Yaushe INEC za ta wallafa sunayen ƴantakara?

Asalin hoton, INEC
Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC ta ce za ta buɗe shafinta na intanet domin jam'iyyun siyasa su aika da sunayen 'yan takararsu a muƙamai daban-daban a babban zaɓen da za a gudanar a 2027.
A bisa tsarin aiki hukumar, INEC ta saka sunayen ƴantakarar kowace jam'iyya a shafinta na intanet, domin bayar da dama ga mutane da su san waɗanda ke takara a kujeru daban-daban.
Tuni da jam'iyyun siyasar ƙasar suka kammala zaɓukan fitar da gwanayen muƙamai daban-daban a shirye-shiryensu na tunkarar babban zaɓen 2027.
Jami'ar hukumar, Hajiya Zainab Aminu ta ce tuni ta kammala shirinta domin fara karbar sunayen.
A watan Janairun shekara mai kamawa ne dai INEC za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴanmajalisun dokoki na tarayya, yayin da za a yi zaɓukan gwamnoni da na ƴanmajalisun jihohi cikin watan Fabrairu, kamar yadda INEC ta tsara.
Sunayen da aka shigar ne kawai za su yi takara?
Bisa tsari da ƙa'idar hukumar zaɓen Najeriya, sunan da aka saka a shafinta ne kawai zai yi takara a zaɓen mai zuwa.
Hajiya Zainab Aminu ta ce ai dama tuni jam'iyyun suka gudanar da zaɓukansu na fitar da gwanaye.
''Don haka duk waɗanda suka samu nasarar a zaɓukan fitar da gwanayen ne za a saka a shafin'', in ji shi.
Ta ƙara da cewa hukumar INEC za ta bayar da horo ga wasu jami'an jam'iyyun ƙasar domin samun damar yin aikin yadda ya kamata.
Wane shiri APC ta yi?
Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ce ita ma a shirye ta ke ta miƙa sunayen nata 'yan takarar.
Bala Ibrahim, daraktan yaɗa labarai na sakatariyar jam'iyyar APC na ƙasa, ya shaida wa BBC cewa, kamar sauran jam'iyyu suma sun shirya miƙa nasu sunayen 'yan takarar.
Ya ce," Dama dai an jima ana aiki a kan waɗannan sunaye, kuma na tantance waɗanda suka cancanci tsayawa takarar, dama INEC muke jira ta bayar lokacin da za a fara miƙa sunayen waɗannan 'yan takara."
"To tun da yanzu INEC ta shirya karɓar sunayen, to muma za mu miƙa mata su don tabbatar da an cika dukkan sharuɗan da INEC ɗin ta gindaya." In ji shi.
Bala Ibrahim, ya ce,"Yanzu daga tsakanin lokacin da INEC ta bayar da umarnin a miƙa sunayen 'yan takarar zuwa lokacin da za a rufe, za mu miƙa namu, sannan za mu bai wa waɗanda suka samu nasara a zaɓukan fitar da gwani takardar shaidar Takara."
Da gaske APC na shirin sauya sunayen ƴantakara?
Kawo yanzu dai jam'iyyar APC ba ta sanar da cikakkun sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓukan fitar da gwanin ba, balle ta ba su shaidar samun takara, wani abu da wasu ke zargin tana shirin sauya sunayen ne.
To sai dai Bala Ibrahim ya kare matakin da cewa jam'iyyar ba ta wallafa sunayen ba ne saboda bin ƙa'ida da doka.
"Idan mutum na so ya yi abu cikin tsafta ma'ana a ka'idance da shari'ance ba tare da an bakantawa wani ba, to dole ne sai an yi taka tsan-tsan an ja kafa an yi komai ta yadda kowa zai gamsu," in ji shi.
Bala Ibrahim, ya bayar da tabbaci, cewa jam'iyyar tasu ba za ta bari wani abu ya kawo matsala ba, wajen mika sunayen 'yan takarar da aka tantance.










