Fitattun ƴan siyasar Najeriya 9 da ba su taɓa sauya sheƙa ba

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Za a iya cewa sauya sheƙar jam'iyyar siyasa abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya.

Tun dai bayan dawowar dimokraɗiya a shekarar 1999 ake samun yanayin da mutane ke fita daga wata jam'iyya su koma wata, musamman tsakanin manyan jam'iyyun ƙasar PDP da kuma uku wadanda suka hade wato ANPP, ACN da CPC da kuma wani bangare na PDP suka zama APC.

Al'amarin sauya sheƙar ya ƙara ƙamari tun bayan zaɓen 2023 inda ƴan siyasa jam'iyyar PDP da APC suka rinƙa ficewa suna komawa jam'iyyu irin su LP da ADC da NDC da PRP ma sauran jam'iyyu.

To amma duk da haka, akwai wasu manyan 'yan siyasa da ba su taɓa sauya sheƙa ba tun 1999 har zuwa yanzu kuma BBC ta zaƙulo su.

Bola Tinubu

Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya a 2023

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban Najeriya mai ci kuma fitaccen ɗan siyasa ba wai kawai a jiharsa ta Legas kawai ba har a Najeriya baki ɗaya.

Da shi aka kafa jam'iyyar AD a shekarar 1998, bayan dawowar dimokradiya.

Ya yi gwamnan jihar Legas sau biyu a jere daga 1999 zuwa 2007.

Daga baya jam'iyyarsa ta hade da gamayyar jam'iyyun siyasa uku na kasar, inda suka samar da jam'iyar APC.

Bola Tinubu ya zamo shugaban Najeriya a 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Goodluck Jonathan

Goodluck Jonathan ya kasance shugaban Najeriya daga 2010 zuwa 2015.

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shi ma bai taba fita daga jam'iyyarsa ta PDP ba, tun daga lokacin da ya kasance mataimakin gwamnan jihar Bayelsa da mataimakin shugaban ƙasar da kuma yanzu da yake tsohon shugaban ƙasa.

Goodluck Jonathan ya yi shugabancin Najeriya daga 2010 zuwa 2015 lokacin da marigayi Muhammadu Buhari ya kayar da shi.

Kafin nan Goodluck Jonathan ya kasance mataimakin shugaban ƙasa Umar Musa Ƴar'adu'a daga 2007 zuwa 2010 inda aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa bayan mutuwar Ƴar'adu'a.

Jonathan ya yi gwamnan jihar Bayelsa daga 2005 zuwa 2007 sannan kuma ya yi mataimakin gwamnan jihar daga 1999 zuwa 2005.

Kashim Shettima

Kashim Shettima ne mataimakin shugaban Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Mataimakin shugaban Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima shi ma yana cikin sawun manyan 'yan siyasar da ba su taɓa sauya sheƙa ba.

Ya yi jam'iyyar ANPP kuma ya koma APC lokacin da jam'iyyarsa ta haɗe da wasu jam'iyyu gabanin babban zaɓen shekarar 2015.

Nyesom Wike

Barista Nyesom Wike ɗan jam'iyyar PDP da ke aiki a matsayin minista a jam'iyya mai mulki ta APC.

Asalin hoton, Getty Images

Barista Nyesom Wike wanda shi ne ministan babban birnin tarayyar Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Rivers bai taɓa sauya sheƙa ba zuwa wata jam'iyyar bayan PDP.

Wike ya yi shugaban ƙaramar hukumar Obio Akpor har karo biyu daga shekarar 1999 zuwa 2007.

A 2011 ne tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya naɗa shi ƙaramin ministan ilimi, kafin daga bisani ya zama ministan ilimin bayan da aka sauke Farfesa Ruqayya Ahmed.

A 2015 ne kuma Wike ya samu nasarar zama gwamnan jihar ta Rivers bayan ya kayar da abokin takararsa na APC, Dakuku Peter Side. Wike ya yi takarar neman shugabancin Najeriya a zaɓen cikin gida na jam'iyyar PDP a 2022, inda kuma Atiku Abubakar ya kayar da shi.

A 2023 ne Bola Tinubu ya nada shi a matsayin ministan Abuja duk kuwa da yana jam'iyyar PDP. Kuma tun lokacin Wike ya zamar wa jam'iyyar ta PDP "ƙadangaren bakin tulu", da ya sa wasu ƴan jam'iyyar suka gwammace ya fice ya ba su wuri.

Sule Lamiɗo

..

Asalin hoton, Getty Images

Alhaji Sule Lamiɗo ya fara siyasa a jam'iyyar PRP. Ya wakilci mazaɓar Birnin Kudu a majalisar wakilai ta Najeriya daga 1979 zuwa 1983.

Yana daga cikin na gaba-gaba da suka kafa jam'iyyar PDP a shekarar 1998, kuma ya yi ministan harkokin waje daga 1999 zuwa 2003 lokacin mulkin Obasanjo.

Alhaji Sule Lamiɗo ya yi gwamnan jihar Jigawa sau biyu a jere daga 2007 zuwa 2015. Har yanzu shi ne jagoran PDP a jiharsa, kuma bai taɓa barin wannan jam'iyya ya koma wata ba.

Sai dai a baya-bayan nan an gan shi a wani taron kafa sabuwar jam'iyyar haɗaka ta ADC, wani abu da wasu masu fashin baƙi suka ce tamkar sansanar sauya sheƙa ne.

Ahmed Makarfi

Ahmed Maƙarfi

Asalin hoton, Maƙarfi

Shi ma ya shiga jam'iyyar PDP ne tun a shekarar 1998. Ya zama gwamnan jihar Kaduna daga 1999 zuwa 2007 karkashin PDP.

Bayan nan kuma sai ya zama sanata a shekarar 2007.

Ibrahim Geidam

..

Asalin hoton, YobeGovernment House

Tsohon gwamnan jihar Yobe kuma tsohon ministan ƴansanda na Najeriya, Ibrahim Geidam shi ma yana cikin sawun manyan 'yan siyasar da ba su taba sauya sheka ba.

Sai dai kamar takwaransa na Borno, ya taba yin jam'iyyar ANPP kafin ya koma APC, lokacin da jam'iyyarsa ta haɗe da wasu jam'iyyu gabanin babban zaɓen shekarar 2015.

Ahmad Sani Yariman Bakura

Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya kasance gwamnan farko a jihar Zamfara tun bayan komawar Najeriya turbar dimokraɗiyya a 1999.

Kuma tun lokacin bai taɓa sauya sheƙa ba illa dai kamar sauran takwarorinsa na jam'iyyar ANPP ya koma jam'iyyar haɗaka ta APC a 2014.

Duk da saɓata-juyatar siyasa a jiharsa ta Zamfara, yarima bai taɓa nuna alamun komawa wata jam'iyya ba.

Abdul Ningi

..

Asalin hoton, Ningi/X

Abdul Ahmed Ningi fitaccen dan siyasa ne a jihar Bauchi. Ya shiga jam'iyyar PDP tun shekarar 1998.

Tun a 1999 ya shiga majalisar wakilan Najeriya har zuwa 2011. Daga bisani ya zama sanata a 2011 zuwa 2015.

A zaben 2015 ne ya yi rashin nasara, amma duk da haka bai fice daga jam'iyyar ba.

Sai dai kuma ya sake samun nasarar komawa majalisar dattawa a 2023.