Me ya sa girgizar ƙasar Venezuela ta yi muni?
- Marubuci, Tom McArthur
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Kimanin mutum 1,500 ake tunanin sun mutu yayin da wasu 3,360 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa a Venezuela, a cewar gwamnati, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da neman waɗanda suka tsira da rayukansu, iyalai kuma suna jiran tsammani.
Waɗanda suka jikkata na samun kulawa ne a wasu asibitoci na wucin-gadi, bayan da gine-gine da dama da ke yankin arewaci da kuma a Caracas babban birnin ƙasar suka ruguje sakamakon girgizar ƙasa guda biyu da suka faru.
Jami'in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya ce kusan ma'aikatan ceto na ƙasa da ƙasa 2,000 na gudanar da gagagrumin shirin kai ɗauki .
Girgizar ƙasa biyu masu ƙarfi sun auku a Venezuela cikin ƙanƙanin lokaci a ranar Laraba. Girgizar ƙasa ta biyu ta kasance ɗaya daga cikin girgizar ƙasa mafi ƙarfi da aka taɓa samu a ƙasar cikin ƙarni guda, inda take da ƙarfin maki 7.5.
Hukumomin ƙasar sun ce yankin La Guaira da ke arewacin babban birnin ƙasar ya fi fama da matsalar. A Jihar ne kuma ake da ɗaya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa biyu na ƙasar da filin jirgin sama na Simón Bolívar a Maiquetía - wanda shi ne babban filin jirgin saman ƙasar.
Mutane da dama sun ɓace, kuma akwai yiwuwar adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
A La Guaira, Natacha Diaz ta shaida wa BBC cewa ƴaƴanta mata biyu - masu shekaru 22 da 23 - sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan wata cibiyar kasuwanci da ta ruguje, inda suke aiki a matsayin masu gyaran farce.
"Sun kasance tare da abokansu," in ji ta. "Ina son a nemo su, na yi amanna cewa suna can" a lokacin da girgizar ƙasar ta faru.
"Ina son su dawo gare ni, su ne kaɗai abin da nake da su a rayuwar nan."
A ranar Asabar, jami'in Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya shaida shirin BBC radio cewa tawagogin ma'akatan ceto sun nufi yakunan da bala'in ya auka wa, saboda sa'o'i 72 na farko bayan girgizar ƙasar suna da "matuƙar muhimmanci".
"Abin takaici ne, yana da ban tsoro kuma a gare mu muna aiki ne babu ƙaƙƙautawa yayin da mu ke jin kururuwar waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine."
"Ba za mu iya tsayawa ba ko da na daƙiƙa ɗaya yayin da muke jin su, amma mafi tayar da hankali shi ne lokacin da waɗannan muryoyin suka yi shiru. Mun ƙudiri aniyar ceton rayuka da yawa gwargwadon iko."

Ɗaruruwan gine-gine da suka haɗa da asibitoci da cibiyoyin kasuwanci da dama sun ruguje, in ji Jorge Rodríguez, inda ya ƙara da cewa aƙalla wasu wuraren samar da ababen more rayuwa 1,000 kuma sun lalace.
An ce cibiyoyin jinya da suka tsira sun cika maƙil, inda likitocin suka shaida wa BBC cewa tun kafin bala'in marasa lafiya na shan wahala wurin samun magani.
"Duk asibitocinmu ba su da kayan aiki, ba su da magani, ana zaune lafiya ma, ba ma iya kula da lafiyar mutanenmu," in ji likita Pedro Javier Fernandez.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai rahotannin cewa masu aikin ceto na ammfani da hannunsu wurin zaƙulo mutane daga ƙarƙashin gine-ginen da suka ruguje, saboda katsewar hanyoyin sadarwa, da lalacewar tituna, da kuma ƙarancin kayan aiki, sun sa ɗaukar matakan gaggawa ya yi matuƙar wahala.
Fletcher ya ce Majalisar Dinkin Duniya na da tawagogin bincike da ceto guda 39 da aka tura, kowannen su ya ƙunshi mutane 50-100.
