Wace rawa Arewa maso Gabas ke takawa a zaɓen shugaban Najeriya?

Yankin Arewa Maso Gabas ya ƙunshi jihohi shida ne, wato Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, waɗanda ke da jimillar masu rajistar zaɓe sama da miliyan 12.

Asalin hoton, Ismaila Uba Misilli/FB

Bayanan hoto, Yankin ya ƙunshi jihohi shida ne, wato Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, waɗanda ke da jimillar masu rajistar zaɓe sama da miliyan 12.
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na daga cikin shiyyoyin da ke taka muhimmiyar rawa a zaɓen shugaban ƙasa, musamman saboda jiga-jigan ƴan siyasa da suka fito daga wannan yanki.

Yankin ya ƙunshi jihohi shida ne, wato Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, waɗanda ke da jimillar masu rajistar zaɓe sama da miliyan 12.

Ko da yake yankin ba shi ne wanda ya fi yawan masu rajistar zaɓe ba a Najeriya, amma kasancewar yana ɗaya daga cikin manyan shiyyoyin Arewa, jam'iyyun siyasa da ƴan takarar shugaban ƙasa kan ba shi muhimmanci wajen neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri'a.

A zaɓukan shugaban ƙasa da suka gabata, yankin na ɗaya daga cikin wuraren da suka taka rawa wajen tabbatar da nasarar wasu ƴan takarar shugaban ƙasa, lamarin da ya sa ake sa ido kan yadda ƙuri'unsa za su kasance a babban zaɓen 2027.

Yankin ya samar da mataimakan shugaban ƙasa biyu - Atiku Abubakar daga Adamawa sai Kashim Shettima daga Borno.

Me ya sa Arewa maso Gabas ke da muhimmanci?

Masana na ganin duk ɗan takarar da ke neman zama shugaban ƙasa ba zai iya yin watsi da yankin ba, musamman idan yana neman samun gagarumin goyon baya daga Arewa.

A bisa bayanan hukumar zaɓe ta ƙasar (INEC) kafin zaɓen 2023, Arewa maso Gabas na da masu rajistar zaɓe mutum 12,542,429.

Ko da yake wannan adadi bai kai na Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya ba, amma ya fi na Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas fitowar masu kaɗa ƙuri'a..

Baya ga yawan masu kaɗa ƙuri'a da yankin ke da su, akwai fitattun ƴan siyasa da suka taka muhimmiyar rawa a matakin ƙasa.

Yankin ya samar da mataimakan shugaban ƙasa biyu - Atiku Abubakar daga jihar Adamawa da Kashim Shettima daga jihar Borno. Baya ga wasu ƙusoshin gwamnati da ake damawa da su daga yankin kamar su mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu a gwamnatin Tinubu.

Masanin siyasa Farfesa Abubakar Kari ya ce "ƙuri'un da ake samu daga Arewa maso Gabas kan yi tasiri a zaɓen shugaban ƙasa, musamman idan aka yi la'akari da yadda wasu jihohin yankin ke da yawan masu fita kaɗa ƙuri'a a lokutan zaɓe."

"Suna da masu kaɗa ƙuri'a sosai," in ji shi.

Bambancin Arewa maso Gabas idan aka kwatanta da sauran shiyyoyi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayanan INEC na rajistar masu zaɓe kafin zaɓen 2023 sun nuna cewa Arewa maso Gabas ce ta biyar a yawan masu rajistar zaɓe a cikin shiyyoyin Najeriya, inda take da jimillar masu rajista 12,542,429.

Ga yadda jimillar masu zaɓe yake a shiyyoyin ƙasar:

  • Arewa maso Yamma - 22,255,562
  • Kudu maso Yamma - 17,958,966
  • Arewa ta Tsakiya - 15,363,731
  • Kudu maso Kudu - 12,674,248
  • Arewa maso Gabas - 12,542,429
  • Kudu maso Gabas - 10,907,606

Alƙaluman sun nuna cewa Arewa maso Gabas na da tazarar masu rajista kusan 131,819 tsakaninta da Kudu maso Kudu, inda ta zarce Kudu maso Gabas da fiye da mutum miliyan 1.6.

Yawan ƙuri'un da ke fitowa daga jihohin wannan yanki a lokacin zaɓe ne ke taka muhimmiyar rawa.

Farfesa Kari ya buga misali da yadda tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu ƙuri'u masu tarin yawa daga yankin, inda ya ce hakan ya sa ƴan takarar shugaban ƙasa ke ɗaukar yankin da muhimmanci.

