BBC ta ga yadda Taliban ke mulki a Afghanistan

- Marubuci, Kawoon Khamoosh
- Aiko rahoto daga, BBC World Service, Sheberghan, Kabul and Kandahar
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Gwamna Abdullah Sarhadi ya ba da kuɗin maganin wani yaro da ya karya hannu, sannan ya bayar da tallafi ga wani masallaci. Daga baya a ofishinsa da ke arewacin Afghanistan, wata tattaunawa mai ban mamaki ta gudana.
Wata matashiya ta shaida wa tsohon kwamandan Taliban mai gemu cike da furfura cewa tana son a raba aurenta da mijinta, wanda take zargi da cin zarafinta da dukan ta tsawon watanni. Ta nace kan matsayarta.
A ƙasar da aka hana 'yan mata karatun sakandare, budurwar mai shekara 18 ta yi bayanin matsayarta cikin natsuwa da ƙwarin gwiwa, duk da cewa ta rufe fuskarta gaba ɗaya da mayafi sannan ta saka tabarau.
"Da akwai wata damar da za mu ci gaba da zama tare, da ban zo nan ba. Na riga na yanke shawara," in ji ta.
Bayan da gwamnan ya yi ƙoƙarin lallashin ta ka da ta nemi saki, daga baya ya yi ikirarin cewa mata "marasa zurfin tunani ne kuma hankalinsu bai cika ba", lamarin da ya jawo jami'ai, masu gadinsa da dattawan da ke wurin suka bushe da dariya.
Wannan yanayi ya ba da damar ganin yadda rayuwa ke gudana a ƙarƙashin mulkin Taliban, shekaru biyar bayan da suka kifar da gwamnatin da Amurka ke marawa baya a 2021.
A wannan lokaci, an ware mata daga yawancin wuraren aiki, an hana su shiga jami'o'i, kuma ba za su iya tafiya su kaɗai ko shiga wuraren shakatawa da nishaɗi ba.
A cikin shekaru biyu, BBC ta samu damar shiga cikin rayuwar wasu manyan shugabannin Taliban. Ta kuma yi zama da maza waɗanda a baya suka shirya hare-haren kunar bakin wake ko suka shafe shekaru a boye, amma yanzu sun zama jami'ai da sojoji.
Taliban sun hau karagar mulki suna cewa sun sauya, amma yawancin manufofinsu suna kama da tsauraran fahimtar Shari'ar Musulunci da suka aiwatar a shekarun 1990.
Mutanen da muka gana da su sun yi ƙoƙarin nuna kansu a matsayin masu hankali da adalci, amma ba sa son magana sosai game da tashin hankalin da suka yi a baya.
Haka kuma mun ga lokutan rashin jituwar da ke tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka.
Rikicin neman saki

