Dalilai 5 da suka sa gwamnan Osun Adeleke ke son tiƙar rawa

Asalin hoton, Jimoh Abayomi/Facebook
Ademola Adeleke, gwamnan jihar Osun a Najeriya, ya shahara da laƙabin "Dancing Governor" wato gwamna mai yawan rawa saboda yawan rawar da yake yi a wuraren taro da bukukuwa.
A ranar Lahadi bidyoyinsa da hotuna suka karaɗe kafafen sada zumunta da na sadarwa inda yake tiƙar rawa domin murnar lashe zaɓensa wa'adi na biyu bayan doke manyan abokan hamayyarsa na jam'iyyar APC da ADC.
Gwamna Adeleke duk da matsayinsa na gwamna bai hana shi tiƙar rawa ba a duk lokacin da ya samu damar yin ta ko da kuwa a wane wuri ne.
A duk inda ake taro da ya kamata a yi rawa to gwamnan na Osun kan wuce makaɗi da rawa inda yake shan gaban duk wani mai taka rawa kasancewar shi tasa rawar yana yin ta ne da dukkannin jikinsa, inda a mafiya lokuta yake ajiye sandan da ke hannunsa domin taka rawar.
Ga wasu dalilai guda hudu da aka gano su ne dalilain da suka sa Adeleke ya yi fice a tiƙar rawar.
Abin da ya sa nake son rawa - Adeleke

Asalin hoton, Channels TV/Grab
A wata tattaunawa da Ademola Adeleke ya yi da sashen BBC na Yoruba ya ce shi rawa a jininsa take inda ya yi watsi da masu ganin cewa rawar ka iya ɗauke hankalinsa daga harkokin gudanar da mulkin jihar.
- Rawa abin sha'awarsa ne: Ya bayyana cewa rawa wata abu ce da yake jin daɗin yi tun da daɗewa.
- Hanyar nuna farin ciki ce: Ya ce sau da yawa yana yin rawa idan yana murna ko bikin wata nasara.
- Hanyar rage damuwa: An ruwaito cewa yana kallon rawa a matsayin wata hanya ta samun nutsuwa da kawar da gajiya da damuwar aiki.
- Yabon Allah: A wasu bayanai, ya ce rawa wata hanya ce ta nuna godiya da yabo ga Allah.
- Hanyar kusantar jama'a: Masu sharhi sun bayyana cewa rawarsa ta zama wani bangare na halayyarsa da ke sa mutane su ji yana kusa da su kuma suna fahimtarsa cikin sauƙi.
Haka kuma, Adeleke ya taɓa cewa mutane da yawa sun raina shi saboda rawarsa, suna ganin ba zai zama shugaba mai muhimmanci ba, amma ya yi iƙirarin cewa ya mayar da hakan wata kafa ta nuna ayyukansa da nasarorinsa.
Wane ne Ademola Adeleke?

Asalin hoton, Osun State Government House
Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, wanda shi ne gwamnan jihar Osun a halin yanzu, an haife shi ne a ranar 13 ga Mayun 1960 a garin Ede, jihar Osun.
Ya fito daga cikin iyali mai tasiri a siyasa - Mahaifinsa shi ne Sanata Raji Ayoola Adeleke, yayin da mahaifiyarsa, Nnenna Esther Adeleke, ta fito daga yankin Akwete da ke ƙaramar hukumar Ukwa West a jihar Abia.
Ademola Adeleke ya shiga harkar siyasa a shekarar 2001 tare da ɗan'uwansa, Sanata Isiaka Adeleke, wanda ya rasu a watan Afrilun 2017.
Bayan rasuwar ɗan'uwansa, Ademola Adeleke ya tsaya takarar kujerar Sanatan Osun ta Yamma , inda ya samu nasara a zaɓen cike gurbi na shekarar 2017 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.
Kafin komawarsa PDP a watan Afrilun 2017, Adeleke ya kasance mamba a jam'iyyar APC.
Daga baya, ya shiga takarar gwamnan jihar Osun, inda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyarsa bayan ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Akin Ogunbiyi, da ƙuri'u bakwai kacal. Bayan haka ya tsaya takarar gwamna a zaɓen da aka gudanar a ranar 23 ga Yulin 2018.

Asalin hoton, Channels/Grab
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan Disamban 2025, Adeleke ya koma jam'iyyar Accord, inda ya samu tikitin takarar gwamna domin neman wa'adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar Osun.
A ranar 22 ga Maris, 2019, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar zaɓe ta ƙasar ta ce bai kammala ba. Amma daga bisani, a ranar 5 ga Yulin 2019, Kotun Ƙolin Najeriya ta soke wannan hukunci tare da tabbatar da Gboyega Oyetola a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun na 2018.
A zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga Yulin 2022, Adeleke ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, inda ya samu nasara kan gwamna mai ci a wancan lokaci, Gboyega Oyetola.
Adeleke ya samu ƙuri'u 402,979, yayin da Oyetola ya samu 375,027, abin da ya ba shi damar lashe zaɓen.
Ademola ya yi karatun Kimiyyar Siyasa (Political Science) a Jami'ar Jacksonville State University da ke jihar Alabama, Amurka.
Ademola Adeleke fitaccen ɗan kasuwa ne kuma ƙwararren mai gudanarwa.
A cewar bayanan da aka bayar, ya riƙe mukamin Babban Darakta na kamfanin Guinness Nigeria Plc tsakanin shekarun 1992 zuwa 1999.
Haka kuma, ya kasance Babban Daraktan kamfanin Pacific Holdings Limited daga shekarar 2001 zuwa 2016. Kafin wannan, ya yi aiki da kamfanin Quicksilver Courier da ke Atlanta, jihar Georgia ta Amurka tsakanin 1985 zuwa 1989.
Adeleke ya kuma yi aiki da kamfanin Origin International LLC da ke Atlanta, Georgia, inda ya riƙe mukamin mataimakin shugaban kamfanin tsakanin 1990 zuwa 1994.












