Ko Firaministan India zai iya zuwa Iran domin jana'izar Ali Khamenei?

Asalin hoton, Getty Images
Za a gudanar da jana'izar tsohon jagoran addinin Iran marigayi Ali Khamenei da aka kashe a hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai ƙasar a tsakiyan watan Yuli, inda ake sa ran hakartar wasu shugabannin ƙasashe.
Shugaban Pakistan Asif Ali Zardari da Firaminsita Shahbaz Sharif sun tabbatar da cewa jami'an ƙasar za su halarci taron jana'izar. Haka kuma wasu kafofin yaɗa labaran India sun ruwaito cewa Iran ta gayyaci Narendra Modi zuwa jana'izar Ali Khamenei.
Har yanzu Iran ba ta tabbatar da a hukumance cewa ta gayyaci wasu shugabannin ƙasashe ba. Hukumomi a Tehran sun ce ana ci gaba da shirye-shirya, inda ake sa ran kusan mutum miliyan 10 zuwa 15 su halarci jana'izar da za a gudanar a babban birnin ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran India, ciki har da Press Trust, mallakin kamfanin dillancin labarai na ƙasar da kuma jarida The Hindu sun ambato majiyoyi daga jakadun ƙasar na shaida musu cewa Iran ta gayyaci Narendra Modi.
Bayan fitar waɗannan labaran, ana ta muhawara kan ko Modi zai je Iran ko a'a.
Sai dai ita ma gwamnatin India ba ta tabbatar ko musanta samun gayyatar zuwa taron jana'izar daga Iran ba.
Modi bai ce uffan kan kisan Khamenei ba

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan India Narendra Modi ya ziyarci Isra'ila kwanaki biyu kafin Isra'ila da Amurka su ƙaddamar da hari kan Iran, kuma gwamnatin India ba ta yi alawadai da kisan da aka yi wa Ali Khamenei ba a harin na ranar 28 ga watan Fabrairu.
Babbar jam'iyyar adawa ta Congress a India, ta caccaki jam'iyya mai mulki ta Bharatiya Janata kan hakan.
Kakakin jam'iyyar Congress Pawan Khera ya bayyana cewa jam'iyyarsu tana alawadai da abin da ya kira "kunnen uwar shegu" da Firamisnita Modi ya yi kan yaƙin Iran da kuma kisan Ayatollah Khamenei.
Ya kuma ce ofishin jakadancin Iran ba shi da nisa da ofishin Firaministan, amma kuma Mr. Modi ya ƙi zuwa ko don ya yi musu ta'aziyya.
Gwamnatin India ba ta maida martani kan wannan suka a hukumance ba, amma Ministanharkokin waje na India Subrahmanyam Jaishankar ya shaida wa mambobin majalisar cewa "India na son zaman lafiya" kuma Narendra Modi ya tattauna da Donald Trump, inda ya buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin ba tare da ɓata lokaci ba, saboda ci gaba da yaƙin zai shafi tattalin arzikin duniya."
Shin Modi zai je jana'izar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sakamakon abubuwan da suka faru, wasu masu sharhi a India na ganin Narendra Modi ba zai halarci jana'izar tsohon jagoran Iran ɗin ba, yayin da wasu ke ganin ya kamata ya je Tehran.
India dai ta yi maraba da tsagaita wutar da aka yi tsakanin Iran da Amurka, amma kuma a lokacin da ake rikicin, wasu masu sharhi sun ce take-taken da ta nuna sun bayyana cewa ba ta ɗauki wani tsagi ba.
Wani mai sharhi a India Pravin Sawhney ya wallafa a shafinsa na X cewa: "Ko da Firaminista Modi ya je jana'izar Khamenei ko bai je ba, tsohon jagoran Iran ɗin babbar jarabawa ce ga India, kuma za a ci gaba da nazari a kan shi."
Ya ƙara da cewa: "Ina da tabbacin cewa Modi ba zai halarci taron jana'izar ba; Amma zan so a ce hakan bai faru ba, saboda ba lallai India ta nuna cewa tsare-tsarenta ba su kan daidai ba."