Asalin hoton, EPA/REX/Shutterstock
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sarhadi ya ce wa matar, wadda aka kira Tuba domin kare sunanta, cewa ya kamata ta ci gaba da zama da mijinta.
"Ki tambayi kanki, wa zai aure ni bayan na rabu da mijina? Dole ne ki yi haƙuri sosai, in ba haka ba za ki rasa mutunci da kima," in ji Sarhadi.
Sai ta mayar masa da martani cewa "Malam Gwamna, mutuncina da kimata sun riga sun lalace."
Mijinta yana zaune yana sauraro yana jiran lokacinsa na magana.
A ƙarƙashin shari'a, idan mace ce ta nemi a raba aurenta, ana iya buƙatarta ta mayar da wani ɓangare ko duk kuɗin sadakin da aka ba ta.
Sau da yawa ana cimma yarjejeniyar kuɗi tsakanin ɓangarorin. Amma mijin wannan matar ya nemi a ba shi har sau huɗu na abin da ya bayar, abin da danginta suka ƙi amincewa da shi.
Gwamnan ya yanke hukuncin cewa a ware wa matar ɗakinta. Ya kuma ce za a gargadi mijin kada ya sake dukan ta, in ba haka ba za a daure shi.
Sai dai mahaifin matar bai gamsu ba. Daga baya ya shaida wa BBC cewa za su bi hanyar kotu domin neman saki, duk da cewa a tsarin kotunan Taliban yana da matuƙar wahala mace ta samu saki ba tare da yardar mijinta ba.
Tsohon fursunan Guantanamo
Sarhadi ya kasance kwamandan soja a gwamnatin Taliban ta farko a shekarun 1990.
Yana cikin dubban mayaƙan Taliban da suka miƙa wuya bayan rundunar haɗin gwiwar da Amurka ke jagoranta ta kifar da Taliban a ƙarshen 2001.
An tsare shi na tsawon shekaru a sansanin Guantanamo Bay na Amurka, daga baya kuma aka sake shi.
Bayan Taliban sun sake karɓar mulki, ya zama gwamna a Bamiyan sannan daga baya a Jawzjan. Yanzu kuma mataimakin kwamandan rundunar soja ne a lardin Kunduz.
Yana amfani da tsohuwar waya mai ƙaramin allo, yana cewa haramcin amfani da wayoyin zamani ga jami'ai ya jawo jinkirin aiki.
Rushe gumakan Buddha
Duniya ta yi Allah-wadai lokacin da Taliban suka rusa manyan gumakan Buddha da ke Bamiyan.
Da farko Sarhadi ya yi ƙoƙarin kauce wa tambayoyi game da lamarin, amma daga baya ya ce "Ni da hannuna na rusa su."
Ya ƙara da cewa "Duk abin da muka yi kuma muke yi yana bisa umarnin Allah da shiriya. Muna rushe gumaka maimakon sayar da su. Me zai sa in yi nadama? Nufin Allah ne."
Tsohon mai kula da hare-haren ƙunar bakin-wake

A Kabul, BBC ta gana da Habibullah Badr, wani babban jami'in Taliban.
Ya ce a baya shi ne ke kula da ayyukan masu kai hare-haren ƙunar-baƙin-wake a Kabul.
"Na san dukkan hanyoyi da titunan Kabul sosai. Muna da duk bayanan da muke buƙata," in ji Habibullah Badr.
Hare-haren ƙunar bakin wake na Taliban sun kashe dubban mutane a Afghanistan, ciki har da fararen hula da yawa.
Amma Badr ya kauce wa amsa tambayoyi game da wasu hare-hare da suka afku a yankunan fararen hula.
Ƙorafi kan hana ƴan mata makaranta
A wani taron ƙabilu da BBC ta halarta, shugaban wata gidauniya mai zaman kanta Sultan Mohammad Talaee ya yaba wa Badr, amma ya yi ƙorafi:
"Muna fatan a buɗe makarantu da ilimi ga kowa. Wannan babban alheri ne ga Afghanistan."
Nan take aka yi shiru, kuma aka cire masa makirufo. Amma daga baya ya shaida wa BBC cewa "Na nemi a sake buɗe makarantun 'yan mata. Neman ilimi wajibi ne ga maza da mata a Musulunci."
Ya kuma ce akwai wasu abubuwan da yake son faɗi amma ba a ba shi damar yin magana ba.
Daƙile ƴancin faɗar albarkacin baki