"Muna da kusan mutane 2000 da ke tawagar, akwai karnuka 111, har ma tawagogin likitoci. Muna shiga da waɗannan ƙananan jirage marasa matuƙa, da ake kiransu 'cockroach drones', waɗanda ke taimaka mana wurin nemo mutanen da suka maƙale a cikin gine-gine."
Jirgin sojojin Burtaniya ɗauke da ƙungiyoyin bincike da ceto na Birtaniyya da karnuka da jirage marasa matuƙa ya tafi ƙasar ta Venezuela domin kai ɗauki.
Jirgin na ɗauke da ƙwararru daga ma'aikatun kashe gobara 14 na Burtaniya, ƙarƙashin jagorancin 'Merseyside Fire and Rescue'.
Sauran ƙasashe da suka haɗa da Amurka da Netherlands da Mexico da Switzerland sun aike da nasu tawagogin. Amurka ta kuma sanar da tura jiragen ruwan yaƙi da jiragen sama na jigilar kaya da kuma dala miliyan 150 (£113m) a matsayin agaji.
Wani wakilin BBC a yankin Caraballeda, da ke jihar La Guaira, ya ga manyan injuna sun iso domin fara aikin kawar da ɓaraguzan gine-gine.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatan ceto na ƙasa da ƙasa sun fuskanci abin da suka bayyana a matsayin "lalacewa mai ban tsoro", in ji babban sakatare na Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway.
Ƙasar Venezuela ba ta shirya wa zuwan wannan bala'i ba kuma tana cikin mawuyacin hali wurin kai ɗaukin gaggawa saboda "kayan aikinta na da matuƙar rauni" bayan shekaru da dama na rashin saka hannun jari, Jan Egeland ya shaida wa BBC.
Ƙasar Venezuela ta kwashe sama da shekara 10 tana fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki, lamarin da ya janyo taɓarɓarewar yanayin rayuwa a ƙasar mai arzikin man fetur.
Tun da farko, babban jami'in jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya ce bala'in "yana buƙatar muhimman matakai na kasa da kasa kuma za mu haɗa kai kuma za mu tabbatar da an yi nasara".
"Ina son mutanen Venezuela su san cewa taimako na zuwa," in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
Wani lamari da ya ƙara wa mutane a duk faɗin ƙasar ƙwarin gwiwa shi ne ceto wasu matasa ƴan uwa su uku da aka yi a La Guaira, waɗanda aka zaƙulo su daga ɓaraguza, sun yi butu-butu da ƙura da tarkace, kamar yadda bidiyon da aka watsa a gidan talabijin na kasar ya nuna.
"Zo nan, yarona, zo nan," wani mutum ya ce wa yaron na farko yayin da yake fitowa da rai daga ƙarƙashin ɓaraguzan.
Sai wata yarinya ta fito, yayin da mutumin ya tambaye ta: "Ku ƴan'uwa ne?", sai ta amsa: "E, mu uku ne."
Ba da daɗewa ba, ƴar'uwar ta uku ta fito, tana kuka yayin da ƙura ya lulluɓe ta daga kai har zuwa ƙafa.
Wannan bala'i ya afku ne a daidai lokacin da ake fama da rashin tabbas a Venezuela.
Ƙasar da wata shida da suka gabata ne sojojin Amurka suka kama Nicolás Maduro, shugaban da ke mulkin ƙasar tun a shekara ta 2013, a birnin Caracas, kafin daga bisani a tafi da shi birnin New York domin fuskantar tuhumar safarar miyagun ƙwayoyi.
Abokiyar Maduro kuma tsohowar mataimakiya shugaban ƙasa, Delcy Rodríguez, ta karɓi ragamar tafiyar da ƙasar, abin da ya fusata magoya bayan ƴan adawa da suka yi fatan gwamnatin Trump za ta ɗora jagorar ƴan adawa María Corina Machado a matsayin shugabar ƙasar.














