Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Donald Trump ya caccaki Fafaroma Leo

    Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki shugaban ɗariƙar katolita na duniya Fafaroma Leo, inda ya zarge shi da rauni wajen yaƙi da laifuka da kuma rashin ƙwarewa a harkokin ƙasashen waje.

    Da yake magana da manema labarai bayan wallafa saƙon a shafukan sada zumunta, Trump ya ce shi ba “babban mai goyon bayan” Fafaroma ba ne, wanda ya yi ta bayyana ra’ayoyinsa kan yaƙin Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.

    A nasa ɓangaren, Fafaroma Leo ya bayyana barazanar da shugaban ya yi ta rusa al'umma da tarihin Iraniyawa a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba”.

    Trump ya ƙara da cewa ba ya son Fafaroma da ke sukar shugaban Amurka, yana mai ikirarin cewa bai zama lallai Fafaroma ya hau kujerar da yake kai ba da ba shi ne a Fadar White House ba.

    A lokacin hutun Easter kuwa, Fafaroma Leo ya roƙi shugabanni a bainar jama’a da su kawo ƙarshen tashin hankali tare da daina bautar da jama'a da kuma ƙuntata masu.

  2. Hare-haren Rasha sun ci gaba a Ukraine bayan tsagaita wuta

    An sake samun hare-haren Rasha a Ukraine bayan ƙarewar wa’adin tsagaita wuta da aka ayyana domin bikin Easter na Orthodox a ƙarshen ranar Lahadi.

    Rahotanni sun ce an ji ƙarar fashe-fashe a yankunan Sumy da Dnipro-petrovesk da kuma Kirovoh-rad.

    Haka kuma an ji ƙarar garkuwar tsaron sararin samaniya a birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Tsagaita wutar dai ba ta cika lokacin da aka kwashe ba, sai da ɓangarorin biyu suka zargi juna da ƙarya yarjejeniyar sau da dama.

  3. Peter Magyar ya zama firaiministan Hungary bayan doke Viktor Orban a zaɓen

    Magoya bayan ƴan adawa a Hungary sun shafe dare suna bukukuwa bayan gagarumar nasarar da Peter Magyar da jam’iyyarsa ta Tisza ta samu a zaɓen ƙasar.

    Jam’iyyar Tisza mai goyon bayan muradun ƙungiyar tarayyar Turai ta samu kashi biyu bisa uku na kujerun majalisar dokokin ƙasar, lamarin zai ba ta damar canza kundin mulkin ƙasar.

    Mr Magyar ya yi jawabi ga ɗinbin magoya bayansa a Budapest, inda ya ce sun ƙwato ƴancin Hungary ta hanyar kawar da gwamnatin firaminista Viktor Orban.

    Mr Magyar ya shaida wa magoya bayan nasa cewa da wannan nasara, Hungary za ta koma yadda take a baya, a matsayin babbar ƙawa ga ƙungiyar tarayyar Turai da kuma ƙngiyar tsaro ta NATO.

    Tuni dai Viktor Orban ya kira Peter Magyar ta waya, tare da taya shi murnar nasara a zaɓen, sannan kuma ya yi jawabin karɓar ƙaddara ga ƴan jam’iyyarsa da ta sha kayi.

    A gefe guda kuma ƴan adawa ne suka shiga shagulgulan murnar wannan nasara, inda suka shafe dare suna kaɗe-kaɗe da raye-raye,

    Wannan dai gagarumar nasara ce ga jam’iyya mai ra’ayin mazan jiya da aka kafa shekau biyu da suka gabata, kuma ta janyo murna da farin ciki a ƙasar da ma ƙasashen Turai.

    Mr Orban wanda abokin ɗasawar Donald Trump da kuma Vladimir Putin ne ya bayyana Rashin nasarar tasa a matsayin abin baƙin ciki.

    Ya dai shafe shekau 16 yana jan ragamar gwamnatin Hungary.

  4. Gwamna Zulum ya ce sun rufe kasuwar Jilli

    Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatin jihar Bornon ta rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka gabata kasancewarta matattarar ƴan ta'adda.

