi ikrarin cewa shi ne shugaban jam'iyyar.

Tambayar da ƴan Najeriya ke yi ita ce ko me korar take nufi? BBC ta tuntuɓi lauyoyi guda biyu da suka haɗa da Barista Bulama Bukarti da kuma Barista Abba Hikima domin jin ra'ayoyi mabanbanta.

Ra'ayin Bulama Bukarti

Barista Bulama Bukarti wanda ne mai zaman kansa a Birtaniya ya shaida wa BBC cewa duk da cewa al'amarin jam'iyyar ADC yana da sarƙaƙiyar gaske amma a ganinsa wannan kora ba ta koru ba.

"Wannan da'awa gaskiya ba za ta tabbata ba kuma akwai naƙasu a cikinta har sai kotu ta tabbatar da wane ɓangare ne yake da gaskiya a wannan rikicin na shugabanci. Saboda haka duk wata da'awa da ɓangaren David Mark ya yi cewa ya kori su Nafi'u ko kuma su Nafi'u su ce sun kori ɓangaren David Mark abune wanda zai zama na siyasa amma a dokance ba zai tabbata ba," in ji Bukarti.

Barista Bukarti ya kuma ƙara da cewa ko da kotu ta tabbatar da shugaba halastacce to ba haka kawai ake korar mutum daga jam'iyya ba.

"Kundin tsarin mulkin kowace jam'iyya na zayyana matakan da sai an bi kafin a kori mutum daga jam'iyyar saboda idan ba haka ba kowa zai wayi gari ya kori duk mutumin da ba ya son sa," in ji barista.

Masanin shari'ar ya ƙara da cewa shari'ar da ke gaban kotun ɗaukaka ƙara dangane da shugabancin jam'iyyar shi ma babban dalili ne da ke nuna cewa korar da aka yi wa Nafi'u Gombe ba ta yiwu ba.

"Kotun ɗaukaka ta ce ya tsaya a inda yake. Kuma ko da hakan na nufin a tsaya daga inda David Mark ya zama shugaba ko kuma daga inda shi Nafi'u ke cewa ya zama shugaba kowanne ka ɗauka a ciki. Kuma kotun ta yi gargaɗin cewa ka da wanda ya yi wani abun da zai ɓata mata shari'a....to idan ka zo ka fara korar mutune ko ma ka yi taron jam'iyya to hakan ya yi karo da umarnin kotun ƙolin," in ji barista.

Ra'ayin Abba Hikima

Shi kuwa Barista Abba Hikima wanda shi ma lauya ne mai zaman kansa a birnin Kano, Najeriya ya ce shi yana da ra'ayi daban inda yake ganin korar da ADC ta yi wa Nafi'u Bala.

"Shi babban taron jam'iyya shi ne babban gangamin jam'iyya da ya fi kowane ƙarfi wanda a nan ne yanke duk abin da ya kamata. A nan ne ma za a iya sauya kundin jam'iyya. Saboda haka duk abin da aka yanke a wannan taron to ya tabbata kuma ya fi ƙarfin kowa," in ji Abba Hikima.

Sai dai kuma Barista Abba Hikima ya bayar da wani hanzari inda ya ce idan dai har babban taron jam'iyyar halastacce ne ko hukunci ya tabbata.

"Sai dai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba. Hanzarin shi ne ban gama tantance abin da ke gaban kotu ba. Idan abin da ke gaban kotu ya shafi babban taron misali kamar a ce kotun ta hana yin sa amma suka yi to wannan zai samar da tasgaro ga duk abin da aka yanke a wurin taron. To amma idan babu wannan to duk abin da aka yanke a babban taron ya tabbata." A kalaman Abba Hikima.

Martanin Nafi'u Bala

Nafi'u Bala Gombe wanda shi ne mutumin da ake taƙaddama a kansa bisa ikrarin kasancewa shugaban jam'iyyar ADC ya ce har yanzu shi ne halastaccen shugaba kasancewar sun saɓa umarnin kotu.

"Sun karya umarnin kotu saboda kotu ta yi umarnin a tsaya a inda ake domin haka wannan korar haramtacciya ce. Kuma mu ba za mu yi babban taro ba har sai mun jira hukuncin kotu. Muna tabbatarwa da jama'a cewa komi zai lafa insha Allah," in ji Nafi'u Gombe.

Nafi'u Bala ya kuma ƙara da cewa shi a wurinsa mutanen da suke bayyana kansu a matsayin shugabannnin jam'iyyar ta ADC ba ma ƴan jam'iyyar tasu ba ne.

"Yaya za a yi agola ya kori ɗan gida? Kun taɓa jin inda aka yi hakan. Mu gama ɗayansu ba mu san su a jam'iyyar ADC ba tunda babu wanda ya yi rijista. Saboda haka ba ƴan jam'iyyarmu ba ne," in ji Nafi'u Bala.