Wane ne ɗantakarar gwamnan Kano a jam'iyyar ADC?

Ƴantakarar gwamnan ADC a Kano, Sheikh Ibrahim Khalil (a hagu) da Ibrahim Al-Amin Little (a dama)

Asalin hoton, Facebook Multiple

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Jam'iyyar hamayya ta ADC a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta shiga cikin wani ruɗani kan rashin sanin wanda zai yi mata takarar gwamna a zaɓen 2027.

Manyan ƴantakara biyu Sheikh Ibrahim Khalil da Ibrahim Al-Amin Little da ke fatan samun tikitin takarar na cikin halin rashin tabbas, yayin da magoya bayansu ke iƙirarin bai wa ɓangarensu takarar.

Wannan na zuwa ne bayan da ADC ta rusa shugabancin jam'iyyar na Kano tare da kafa kwamitin riƙo.

Kano na cikin jihohin ƙasar da jam'iyyar ADC ke fuskantar rikicin shugabanci, wani abu da ya fara janyo tarnaƙi wajen fitar da ƴantakarar.

Mene ne asalin rikicin ADC a Kano?

Rikicin shugabancin ADC a Kano ya samo asali ne tun bayan ficewar tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso daga cikinta.

A ƙarshen watan Maris ɗin shekarar nan ne jagoran na Kwankwasiyya ya shiga jam'iyyar ADC, wani abu da ya ƙara wa jam'iyyar ƙarfi da tarin magoya baya a jihar, wadda ta fi kowa yawan al'umma a arewacin ƙasar.

Kafin shigar Kwankwaso ADC, Musa Ungogo ne shugabanta na jihar Kano.

Bayan shigar Kwankwaso, jam'iyyar ta zaɓi shugabannin riƙo, inda aka zaɓi mutanen Kwankwaso a matsayin jagororin jam'iyyar a jihar, yayin da Musa Ungogo ya zama mamba a kwamitin zartarwar jam'iyyar na jiha.

To sai dai ficewar Kwankwaso daga jam'iyyar a farkon watan Mayu tare da magoya bayansa ta sa shugabancin ADC a jihar Kano ya rushe, bayan da mutanen Kwankwaso suka ajiye shugabancin jam'iyyar suka kuma bi shi zuwa jam'iyyar NDC.

Bayan shugabannin jam'iyyar jihar sun ajiye muƙamansu, shi ne sai Musa Shu'aibu Ungogo ya yi iƙirarin shugaban riƙo na jam'iyyar, yayin da a gefe daya Hajiya Naja'atu Muhammad ta naɗa shugabannin riƙo ƙarƙashin Alhaji Umar Bala Kwalwa.

Ɓangarorin biyu sun riƙa samun saɓanin fahimta a tsakaninsu, har sai da uwar jam'iyyar ta ƙasa ta ce kowane ɓangare ya dakata har sai ta yanke hukunci kan shugabancin jam'iyyar a jihar.

Su wane ne ke son yin takara karkashin ADC a Kano?

Mutane biyu ne ke takarar gwamna a jihar Kano a jam'iyyar ta ADC da suka haɗa da:

  • Sheikh Ibrahim Khalil

Fitaccen malamin addini kuma ɗansiyasa a jihar Kano ya jima a cikin jam'iyyar.

A zaɓen shekarar 2023 ya tsaya wa jam'iyyar takarar gwamna, inda kuma ya zo na uku a zaɓen.

Yana fatan sake samun tikitin jam'iyyar domin yi mata takara a zaɓen 2027 da ke tafe.

  • Al'amin Little

Fitaccen ɗansiyasa ne a jihar Kano, wanda ya jima ana damawa da shi a fagen siyasar jihar.

Litle ya sha tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar PDP a zaɓukan da suka gabata

A watan Yulin 2025 ne ya koma ADC bayan ficewarsa daga tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.

A yanzu yana da burin tsayawa takarar gwamnan Kano a jam'iyyar ADC.

