Arsenal na son Osimhen, Barca za ta taya Rodri fam miliyan 60

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na kan gaba wajen neman neman ɗauko ɗanwasan Ingila mai shekara 21 Jack Hinshelwood daga Brighton. (Sun)
Barcelona na shirin taya ɗanwasan tsakiya na Spain Rodri fam miliyan 60, amma har yanzu akwai sauran cikon fam miliyan 10 da Manchester City ke buƙata. (Independent)
Manchester United da Tottenham da Arsenal sun tattauna kan yiyuwar ɗauko ɗanwasan Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 27 da Galatasaray. (Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Liverpool da Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 27, ya cimma yarjejeniyar komawa Tottenham. (Voetbal International - in Dutch)
Crystal Palace na son fam miliyan 25 kan ɗanwasan Colombia mai shekara 30 Daniel Munoz, wanda Everton ke farauta. (Football Insider)
Como ta nuna sha'awar ta kan ɗanwasan Ingila mai shekara 23 Liam Delap, wanda Chelsea ta saka wa kuɗi fam miliyan 55. (Mail)
An ƙwace ragamar kaftin ga ɗanwasan tsakiya na Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 31, a Marseille bayan ya yi watsi da tayin fam miliyan 15 domin zua Newcastle. (Mail)
Newcastle na shirin ɗauko ɗanwasan Brighton da Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 22, yayin take shirin ƙarfafa tsakiyarta. (Talksport)
Ɗanwasan gaba na Arsenal Gabriel Jesus na tattaunawa da Napoli. (Fichajes - in Spanish)
Tottenham na ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya domin ɗauko Savinho na Brazil yayin da ɗanwasan ke son raba gari da Manchester City. (Standard)











