Abu 5 da suka hana jam'iyyu fara yaƙin neman zaɓe gadan-gadan a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ya rage 'yan watanni a gudanar da babban zaɓen Najeriya na 2027, har yanzu yaƙin neman zaɓe bai fara ɗaukar zafi gadan-gadan ba.
Hakan dai na haifar da tambayoyi a kan abin da ke janyo tsaiko ga kankamar harkokin siyasa a faɗin ƙasar, duk kuwa da shiga lokacin yaƙin neman zaɓen.
Ana dai ganin sauye-sauyen siyasa da sauyin sheƙar 'yan siyasa da kuma rigingimun cikin jam'iyyu sun taka rawa wajen rashin ganin kazar-kazar ɗin jam'iyyu.
Ga alama yaƙin neman zaben ƴan takara a matakai daban-daban ya gaza kankama gadan-gadan, duk da kasancewar an shafe kwanaki da fara yaƙin neman zaɓen a hukumance.
Kasa da kwanaki dari suka rage kafin zaɓukan, amma har yanzu hada-hadar zaɓen ba kamar yadda aka saba gani a shekarun baya ba, lamarin da ke alamta an samu raguwar karsashi da armashin harkokin zaɓen.
Abubuwan da suka janyo tsaikon
Mutane da dama dai na ta mamakin yadda har yanzu ƴansiyasar ke ɗari-ɗari da harkokin yaƙin neman zaɓe.
To amma masana da masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin hakan a matsayin wata dabara ta amfani da lokaci da tsoron kashe kuɗi.
Dr Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ne kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta CAS a Kano, ya shaida wa BBC cewa abubuwa da dama ne suka haddasa hakan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai ya lissafo wasu abubuwa huɗu da yake ganin suna daga cikin matsalolin da suka haɗa da:
- Lokaci
Abu na farko da ya haifar da jan-ƙafa wajen fara yaƙin neman zaɓe shi ne batun lokaci a cewar Dr Sufi.
Ya ce wasu na ganin kamar idan aka fara da wuri, saboda tsawon lokacin da za a ɗauka ana yi za su iya gajiya.
A ƙarƙashin dokar zaɓe dai akwai aƙalla wata biyar na yaƙin neman zaɓe kafin lokacin zaɓe.
- Tsoron kashe kuɗi
Abu na biyu da masanin siyasar ya bayyana a matsayin dalilin jinkirin shi ne tsoron kashe kuɗi da jam'iyyun siyasa ke yi.
''Dokokin zaɓe sun ƙayyade adadin kuɗaɗen da ya kamata a kashe a kowanne mataki, don haka fara kashe kuɗin tun wuri zai sa iya kashe fiye da abin da doka ta ce." In ji malamin.
Malam Kabiru Sufi, ya ce akwai kuma batun tsadar allunan tallace-tallacenn ƴantakara wanda jam'iyyu ke kokawa.
Wasu bayanai dai na cewa akwai jam'iyyu da ma ciki har da mai mulki da ke cewa sai daf da zaɓe za su shiga kamfen din ka'in da na'in, saboda idan suka fara da wuri to kashe kudin zai yi yawa, lamarin da yasa jam'iyyu da dama suka ce za su yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yada manufofinsu.
- Rashin tabbas a zaɓen
Dr Sufi ya ce wani dalilin jan-ƙafar shi ne rashin tabbas da wasu jam'iyyun ke da shi game da zaɓen na 2027.
''Ga ƙananan jam'iyyu wasunsu na ganin kamar ba inda za su je a zaɓen, don haka suke fargabar kashe kuɗaɗensu wajen yakin zaɓen da ba su ta tabbas game da shi'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Wannan ya sa wasu ƴan jama'iyyar hamayya suka fara goyon bayan Tinubu na APC, duk da kasancewarsu a jam'iyyun adawa.
- Rigingimun cikin gida na jam'iyyu
Masanin kimiyyar siyasar ya ce wani dalilin jinkirin fara yaƙin neman zaɓen shi ne rikicikin cikin gida da wasu jam'iyyun ke fuskanta.
"Akwai rigingimu na cikin da jam'iyyu ke fama da su, saboda akwai batun zuwa kotu da wasu jam'iyyun ke fama da shi, ga kuma batun rashin sanin waɗanda ma ya kamata su yi takara a wasu jihohin, hakan ya sa ƴan siyasa da dama ke jan kafa wajen ci gaba da yakin neman zaɓe," in ji shi.