Me ya hana ADC fitar da ɗantakara a Kano?

Dangane da wanda zai yi wa jam'iyyar takarar gwamnan jihar kuwa BBC ta tuntuɓi ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar na ƙasa, Faisal Kabir, wanda kuma ya ce har yanzu uwar jam'iyya ba ta yanke wanda zai yi mata takarar gwamna a Kano ba.

''Dangane da zaɓar ɗantakarar masalaha aka amince a yi, kuma uwar jam'iyya ce za ta yanke shawara kan haka'', in ji shi.

Faisal ya ce har yanzu shugabannin jam'iyyar na ƙasa na tattaunawa kan fitar da ɗantakarar gwamnan na Kano.

Kuma muna fatan cimma hakan nan ba da jimawa ba, bayan tuntuɓar duka masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Ya ƙara da cewa jam'iyyar za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta daɗaɗa wa kowane ɓangare a hukuncin da za ta yanke.

''Dama dai kowa ya sani takara mutum ɗaya ne zai samu, amma jam'iyya za ta yi amfani da hikima da adalci ga kowane ɓangare, don tabbatar da ɗorewar jam'iyyarmu'', in ji shi.

Me ɓangarorin biyu ke cewa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alhaji Umar Bala Kwalwa, na ɓangaren Hajiya Naja'atu ya ce an kira duka ƴantakarar biyu zuwa Abuja, inda aka ba su damar yin sulhu a tsakaninsu, amma suka kasa cimma hakan.

''An kafa kwamitin sasanci domin fitar da ƴantakara a tsakaninsu, kuma aka ba su damar su yi masalaha, amma hakan bai samu ba, aka ƙara ba su wata ranar suka zauna tsakaninsu nan ma ba a cimma nasara ba'', kamar yadda ya ce.

Alhaji Umar Kwalwa ya ce bayan sun gaza cimma matsaya, sai suka bayyana wa kwamitin sasancin cewa sun miƙa wuya sun ba shi wuƙa da nama, domin zaɓar wanda suke ganin ya dace.

''Kowannensu ya furta da bakinsa a gaban kwamiti cewa ya amince da duk matakin da kwamiti ya ɗauka game da wanda zai yi takara, aka kuma yi a rubuce, kowanensu ya saka hannu, don haka kwamiti ya yi aikinsa, ya kuma miƙa wa uwar jam'iyya rahoto'', in ji sji.

Ya ƙara da cewa a yanzu abin da ya rage shi ne uwar jam'iyya ta kammala tattaunawa domin sanar da ɗantakarar gwamnan Kano.

Amma a nasa bangaren Umar Shu'aibu Ungogo ya yi iƙirarin cewa an yi zaɓen fitar da gwani a jam'iyyar inda Ibrahim Khalil ya lashe zaɓen.

Ya ce an aika kwamitin wakilan zaɓen ƙarƙashin jagorancin John Ayuba, wanda ya ce sun jagoranci gudanar da zaɓen.

''An fara da zaɓen ƴan majalisar jiha da na gwamna a ƙarƙashin kulawata, yayin da aka gudanar da na shugaban ƙasa ƙarƙashin kulawar Hajiya Naja'atu'', in ji shi.

Ungogo ya ce da kansa ya kira Litle domin shiga zaɓen, amma sai ya ce masa ba zai shiga takara ba saboda ya riƙe shugabancin jam'iyyar a baya.

''Amma duk da haka aka yi zaɓe da shi, Sheikh Ibrahim Khalil ya samu nasara da rinjayen ƙuri'u, amma sai Hajiya Naja'atu ta hana,'' kamar yadda ya yi iƙirari.

Ya ce sai da aka je Abuja ne sai aka fito da batun sasanci tsakanin ƴantakara.

Ungogo ya ce yanzu haka suna jiran uwar jam'iyya ta ƙasa domin sanin matakin da ta ɗauka game da batun.