Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa gwamnan Kano ke jan ƙafa kan naɗin mataimakinsa?
Duk da cewa batun sauya sheƙar wasu manyan ƴan siyasar Kano zuwa jam'iyyar ADC shi ne abin da ke tashe a yanzu, amma wani abu da ke ta yawo a zukatan al'ummar jihar shi ne batun mataimakin gwamna da babu shi.
Yanzu an kwashe kusan mako uku tun bayan da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam ya sauka daga muƙaminsa bayan rikicin siyasa da ya turnuƙe sanadiyyar sauya sheƙar gwamnan jihar zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Tun bayan saukar tasa ne ake ci gaba da hasashen wanda zai maye gurbinsa.
Aminu Abdussalam ya sauka daga muƙaminsa ne lokacin da gwamnan ke halartar babban taron jam'iyyar APC na ƙasa da aka gudanara a Abuja a ƙarshen watan da ya gabata.
Sai dai siyasar jihar ta ƙara ɗaukar zafi ne tun bayan komawar Gwamna Abba, inda ake sa ran zai sanar da magajin nasa, amma har yanzu shiru.
Ƴan tsohuwar APC sun miƙa wa Gwamna sunayen mutum uku
A ƙarshen mako ne jiga-jigan jam'iyyar APCn jihar suka yi wani zama na musamman da rahotonni suka ce sun tattauna batun mataimakin gwamnan.
A lokacin zaman ƴan tsohuwar APC sun miƙa wa gwamnan sunayen wasu mutum uku da a ciki suka ce ya zaɓi mataimakin nasa.
Ɓangarorin da suka yi zaman sun haɗa da na tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da ɓangaren Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril da kuma ɓangaren su Kawu Sumaila.
Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC na jihar ne ciki har da Gwamna Abba Kabir Yusuf ne suka halarci zaman.
A ƙarshen taron, masu ruwa da tsakin sun gabatar da sunayen Murtala Sule Garo daga ɓangaren Ganduje da Rabi'u Suleiman Bichi daga ɓangaren Sanata Barau, sai kuma Kabiru Alhassan Rurum daga ɓangaren su Kawu Sumaila ƴan Kano ta Kudu.
A baya-bayan nan an jiyo Hon. Al'assan Ado Doguwa na shawartar gwamnan kan zaɓen mataimakin nasa.
Cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga Hon. Doguwa na magana da maoiya bayansa, inda yake nuna dacewar Murtala Sule Garo a kan kujerar mataimakin gwamnan.
Me ya sa kujerar ke ɗaukar hankali?
Farfesa Kamilu Sani Fagge, Malami a Jami'ar Bayero da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya ya ce a tsarin dokokin Najeriya, gwamna ne ke da ikon zaɓen wanda yake son ya zama mataimakinsa.
Malamin jami'ar ya ce siyasar Kano gida-gida ce, kowa da ɓangarensa, kuma kowa na son samun kujerar don ƙarfafa gidansa a siyasance.
''Kowane gida na da burin samun kujerar domin ƙarfafa kansa da kuma shirin 2031 idan Abba ya gama wa'adinsa'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ce Gwamnan zai so ya ɗauka daga yaransa, wanda za su yi aiki tare saboda gudun saɓani idan tafiya ta fara nisa.
''Su ma tsofaffin ƴan APC kamar gidan GAnduje da gidan Barau, suma kowannensu na lissafin samun kujerar saboda 2031, ga kuma ɓangaren Kano ta Kudu da suke ta ƙorafin rashin yin Gwamna ko mataimaki a jihar'', in ji shi.
Me ya janyo jinkirin
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce abubuwan da ke janyo jinkirin ba zai rasa nasaba ta taka-tsantsan da gwamnan ke yi don gudun haifar da matsala a siyasar jihar.
''Shi akwai wanda yake so, sannan ga waɗanda ya tarar a APC su ma nasu zaɓin, don haka dole ya yi taka-tsantsan'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ce idan gwamnan bai yi taka-tsantsan ba, zai iya fuskantar matsala a zaɓen 2027 da ke tafe.
''Domin kuwa yana fargabar cewa kowane gida, zai iya yi masa zagon ƙasa, idan ya ɓata masa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ƙalubalen da ke gaban Abba
Wani abu da ke ɗaukar hankalin masu nazarin siyasar shi ne ɓangaren da gwamnan zai ɗauka tsakanin ƴan tsohuwar APC da kuma ƴan komen.
Yayin da ƴan tsohuwar APCn ke ganin dacewar ɗaukar mataimakin gwamnan daga ɓangarensu, akwai kuma hasashen da ake yi cewa Gwamnan Abba zai ɗauki mataimakin nasa ne daga cikin waɗanda suka bi shi APC daga NNPP.
Dr Kabiru Sufi, Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya ya ce idan gwamnan na son tafiya da ƴan jam'iyyar APC da ya tarar zai fi kyau ya ba su dama kamar yadda ya kamata.
''Hakan ne kaɗai zai ba su damar bayar da haɗin kai cikakke a tafiyar'', in ji masanin siyasar.
Me ya kamata gwamnan ya yi?
Farfesa Kamilu ya ce abin da ya kamata gwamnan ya yi shi ne ya yi amfani da hanyar dipplomasiyya wajen magance matsalar.
''Ya zauna da kowane ɓangare ya haƙurƙurta da su, kowa dai ya sani kujerar nan guda ɗaya ce don haka mutum ɗaya ne zai samu'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa akwai muƙamai na kwamishinonin da suka ajiye aiki da shugabannin ma'aikatu, don haka yana da kyau gwamnan ya yi wa sauran ɓangarorin da ba su samu muƙamin mataimakin gwamnan alƙawuran wasu muƙaman kwamishinoni da shugannin ma'aikatu.