    Gwamnan wanda ya faɗi hakan a wata sanarwa da yake mayar da martani ga harin ’kuskure" da sojojin saman Najeriya suka musanta wanda bayanai suka nuna mutum fiye da 50 sun mutu, ranar Asabar.

    “An sanar da ni kan abin da ya aru dangane da harin sama da rundunar sojin sama ta kai a kasuwar Jilli da ke kan iyakar Borno da Yobe. Ina son sanar da cewa gwamnatin Borno ta rufe kasuwar Jilli da Gazabure shekaru biyar da suka wuce.”

  5. Farashin ɗanyen mai ya tashi sakamakon rikicin Hormuz

    Farashin mai ya tashi bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, da kuma sanarwar da Washington ta yi cewa za ta rufe mashigar tekun Iran baki ɗaya.

    Farashin ɗanyen mai na Brent ya tashi da fiye da kashi bakwai cikin ɗari, inda ya kai dala 103 kowacce ganga.

    Iran dai ta yi gargaɗin cewa za ta kai hari kan duk wani jirgin ruwan soji da ya doshi mashigar Hormuz.

    Sa'o'i bayan alwashin Shugaba Trump na hana zirga-zirgar jiragen ruwan, rundunar sojin Amurka ta yi ƙarin haske kan batun, inda ta ce matakin zai shafi jiragen ruwa ne da kodai suka tashi daga gaɓar tekun Iran ko kuma suke kan hanyar zuwa can.

    Ta ce sojojin Amurka ba za su hana jiragen ruwa daga wasu tashoshin wucewa ta mashigar Hormuz ba.

    Birtaniya dai ta ce ba za ta shiga yunƙurin aiwatar da matakin na Amurka ba.

    Duk da yawan dakarun sojin Amurka a Gabas ta tsakiya, Iran ta yi nasarar jigilar miliyoyin gangar manta zuwa sassan duniya a lokacin da ake ci gaba da yaƙin, wani abu da fadar White House ta sha alwashin daƙilewa.

    A nata ɓangaren, rundunar sojin Iran ta yi gargaɗin cewa duk wani jirgi da ke ƙoƙarin kutsa kai ta mashigar Hormuz zai ɗanɗana kuɗarsa.

    Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa ko kaɗan bai damu ba da matakin da Iran za ta ɗauka, kodai ta koma a ci gaba da tattaunawa ko kuma ta yi biris, yana mai cewa zabi ya rage mata.

  6. Iran ta sha alwashin kai hari ga jiragen ruwan Amurka da ke son toshe Hormuz

    Rundunar juyin-juya halin Iran ta IRGC, ta yi barazanar kai hari kan duk wani jirgin ruwan sojin Amurka da ya doshi mashigar Hormuz da Trump ya ce zai kai wa jiragen dakon mai hari,.

    Wannan dai na zuwa ne bayan da rundunar sojin Amurka dai ta ce umarnin da shugaba Trump ya bayar na toshe mashigar Hormuz ga jiragen da ke fita ko zuwa mashigar zai fara aiki da yammacin Litinin, agogon Iran.

    Shugaba Trump ya sanar da matakin ne bayan tattaunawa da Iran ta gaza cimma yarjejeniya domin kawo ƙarshen rikicin da kuma buɗe wannan muhimmiyar hanyar kasuwanci gaba ɗaya.

    Jim kaɗan da sanarwar Trump ɗin farashin ɗanyen mai na Brent ya yi tsallen baɗake inda ya haura dala 102.

    Mista Trump ya ce matakin zai ƙara zama matsin lamba ga Iran, don sake buɗe mashigar ta Hormuz.

    Shugaban majalisar wakilan Iran Muhammad Bagher Ghalibaf, ya ce barazanar ba ta ɗaga musu hankali ba kuma suna jira.

  7. Buɗewa

    Masu bibiar shafin BBC Hausa na kai tsaye barkan ku da safiyar ranar Litinin wadda hausawa ke yi wa taken ko nasara na tsoran ki.

    Kamar kullum yau ma muna tafe da labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a yaƙin da AMurka da Isra'ila ke yi da ƙasar Iran da ma sauran al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu a shafin da ma sauran shafukan BBC Hausa na Facebook da Instagram da X da Yotube.