Lokacin da aka tambaye shi game da matakan Taliban na taƙaita 'yancin kafafen yaɗa labarai, sai ya ce:
"A al'umma irin ta Afghanistan muna da iyakokinmu. Ba za mu bari kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa duk irin farfagandar da suke so ba. Ba za su iya watsa shirye-shiryen da suka saɓa wa dokokin Musulunci da al'adun addini ba."
Gwamnatin Taliban tana Kabul, amma Mujahid yana yawan zama a birnin Kandahar da ke kudancin ƙasar, wanda shi ne cibiyar Taliban, kuma wasu yanzu suna kallonsa a matsayin babban birnin ƙasar a aikace.
Mun nemi ganawa da jagoran Taliban mafi girma, Hibatullah Akhundzada, wanda yake zaune a can. Ba kasafai yake bayyana a bainar jama'a ba, kuma bai taɓa yin hira da kafar yaɗa labarai ba. An gaya mana cewa a halin yanzu ba zai yiwu mu gana da shi ba.
An ƙara tsaurara dokoki a Kandahar tun bayan ziyarata ta ƙarshe shekaru biyu da suka gabata. Yanzu dole ne maza su tsayar gemu. An hana gidajen rediyo kunna kiɗa ko watsa muryoyin mata, sannan ba a ba mu izinin ɗaukar hotunan bidiyo a cikin birnin ba.
Bayan tafiyar mota ta kusan sa'o'i biyu a kan hanyoyi masu ƙura, wasu daga cikin tsoffin mayaƙan Taliban da suka fi biyayya ga ƙungiyar sun nuna wa BBC tsohuwar hanyar kogunan sirri da suke amfani da su lokacin yaƙi.
Abid Lalai, wani tsohon mayaƙi wanda yanzu yake aiki a wurin binciken ababen hawa a ƙarƙashin rundunar tsaro ta Ma'aikatar Harkokin Cikin gida, ya nuna mana wuraren da yake harbi daga cikinsu da kuma inda yake ajiye Alƙur'aninsa da rataye bindigarsa ta AK-47.
Shugabansa, Abdul Samad, ya nuna mana wata maƙabarta marar alama, yana cewa mahaifinsa yana binne a wurin, bayan an kashe shi yana yaƙi tare da Taliban.
Martanin kakakin Taliban

BBC ta tattauna da kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, wanda ya bayyana cewa ainihin sunansa Tahir Shah Seddiqi ne.
An tambaye shi dalilin da ya sa Taliban ba su cika alƙawarin da suka yi bayan dawowa mulki ba na barin mata su yi aiki da karatu.
"Muna da cikakken biyayya ga haƙƙin mata da 'yancin faɗar albarkacin baki cikin iyakar Shari'a."
Ya kuma yi ikirarin cewa barin mata su yi aiki a ofisoshi irin nasa zai iya haifar da "lalacewar tarbiyya" tare da rage musu mutunci.
Game da ilimin mata, ya ce har yanzu ana tattaunawa kan neman mafita da ta dace da Shari'a.

Yankin yana cikin mafi talauci a ƙasar, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutum uku cikin huɗu ba sa iya samar wa kansu muhimman abubuwan rayuwa na yau da kullum.
Samad ya ce mutanen yankin suna matuƙar buƙatar ruwa, hanyoyi da cibiyoyin lafiya.
Ya ce:
"Jami'an Daular Musulunci (Taliban) ba su manta da mu ba. Wataƙila shugabannin suna shagaltuwa da wasu manyan abubuwa. Muna da fata cewa wata rana za su kula da mu."
Shekaru biyar bayan Taliban sun sake komawa mulki, talauci, rashin aikin yi da rashin daidaiton tattalin arziki na ci gaba da zama manyan matsaloli.
Jami'an Taliban da muka tattauna da su sun ce suna ƙoƙarin magance waɗannan matsalolin, amma mun kuma gana da wasu mutane da ke ganin cewa ƙungiyar Taliban ita ce babbar matsalar ƙasar gaba ɗaya.
Talauci da ƙalubalen rayuwa
A yankunan karkara da BBC ta ziyarta, tsofaffin mayaƙan Taliban sun nuna wa 'yan jarida wuraren da suka kasance suna ɓoye lokacin yaƙi.
Duk da cewa Taliban na iko tsawon shekaru biyar yanzu, talauci, rashin aikin yi da matsalolin tattalin arziki suna ci gaba da addabar ƙasar.
Wasu daga cikin jami'an Taliban sun ce suna aiki domin magance matsalolin, amma wasu 'yan Afghanistan na ganin Taliban su ne babban matsalar ƙasar.
Wata mata da aka ɓoye sunanta da Hoda ta ce:
"Ban san yadda ƙungiyar da ba ta fahimci rayuwa ba ta samu mulki ba."
"Mata ba za su yarda da wannan yanayi ba. Za su iya ƙara tsaurara dokoki, amma ba zai ci gaba da kasancewa haka har abada ba."
"Ina ganin Taliban suna tsoron mata masu ilimi. Shi ya sa suke takaita mata. Suna son mata marasa ilimi domin kada su reni mutane masu hikima, domin hakan ne zai kawo ƙarshen Taliban."