Zuwa yanzu dai jam'iyyar PDP, da ke cikin jam'iyyun hamayya na ci gaba da fuskantar rikici a cikinta.
- Batun haɗakar ƴanhamayya
Wani ƙarin dalilin jan ƙafar kamar yadda masana ke cewa shi ne batun haɗewar ƴan hamayya wuri guda domin ƙalubalantar Tinubu na APC.
"Wannan na daga ciki, domin har zuwa wannan lokaci ƴan hamayyar ba su fitar da rai game da yiwuwar haɗewar tasu ba'', in ji shi.
A nata ɓangaren jam'iyya mai mulki ta APC, tana nazari a kan salon jam'iyyun hamayyar, Shi ya sa suke ta jan kafa wajen fara yakin neman zabe."
Abin da ya kamata ku sani kan yaƙin neman zaɓen Najeriya da za a fara
A ranar Larabar nan ne 19 ga watan Agusta 2026 za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a hukumance a Najeriya, kamar yadda hukumar zaben kasar INEC ta bayyana.
A bayananta hukumar ta ce, daga ranar jam'iyyu da 'yansiyasa za su fara yakin neman zaben har zuwa jajiberin ranar kada kuri'a - sa'a 24 kenan da za a gudanar da zaben na shekara mai zuwa - 2027.
A tattaunawarta da BBC, mai magana da yawun hukumar zaben ta Najeriya, Zainab Aminu Abubakar ta bayyana hakan:
''Kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanadar, sashe na 94, sakin layi na biyu, ya bukaci jam'iyyun siyasa su fara yakin neman zabe na zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisu na tarayya, kwanaki 150 kafin ranar zabe.''
''Kuma duba da jadawalin zaben 2027 hukumar zaben ta ayyana yau 19 ga watan Agusta a kan ranar da za a fara wannan gangamin yakin neman zaben wadannan kujeru,'' in ji ta.
Za a yi zaben na shugaban kasa ne da 'yan majalisun tarayya da na dattawa da kuma na wakilai ranar 14 ga watan Janairun 2027, kamar yadda jadawalin hukumar zaben ya nuna.
Lokacin kamfe na gwamnoni da 'yan majalisun jiha
Shi kuwa yakin neman zaben gwamnoni da na majalisun jihohi za a fara shi ne ranar tara ga watan Satumba, 2026, kamar yadda jadawalin na INEC ya tabbatar.
Zaben gwamnonin da 'yan majalisun jihohi kuwa za a yi shi ne, ranar 6 ga watan Fabarairu na shekarar ta 2027.
Dokokin zabe sun kuma tanadi cewa dole ne a dakata da duk wani gangamin yakin neman zabe sa'o'a 24 kafin ranar zabe.
Dangane da abubuwan da ya kamata 'yan siyasar su kiyaye da su, kamar yadda doka ta tanada.
Zainab ta ce, babban abin da ya kamata su kiyaye da shi, shi ne yin yakin neman zabe ba tare da tashin hankali ba ko rigingimu da amfani da 'yanbanga ba.
Ta kara bayani da cewa: ''Kuma jam'iyyun siyasa da 'yan takara su kiyaye da amfani da kalamai na batanci ko cin zarafi ga wata jam'iyya ko dantakara ko kuma cin zarafi ga wani sashe na kasa ko wani addini.''
''Haka kuma doka ta hana yakin neman zabe a wurare na ibada. Domin wuararen ibada ba wuri ne da za a je ana yakin neman zabe ba, domin Najeriya kasa ce da ta kunshi addinai daban-daban da yaruka daban-daban.
''Idan aka ce za a rika bin layin addini ko kabila wajen yakin neman zabe to za a iya kawo barazana ga hadin kai da zaman lafiya da ake kokarin ganin an gina a kasar,'' in ji mai magana da yawun INEC din.
Abubuwan da doka ta hana
Mai magana da yawan INEC din ta kuma ce doka ta hana jam'iyyu biyu ko fiye da haka su fito a rana daya a waje daya a lokaci daya kowace ta ce za ta yi yakin neman zabenta, domin za a iya samun tashin hankali.
''Shi ya sa doka ta tanadi cewa kowace jam'iyya ta sanar da jami'an tsaro rana da lokaci da wuri da za ta gudanar da yakin neman zabenta, saboda su wadannan jami'an tsaro za su iya tsara yadda za a kaucewa matsala a ce wannan jam'iyya ta fito waccan ma ta fito ba a lokaci daya,'' a cewarta.



























