Biya ya naɗa sabon shugaban majalisar tsarin mulkin Kamaru

Asalin hoton, ge
Shugaban ƙasar Kamaru, wanda ya daɗe yana mulki, Paul Biya, ya naɗa sabon shugaban Majalisar Tsarin Mulkin ƙasar, bayan rasuwar tsohon shugaban wannan muhimmiyar hukuma.
An naɗa Rémy Nama, wanda aka bayyana a matsayin gogaggen alƙali, domin jagorantar majalisar mai mambobi goma sha ɗaya wadda ke da alhakin duba ko dokoki sun yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasa, da kuma yanke hukunci kan sahihancin zaɓe da kuri'un raba gardama.
Kafin wannan naɗi, Rémy Nama yana aiki ne a Babban Sakatariyar Fadar Shugaban Ƙasa.
Da yake magana ta tashar talabijin ta PRCTV, wadda ke watsa shirye-shirye daga Fadar Shugaban Ƙasa, Nama ya ce:
"Ina cike da godiya da jin daɗin wannan amana, kuma zan iya tabbatar masa (Shugaba Biya) cewa zan yi duk mai yiwuwa domin cika amincewar da ya nuna gare ni."
Ya maye gurbin Clement Atangana, mai shekaru 85, wanda ya rasu a ranar 4 ga Oktoba 2026 a birnin Paris bayan fama da jinya.
Majalisar Tsarin Mulkin Kamaru na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da bin kundin tsarin mulki da kuma sa ido kan sahihancin zaɓuɓɓuka da sauran muhimman matakan dimokraɗiyya a ƙasar.

































