'Ya kamata malaman adinin musulunci su nesanta adini daga harkokin siyasa'

Fitaccen malaman addinin Musuluncin nan a Najeriya yi yi kira ga takwarorinsa kan nesanta addini da harkokin siyasa, domin kauracewa kalaman da ke iya tunzura jama'a ko haifar da rabuwar kai a kasar.
Sheikh Muhammad Nurul Khalid wato Digital Imam, ya yi wannan kira ne bayan kalaman shugaban majalisar malaman ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir kan takarar Muslim-Muslim da suka tayar da kura a Najeriya.
A hirar da ya yi filin Gane mani hánya Sheikh Khalid ya nuna damuwa kan ce-ce-ku-cen da suka biyo baya a shafukan sada zumunta sakamakom kalaman da suka fito daga bakin malamin
''Na farko dai dimokuraɗiyya da ake tunkahon ta dore a Najeriya za'a yi mata karan tsaye, shi ne kamar yadda kowa ya sani, ita dimokuraɗiyya tsari ne wanda aka fi so. Ra'ayin alumma ya yi tasiri a zabe, ta hanyar duba da menene bukatun kasa da 'yan kasa''
''Na biyu wanda ya fi muni shi ne kasancewar zai kawo ce-ce-ku-cen da zai iya kai wa ga zub da jini, misali yanzu idan mutum ya duba soshiyal midiya, abin ya dinga faruwa, ashara-ashara da zage-zage sakamakon wannan abun, ai be dadi''
''Saboda haka abinda ya kamata a yi shi ne mu dawo kan turba ta maganar cewa muna son a zauna lafiya ko da mutum yana son ya zabi musulmi da musulmi yanada yanci wanda kuma ya ce shi kirista ya ke so, ya yana da yanci amma ce wani daga cikinsu zaa hantareshi ko a gaya masa bakar magana saboda be zabi kirista ba ko be zabi musulmi ba a nan matsalar take'' in ji shi
Malamin ya nuna rashin dadinsa a kan abubuwan da suka biyo baya da kuma kalaman da wasu suka yi rika a shafukan sada zumunta inda aka bayyana musulmi a matsayin masu tsatsauran ra'ayi
''Naji ba dadi, abinda nayi imani da shi, abinda na tashi na ga iyaye na da malamai na da kakanni na akai na cewa shi ne hanyar tsira , samun aljana da lahira da kuma kyaukyawar rayuwa a duniya in ga an fito ana sukar wannan abin , ba zan ji dadi ba''
''Musulunci inda zaa bi shi a yadda aka karanta shi , to addini ne na zaman lafiya, amma gaskiya in muna son mu wanke musulunci daga wannan bakin fenti sai mun gyra mu malamai tukun, mu gane cewa zaka iya karantar da akidarka da imaninka da adininka da siyasar ka ba tare da ka tsokani wani ba in ji shi''.
Hadarin da ke cikin kalaman Sheihk Jingir
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu na ganin cewa malamai da dama ba su fito sun soki kalaman da suka fito da Sheikh Jingir ba , kuma ana ganin wannan na nufin cewa sun yi shuru ne saboda sun amince da abinda ya fada, amma malamin ya musunta haka
''Shi shuru ba koda yaushe bane yake nuna amincewa ba, sai dai wani lokaci shuru ya fi magana muhimanci ne. Da yawa daga cikin malamai sun yi shuru wala'Allah saboda sun amince da abin da yake kai, wasu kuma saboda suna ganin, ato ai ba farau bane, dan haka ma a tsaya ayi magana ba tada amfani '
Malamin ya kuma ce wasu ba su fahimci hadarin da ke cikin maganar Sheik Jingir ba
''Ina nufin wadanda suka yi magana suka goyi bayanshi ko kuma suka yi shuru a kan goyon baya suna kallon kawai ya ce a zabi muslim-muslim ticket kamar yadda na ce wannan ba laifi bane.Amma cewa wanda bai zaba ba a gaya masa magana mara dadi wannan be yiba''
Malamin ya yi kira ga malaman da suka yi shuru da su sani cewa lokaci ya yi da za a tsaftace karantarwar musulunci.
Digital Malam ya ce matsalar da ake fuskanta ita ce Sheikh Jingir ya dau wata matsaya ce wacce take nuna shi ya zama gagarabadau kuma 'da ya samu masu fada masa gaskiya, ya ji da ba a kai wannan matsayar ba'
Ya ce halin yanzu ana kokarin samar da wata majalisar ladabtarwa ta malamai duk cewa alhaki ya rataya a wuyan jama'atul Nasrul Islam da Majalisar kula da harkokin adinin musulunci.
''Jama'atul Nasrul Islam ita ce kamata a ce tana sanya wa kowani malami akala ko majalisar koli kan harkokin adinin musulunci to amma shin ire -irensu sun yadda da ma da a kirasu' in ji shi''
Mafita
Malamin ya bada shawara a matsayn mafita wajan samun zaman lafiya mai dorewa a kasar:
''Mafita ita ce mu malamai mu yadda cewa ba mu mallaki adinin nan kuma ba mu mallaki kasar nan ba . kowa daga cikinmu ya yarda shi mai karantar wa ne. Idan ya fadi ra'ayin shi, wani be amince ba, to kafirtar da shi bata taso ba, cin zarafinsa ba ta taso ba''
''Ya kamata a nemi yadda za a zauna da juna lafiya, kada a rena wani, kada wani ya dauki kansa gagarabadau'' in ji shi
Game da maganar da ake yi kan cewa tun farko bai kamata malaman adinin musulunci su shiga cikin harkokin siyasa ba Malamin sai ya ce:
''Malamai idan za su yi siyasa, su ajiye malanta gefe daya, su fito su zama 'yan siyasa amma idan ba za su yi siyasa ba , toh su zauna a matsayin iyayen al'umma''
''Malami zai iya bada shawara ya ce ina goyon bayan a zabi wane amma ya fito ya maida kanshi dan siyasa mai talar jam'iyya ko mai tallan dan takara, wannan bai da ce ba, in zai yi ya ajiye malanta'' in ji shi
A karshe malamin ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi la'akari da abubuwa uku wajan zabar shugabanni a zaben dake karatowa wadanda suka hada da tsaro da tattalin arziki da kuma ilimi.