Wasu masu sharhi sun bayyana wannan lamarin a matsayi wata jarabawa ga tsare-tsaren diflomasiyyar India.
Dr. Brahma Chellani ya wallafa a shafin X-Net cewa wannan lamari "ya jefa yanayin diflomasiyyar India cikin wani yanayi."
"A gefe guda kuma, yin shiru da India ta yi bayan hare-haren Isra'ila da Amurka a watan Fabrairu ya sa ƙasar a tsaka mai wuya. Idan kuma ya halarci jana'izar, akwai yiwuwar Washington da Tel Aviv ba za su ji daɗin hakan ba," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Ba iya masu sharhi ne ke matsa lamba gwamnatin Narendra Modi ta halarci jana'izar Khamenei ba, har da manyan ƴan siyasa a India na ganin cewa ya kamata ƙasar ta nuna wakilcinta a Tehran.
Ɗanmajalisar India Asaduddin Owaisi ya shaida wa ƴan jarida cewa: "Ya kamata Firaministan ya halarci jana'izar Khamenei."
Firaministan ya je Isra'ila ya ce yana tare da ita; saboda haka yanzu ma ya zama waajibi ya je Iran," in ji shi.
Mr. Owaisi ya ƙara da cewa: "Matakan mu na alaƙar ƙasa da ƙasa su ne hulɗa da dukkan ƙasashe da kuma ci gaban ƙasarmu."
Gwamnatin India ba ta ce uffan kan batun ba. Sai dai yayin da aka tambayi kakakin Shiv Sena, wani ƙusa a gwamnati ya ce: "Ko India ta je Iran ko ba ta je ba, wannan hukunci ne da Firaminista zai yanke. Shi ne ke da wannan hurumin kuma ba za mu yi magana a kai ba."
"Damar inganta alaƙa da Iran"
Wasu masu sharhi na ganin zuwan Firaministan taron jana'izar Ali Khamenei, wata babbar dama ce da za ta inganta alaƙa tsakanin India da Iran.
"Pakistan na ƙoƙarin maida kanta babbar jagora a tsakanin ƙasashen musulmi bayan rawar da ta taka waje samar da zaman lafiya a baya-bayan nan," in ji wani mawallafi Saba Naqvi.
"A baya Iran na da kyakkyawar alaƙa da India. Amma wannan alaƙa ta lalace saboda kusancinmu da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu," in ji shi.
Naqvi ya shawarci gwamnatin India ta zauna cikin shiri cewa da zarar aka janye takunkuman tattalin arziki kan Iran, "akwai yiwuwar India ta samu damarmaki na kasuwanci a jin ƙai a Iran".
Shi ma Dr. Brahma Chellani na da irin wannan ra'ayin.
Ya rubuta cewa tura babban jami'i zuwa jana'izar Ali Khamenei "zai nuna cewa India ba ta sauya alƙiblarta kan manufar diflomasiyya da kuma alaƙa da Amurka da Isra'ila, musamman saboda India ta zuba jari sosai a mashigar ruwa ta Chabahar."
Iran ta sanar da cewa za a gudanar da taron na kwanaki domin jana'izar tsohon shugaban nata.
Kakakin gwamnatin Fatemeh Mohajerani ya sanar da cewa an ba da hutu a birnin Tehran a ranakun 4 da 5 ga watan Yuli, kuma za a yi hutu a faɗin ƙasar a ranar 6 ga watan Yuli saboda a ba mutane daga sassa daban-daban damar halartar jana'izar.
Za a gudanar da taron bankwana a Tehran a ranar 4 da 5 ga watan Yuli. Sai kuma a gudanar da janaiza a Tehran da Qom a saura ranakun.
Za a binne Ali Khamenei ne a ranar 8 ga watan Yuli a hubbaren babban malamin Shi'a na takwas a Mashhad.












