Yadda Iswap ta fuskanci koma-baya a Najeriya daga farkon 2026

Asalin hoton, Getty Images
Wata shida bayan kamawar shekarar 2026, ƙungiyar IS ta fuskanci abubuwa da dama. Kungiyar ta yi iƙirarin faɗaɗa yankunan da take iko da su a Afirka, amma duk da haka ta samu koma-baya a yankin na Afirka.
Nahiyar Afirka ta ci gaba da zama muhimmin wurin da ƙungiyar ta IS ke ƙaddamar da hare-harenta da kuma yaɗa farfaganda.
Kusan kashi 90% na hare-haren da ƙungiyar ta kai a cikin wannan shekara, ta ce ta kai su ne a cikin nahiyar ta Afirka.
Sai dai duk da haka nan ƙungiyar na mayar da hankali sosai wajen ayyukanta a Syria.
Wannan bayani ya yi nazari ne kan ayyukan ƙungiyar da saƙonnin da ta ke fitarwa daga farko zuwa tsakiyar shekara ta 2026.
Duk da cewa yawancin farfagandar ƙungiyar ya mayar da hankali ne kan ayyukan ressanta da ke Afirka, bayanan da ɓangaren yada labaranta na al-Naba ya riƙa yaɗawa ya nuna muhimmancin Syria ga ƙungiyar.
Haka nan bayanan da ƙungiyar ke fitarwa sun riƙa jinjina wa ayyukan ressan ƙungiyar a Afirka da kuma jinjina musu, musamman domin ƙara wa mayaƙan ƙungiyar ƙaimi a sauran sassan duniya kamar Gabas ta Tsakiya.
Yayin da sakonnin ƙungiyar ke iya alamta juriya da dagiya na mayaƙanta, amma sun fito da wasu hujjojin da ke nuna cewa ƙungiyar tana cikin damuwa, musamman game da karyewar ƙwarin gwiwar mayaƙanta.

Koma baya a Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Idan aka duba alƙaluman mako-nako da wata-wata na hare-haren da mayaƙan ƙungiyar ke kaiwa, ayyukan reshen ƙungiyar a Najeriya ya kai kimanin kashi 50% na hare-haren da ƙungiyar ta ƙaddamar a faɗin duniya.
ISWAP ta riƙa kai hare-hare kan sansanonin jami'an tsaro da sojoji a faɗin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma ayyukan mayaƙan ƙungiyar sun yi ƙamari ne a watannin Fabarairu zuwa Maris, lokacin watan Ramadana.
Sai dai hare-haren ƙungiyar ya yi ƙasa tun daga watan Afrilu.
Ayyukan hadin gwiwa da dakarun Najeriya da na Amurka suka ƙaddamar kan ISWAP a ranar 16 ga watan Mayu ya kawo cikas ga ƙungiyar, lamarin da ya sanya ƙungiyar ta gaza fitar da sanarwar iƙirarin kai wasu hare-haren, wanda hakan alama ce ta cewa an yi illa ga ɓangaren yaɗa labaranta.
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren da dakarun na Najeriya da Amurka suka kai sun hallaka manyan kwamandojin ƙungiyar, ciki har da jagoranta Abu Bilal al-Manuki - wani abu da ita kanta ƙungiyar ta tabbatar a kaikaice.
A sauran yankin Sahel kuwa hare-haren ƙungiyar sun ci gaba da faruwa jefi-jefi, amma sun kasance masu muni saboda yawan sojojin da take halakawa.
Munanan hare-haren da ƙungiyar ta riƙa kaiwa a yankin Sahel a farkon shekarar 2026 sun kasance ne a cikin Jamhuriyar Nijar, ciki har da mummunan harin da ta kai a babban filin jirgin sama na ƙasar, inda IS ta yi ikirarin cewa an yi amfani da mayaƙa daga ƙasashen waje wajen kai harin.
A watan Mayu reshen ƙungiyar ya yi ikirarin kai hari na farko a arewa maso yammacin Najeriya, wani abu da ƙungiyar IS ta yaba da shi, tare da bayyana shi a matsayin ''faɗaɗa'' yankin da take iko da shi.
Sauran yankunan Afirka
Ayyukan IS Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun kasance jefi-jefi a watanni shida na farkon 2026, inda ta yi ikirarin kai hare-hare sau biyar a watan Afrilu, maimakon hare-hare 45 a watan Mayu.
IS da mambobinta sun yi murnar mamaye sabbin yankuna a karon farko yayin da reshen ungiyar a asar ta DRC ya yi ikirarin kai hare-hare a lardin Haut-Ulele da kuma yammacin lardin Ituri.
Mabiya addinin kirista ne suka fi shan wahala a hare-haren da ungiyar ke kaiwa a asar, inda suka kasance kashi 75% na mutanen da ake ritsawa da su.
A Somaliya, bayan kwashe watanni da dama ba tare da ta kai wani harin a zo a gani ba, a cikin watan Mayu ƙungiyar ta fitar da jerin sanarwa yayin da kafafen yada labarai suka riƙa bayar da rahotannin sake taruwar mambobinta a yankin tuddan Al Miskad da ke yankin Puntland.
Wace ƙungiya ce Iswap?
Ƙungiyar ISWAP ta kafu a shekarar 2016 bayan ɓallewa daga ƙungiyar Boko Haram da Shekau ke jagoranta
Ƙungiyar ta ɓalle ne sakamakon saɓanin ra'ayi tsakanin al-Qaeda da kuma IS, kamar yadda Dakta Kabiru Adamu ya bayyana.
''Aƙidarta ita ce kafa daular Musulunci, sannan tana bambanta mutanen da take kai wa hare-hare, saɓanin Boko Haram da ke kai wa kowa'', in ji shi.
Mutumin da ya jagoranci ƙungiyar na farko shi ne sheikh Abu Mus'ab Albarnawi, wanda aka yi imanin cewa shi ne babban ɗa ga Muhamamd Yusuf, shugaban ƙungiyar Boko Haram na farko.
Ƙarƙashin al-Barnawi, ISWAP ta yi ƙaurin suna wajen ƙaddamar da hare-hare musamman kan jami'an tsaron Najeriya da na ƙasashe makwabta.











