Chelsea da Liverpool da Man Utd na hamayya kan Bowen, Barcelona ta haƙura da zawarcin Alvarez

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea da Liverpool da Manchester United na zawarcin ɗan wasan gaban Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 29, a daidai lokacin da ƙungiyoyin da ke hamayya da juna ke shirin yin riba idan West Ham ta faɗo zuwa matakin gasar Championship inda ake sa ran za ta yi gwanjon fitattun ƴan wasanta. (Guardian)
Barcelona ta fara ja da baya a zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Atletico Madrid ɗan ƙasar Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, a maimakon haka za ta karkata akalarta zuwa kan ɗan wasan gaban Chelsea da Brazil Joao Pedro, mai shekara 24. (Mundo Deportivo)
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya amince da naɗin Enzo Maresca a matsayin wanda zai maye gurbinsa, yayin da AC Milan da Tottenham da Real Madrid su ke zawarcin ɗan kasar Italiya tun bayan da ya bar Chelsea. (Talksport)
Guardiola zai ɗauki hutu na tsawon shekara guda bayan ya bar Manchester City kafin daga bisani ya karɓi aikin horas da tawagar wata ƙasa. (Sport)
Benfica na son kocin Fulham Marco Silva ya karɓi ragamar horas da ƙungiyar daga Jose Mourinho wanda ke hanyarsa ta komawa Real Madrid, yayin da har ila yau ta ke nazari kan tsohon kocin Manchester United Ruben Amorim. (A Bola)
Ɗan wasan gaban Roma ɗan ƙasar Argentina Paulo Dybala, mai shekara 32, yana da sha'awar komawa gasar Premier a kaka mai zuwa. (Sky Sports)
Atletico Madrid da Borussia Dortmund suna fafatawa kan ɗan wasan tsakiya na Brighton da Denmark Matt O'Riley, yayin da kocin Tottenham Roberto de Zerbi shi ma ya nuna sha'awa kan ɗan wasan mai shekara 25. (Teamtalk)
Real Madrid za ta yi nazarin yiwuwar cefanar da ɗan wasan tsakiyar Uruguay Federico Valverde, mai shekara 27, a bazarar nan. (Mundo Deportivo)
Sha'awar da Everton ta nuna kan ɗan wasan FC Midtjylland ɗan ƙasar Chile Dario Osorio, mai shekara 22, ba zai yi tasiri a yarjejeniyar da tea ke neman ƙullawa da ɗan wasan Ingila Jack Grealish mai shekara 30 ba wanda ya ke zaman aro daga Manchester City. (Football Insider)
Everton ta sake farfaɗo da zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Leicester City da Ghana Abdul Fatawu, mai shekara 22. (TeamTalk)