A baya-bayan nan kuma, INEC ta ce tana ci gaba da sabunta rajistar masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

A cikin bayanan da hukumar ta fitar ranar 26 ga Yunin 2026, ta ce mutane 1,565,873 ne suka kammala rajistar zaɓe a ƙarshen mako na bakwai na aikin sabunta rajistar.

Sai dai hukumar ta ce waɗannan alkaluma na wucin gadi ne, kuma za a sake tantance su bayan kammala aikin rajistar.

A waɗannan alƙaluman, Kano ce take kan gaba wajen samun sabbin masu rajista, inda ta samu ƙarin mutane 118,207. Bayan Kano sai Lagos da ke da sabbin masu rajista 78,360, sannan Delta mai 76,395.

Babu wata jiha daga Arewa masi Gabas da ke kan gaba a wannan sabbin alƙaluma.

Jihohin da suka fi tasiri: Borno, Bauchi da Adamawa

Daga cikin jihohi shida na yankin, Bauchi, Borno da Adamawa ne suka fi ɗaukar hankali saboda yawan masu fita zaɓe da kuma tasirin siyasar da suke da shi.

Bauchi ce ta fi yawan masu rajistar zaɓe da mutum 2,749,268, sai Borno da 2,513,294, yayin da Adamawa ke da 2,196,566, kamar yadda bayanan INEC na 2023 suka nuna.

Su kaɗai suna da fiye da rabin masu rajistar zaɓen Arewa maso Gabas. Ƙuri'un waɗannan jihohi sun taka rawa a zaben ƙasar da ya gabata.

Jihar Borno, wadda ita ce mahaifar mataimakin shugaban ƙasa na yanzu Kashim Shettima, ɗan takarar APC Bola Tinubu ne ya yi nasara da ƙuri'u 252,282, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu 190,921. Tinubu ya yi nasara da tazarar ƙuri'u 61,361.

A Bauchi, Atiku Abubakar ya lashe jihar da ƙuri'u 426,607, yayin da Tinubu ya samu 316,694. Tazarar ƙuri'un da Atiku ya bai wa Tinubu ta kai 109,913.

A Adamawa, wadda ita ce jihar Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya samu ƙuri'u 417,611, yayin da Tinubu ya samu 182,881.

Sakamakon zaɓen 2023 ya nuna cewa duk da nasarar da Tinubu ya samu a matakin ƙasa, bai samu mafi yawan manyan jihohin Arewa maso Gabas ba. Daga cikin jihohin uku da suka fi yawan masu rajistar zaɓe a yankin, APC ta yi nasara ne a Borno kaɗai.

Saboda haka, duk ɗan takarar da ke neman zama shugaban ƙasa zai yi ƙoƙarin samun gagarumin goyon baya daga Bauchi, Borno da Adamawa a yankin Arewa maso Gabas.

Ko yankin zai yi tasiri a zaɓen 2027?

Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke iya shafar muhimmancin Arewa maso Gabas a zaɓen shugaban ƙasa shi ne matsalar tsaron da yankin ke fuskanta.

Hare-hare sun yi sanadin mutuwar dubban mutane, lalata kadarori da kuma raba miliyoyin jama'a da muhallansu amma ba lallai kuma ya rage yawan ƙuri'un da za su fito daga yankin ba saboda ko a can baya suna taka rawar gani.

Farfesa Kari ya ce hakan na iya shafar harkokin siyasa da zaɓe, domin wasu masu rajistar zaɓe sun kasa komawa rumfunan zaɓe saboda ƙaura da suka yi zuwa wasu wurare ko kuma fargabar kai wa hari.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, INEC ta ce ta fuskanci ƙalubalen gudanar da zaɓe a wasu yankunan da rikicin ya fi shafa, musamman wuraren da ake fama da matsalar tsaro da kuma sansanonin 'yan gudun hijira.

Masana siyasa na ganin cewa yawan fitowar masu zaɓe na daga cikin abubuwan da ke tantance irin tasirin da kowace shiyya ke da shi a zaɓe.

"Idan rashin tsaro ya hana mutane masu rajistar zaɓe zuwa kaɗa ƙuri'a, hakan na iya rage ƙarfin ƙuri'un yankin," in ji Farfesa Kari.

Sai dai masanin na ganin yankin zai iya yin tasiri la'akari da cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya fito daga wannan yanki, kuma shi ma babban ɗantakarar adawa ta ADC Atiku Abubakar ya fito ne daga yankin.